6

396 28 4
                                    

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓

Written by
NoorEemaan
07082281566

Follow and vote me on wattpad  fisabilillah
@NoorEemaan

Congratulations once again sweetheart nimcy luv Allah Ya kara basira da daukaka. 🥳💃🎉

Page11-12

K'amar wani k'aramin yaro haka Alameen ya share hawaye kana yace "nagode mama, sai ya  mike ya kalli Raliya dake ta faman yaga littafin ba tare da tasan me suke cewa ba, kallon so da tausayi

Ya dauk'i tsahon mutumina goma yana kallonta kana ya fice a sanyaye yayinda matar nan dake zaune a gefen sa ta bi bayan shi tana yiwa su mama sallama...
Cikin tausayawa Al'ameen mama ta kalli baba hadi da cewa "nayi matuk'ar tausayawa Al'ameen baban'su, hakika yana kaunar yarmu Raliya tunda har ya nemi zama da ita duk da wanda lalurar" mama ta karasa tana bin Raliya'n da kallo.

Jinjina kai baba yayi kana yace "wato haleema a dukkanin zancen ki babu karya, tabbas Al'ameen yaron kirki ne hak'an ya k'wadaita mun bashi auran Raliya ba tareda ko shakku ba, sai dai abinda ya fi bani mamak'i shine ranar da damuka wayi gari da labarin batan Raliya da tsahon ciki, sannan ta bayyana bayan kwana bakwai b'ab'u ciki babu alamar sa sai jini kawai dake bin jikin ta, gashi ta dawo ba'a hankalinta ba, bayan nasan yata mai nutsuwa ce" baba ya fada cikin damuwa mai yawa

Idanun mama ne suka ciko da k'walla tuno da ranar tace "baban'su wanna ciwon na Raliya na bani mamak'i, anya anya baban'su ina tamtama"...

" A'a a'a haleema zato zunubi ne, bana zargin kowa sannan kima banason ki zargi kowa, ni dake mun sani cewa Raliya ta fi dukkanin yan'uwan ta haku'ri, bata da abokin fada balle mu zargi wani, in sha Allah zamu cigaba da add'ua, Allah ya shige mana gaba "
Da "ameen" mama da amsa tana share hawaye... Babu jimawa wasu maza biyu suka shigo da alama yayye Raliya'n ne saboda kamaninsu nan suka zauna suka cigaba da tattauna al'amarin daya shigo rayuwar su...

Hada'dden mota kirar matrix ke sharara gudu kan titi, Al'ameen sai faman shafa fusk'ar sa yake yayinda damuwa ke bayyana a fusk'ar sa..
Matar dake gefen mai zaman banza tace "haba my Al'ameen idan hankali ya bata hank'ali ke nemo shi, ka rage dugun nan dan Allah, kada ka zubar damu" tace tana dora hannunta kan nashi.
Ajiyar zuciya ya sauk'e kamar yaro dan karami, gudun ya rage yana furta "thank you Mariya"...
Murmushi kawai ta sakar masa ba tareda tace komai ba..

___________________________________

"Naga ikon Allah yau ni yar dahiru jikar musa, wai bazaki cire takalmin nan ba Nu'aiymahtou? Tun azahar takalmin ke kafarki" kaka tafada tana bin kafar baby Nu'aiymah da kallo, wani gwanjo (second hand) cover shoe ne irin na yara sanye a kafarta
Turo baki tayi tace "ai Papi nane ya siyo min"  inji Nu'aiymah yayinda Nu'aym ke zaune yana kallon diramansu.

'Eh Papi'n naki, nima ai jika nane, idan kika yi wasa wallahi sai na sa ya daina siyo miki komai ma ko Nu'aymu?" Tace tana kallon Nu'aym, dauke kansa yayi kamar bai ji taba yana gimtse dariyar sa
"Toh karka kulani din, har da wani juya keya, wato na tabo yar gwal(gold) din ka ko?"
"Kaka please is ok, bana son wanna fadan naki wallahi, baby yarinya ce fa"
"Anki ayi filis(please) din kawai dan na tausaya maka ka siyo mata tak'almin zuwa makaranta nace ta cire dan kar ya lalace da wuri shine zaka ce kada nayi mata fada, toh ai shikenan, idan ya lalace kudin ka zasu yi kuka ba nawa ba" kaka ta fada ta cigaba da kada miyar kukar ta...

Nu'aiymah ta dawo jik'in Nu'aym ta zauna kan cinyar sa tana yiwa kaka dariya, shima Nu'aym yana kallon ta da murmushi a fusk'ar sa yayinda yake bin fararen kananun jerarrun hakoranta da kallo, hakika soyaayyar Nu'aym a jik'in sa take, har mantawa yake cewa shi din saurayi ne, domin kallon ta yake tamk'ar yar cikin sa jinin jikinsa, zai kuma cigaba da kallonta a matsayin yar cikin na sa har abada, domin bazai iya juran ganin tana kukan rashin iyaye ba.... Nu'aiymah ce ta katse masa tunanin sa da cewa
"Papi ka goya ni kajiiii" ta fada a shagwa'ba tana turo dan tsut din bakin ta
Ba musu ya gyara mata baya ta hau ya mike ta ita, sai tsalle take a bayan tana dariyar farinciki.... Haka ya dinga zagaye tsakar gidan da ita, yana mata  wakar data fi so...

