Shigarta babu wayu sai ga d'an aike wai ana sallama da ita a waje. Abin yaso ba bata tsoro domin dai lokacin data dawo babu kowa a layin nasu haka ma kofar gidansu da ya zama majalisar samarin da rana. Da yamma kuma majalisar ta iyayenta ne.
"Je ka ce waye ke sallamar."
Yaron bai jima da fita ba ya dawo ya fad'a mata Baban Khadija ne ke neman ta. Da sallama ta isa kofar gidan ta tsuguna har kasa ta gaisar da shi.
"Lafiya lau Maama ya mai jikin ya kara ji?"
"Alhamdulillahi da sauki."
"Ma shaa Allah! Dama yanzu Rabe ke shaida min ya ga saukar ki a d'an sahu shine na zo naji, amma dai babu wata damuwa ko?"
"Babu wata damuwa, sai dai babu cikon kud'in magani data gadon da aka bashi shine kawai ya rage mana kuma babu hanyar biyar."
Murmushi ya yi had'e da waigawa hagu da dama sannan ya ce.
"Yanzu kin ga dai babu inda zaki samo kud'in nan kuma babu wanda kuke da shi da zai taimaka muku, ni kuma da kud'in a gurina don haka ki bani dama na 'yan mintioci qalilan zaki samu kud'in da kike bukata. Ke inhar so kike na d'auki nauyin komai na asibitin zan yi."
Tun daya fara magana gabanta ke fad'uwa domin ba yau ta lura da irin kallon da yake bin ta da shi ba.
"Baba kai fa ubana ne kuma ko ba komai ni kawar Khadija ce don Allah kar ka bari wannan girman ya zube a idona."
"Haba Maama ya kike magana kamar karamar yarinya. Wannan abun fa daga ni sai ke kuma babu wanda zai ci har muci mu sid'e."
"Allah fa yana kallon duk abinda kake fad'a da kuma wanda kake shirin yi Baba Sale."
Ta yi shuru na d'an wasu daqiqu saboda ranta ya fara 'baci sannan ta cigaba da cewa."Don Allah Baba kai hakuri ina maka kawai ci ne saboda kai aminin Babana ne kuma baban kawata. Ka yi hakuri ka cigaba da jan wannan girman kar na take shi a karkashin kafata."
"Duk kibar wannan a gefe ai mun zama d'aya kuma ma ban da abinki sau d'aya tak zaki bani dama shi kenan. Kuma na yi miki alkawarin babu wanda zai san abin da muka yi."
Kallon sa take tare da jinjina karfin halinsa. Ya cigaba da.
"Kin ga bud'e min kofa na shiga kar mutane su farga da ni tsaye a nan mutane su fara zarginmu."
Mike wa ta yi daga tsuggunon da ta yi take kallonsa sheqeqe. Babu ko d'igon kunyar da take masa domin ya zube daga idonta ta ce.
"Allah Ya isa tsakanina da kai kuma har kabar duniya ba zan ta'ba yafe maka ba. In ban da rashin kunya da wadatar ilimin addini me zai kawo ka gurin 'yar cikin ka, yarinyar aminin ka da kuka taso tare har tsufa kuna tare don bukata ta kud'i ta 'billo sai ka kwaso dattin jikin ka wai ka zo dama wa, me zaka dama d'in? Ko ce maka aka yi ko na rasa kud'in da zamu biya a asibiti kai ka kai matsayin da zan had'a jiki da shi don biyar bukata ta? Kai kuskuren fahimtar Maama Malam Sale."
Ta nuna shi da d'an yatsa sannan ta cigaba da.
"Ba dan ina jin kunyar Khadija ba da na saka hannuna na wanke wannan shaid'aniyar fuskar taka da mari. Tun ba yau ba kake bibiyata ina sharewa shine don ka ga babu kowa a gidanmu sai ka kwaso sandar kafafun ka kazo gurina saboda gani na zama Hasiya uwar Ali da Khadija ko?"
Baki sake yake kallon ta. Yasan a rina domin Maama akwai tsiwa amma bai yi tunanin za ta yi masa ba. Gyarar murya yayi ya kalle Maama dake tsaye hannunta biyu tokare da kugunta ya ce.
"Nasan a rina Maama in har baki min haka ba baki cika shegiya ba mara asali."
"Ni ko na cika cikakkiyar shegiya tunda har na iya bijire wa shegen uba irin ka mara tsoron Allah."
YOU ARE READING
KADDARAR RAI
Non-FictionKADDARAR RAI! Labari ne kan Kaddarar Maama, Sadeeq, Faiza da Ahmad.