_Ohh! my baby Ohh!! my baby Ohh!!! my baby Nu'aiymah you means the world to me. Ohh! my beautiful baby you are my joy giver, my everything... I love your naughty ways, your childishness gives me alot of joy. When ever i set my eyes on you I felt a lot of happiness,  Papi loves you so Much._

Nu'aiymah Kyakyalle dariyar farinciki take yayinda take bin wakar, wani wajen taci baki inda bata iya ba, k'asancewar yana yawan yi mata wakar har ta haddace wasu guraren...
Kaka na gefe tana cin tuwon ta tana kallon su  hadi da yi musu dariya a fili tace "Allah dai ya kyauta uba mashiririnci, haka zalika yar"
"Ke dai kawai kishi kike kaka har kika gama kuruciyar ki babu wanda ya goyaki" Nu'aym ya fada cikin salon tsokana yana cigaba da yiwa baby'n sa waka...

Ai mik'ewa kaka tayi tana tsame hannun ta daga cikin tuwon hadi da lashe miyar daya bata hannu ta tace"karya kake, yo Allah na tuba ku iyayen yanzu har wata soyaayya kuke nuna wa yara, zaka ce wai ina kishi, toh bari kaji tsabar son da iyayena ke min Allah ya jikan su har madara suke sanya min a koko wanda a lokacin sai y'ay'an wane da wane ke iya shan madara"... Nu'aym ne ya katse ta da fadin "ita baby zallan madarar take sha ba cikin koko ba kinga kuwa ak'wai bambamcin nesa ba kusa ba" ai yowa kansu tayi ita ala dole zata kure shi, yana ganin haka ya fice da sauri Nu'aiymah goye a bayan sa suna dariya...
Suna jiyo muryar ta tana cewa zaku dawo ku same ni ja'irai k'awai.
Haka suka dan dinga zagaye unguwar tana goye a bayan sa taki sauka, har gidan su Abdul-hafeex abokinsa yaje Kasancewar yana ta yi masa korafin baya zuwa, basu wani jima ba suka dawo unguwar su bayan sun tsaya siyan awara kana suka shiga gidan, domin Nu'aiymah taki jinin cin tuwo da kyar yake lallaba ta taci idan ba shi da kudin siya mata wani abun.....

_____________________________
Sanye Nu'aiymah take da uniform yayinda Nu'aym ke rike da hannu ta, labari take bashi na wani malamin su daya dake su yau a makaranta"Papi wani uncle dinmu mai hancin botoromi ya zane mu, dan kawai wata tayi surutu ya hada dukkanin ya daka, ai zaka rama min ko?"
Kasa rike dariyar sa yayi, Nu'aiymah surutu wai botoromi sai ya gimtse dariyar kana atausashe yace "baby uncle ne fa kada ki kara cewa mai hanci botoromi kinji, malam ne he deserve some respect ok?"

"Ok Papi na daina"

" yawwa Papi nah?"

"Na'am baby"

"Yau mummy'n wata yar ajinmu tazo ta kawo mata kayan dadi, shine bayan Mummy'nta ta tafi tace min wai " ke ina Mummy'nki nace mata ban sani ba, ni kaka da uba nake dashi, shine nace zan tambaye ka, Papi ina Mummy na toh? "

Cak! Ya tsaya zuciyar sa ta bada dam! A gaban ta ya tsugunna, idanunsa sun sanja launin yayinda ruwan hawaye ya dan taru cikin su, murya a sanyaye yace "Baby! ni Papi'n ki da kaka mun taba gazawa wurin baki dukkanin farinciki? Ko kin taba neman abu mun gaza yi miki shi?" Ya karasa muryar sa na k'ok'arin bayyana raunin sa...

Duk da wasu kalaman sun mata tsauri bata fahimce ce su duka ba amma, ta girgiza masa kai alamun "a'a"

"To daga yau kada ki kara yin magana akan mummy'n ki, ni da kaka zamu cigaba da baki dukkanin farinciki rayuwa iya iyawar mu kinjiiiiiiii?"
"Eh naji Papi" ta fada tana tabe baki alamun zata yi k'uka, saboda duk da karancin shekarun ta ta hango damuwa mai tarin yawa a idanun Papi'nta, haka suka nufi gida shiru domin bata ga fuskar yin surutu ba balle Papi'n ya biya mata...✍️

(not edited)

Manage
Gobe ma zan yi k'ok'arin Baku update in sha Allah, son so fisabilillah my people

Share fisabilillah

Comment

Editing is not allowed❌

Follow and vote me on wattpad
@NoorEemaan

PAPI NE!Where stories live. Discover now