💓💓💓💓🔥💓💓💓💓
MURADI {SOJA}
💓💓💓💓🔥💓💓💓💓Labari akan wani matashin soja mai zafin ran tsiya,akwai ban dariya, soyayyah,takaddama tsakanin D'a da kuma Uba.
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️Wannan littafin na MURADI free book ne ya yinda DIYAH ya kasance paid book,ku nuna min kauna ta hanyar sayen littafina Diyah domin labarin zai kayatar da ku sosai bazance komi sai kun karanta
Zaku iya nemana ta wannan number domin siyen littafin DIYAH 09066484295
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan littafi nawa ga masoya na a duk Inda suke a fadin duniyar nan,hakika na gode da zallar kauna da soyayyar da Kuke nunamin Allah ya bar kauna.
Nima INA SON KU sosai,
Son So Fissabilillah habibty'sDa sunan Allah mai rahama mai jinkai dukkanin godiya ta tabbata ga Ubangin talikai,Allah ka yi d'adin tsira da aminci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wasallam da Ahalinsa da Sahabbansa baki daya.
Ya Allah ina rokon ka yadda na fara wannan littafi ka bani ikon idar da shi dan alfarmar Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam.🆓 Book
0️⃣1️⃣☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Abuja Soldiers Barack
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆"Congratulations dear Allah ya taimaka ya baka ikon yin aiki cikin gaskiya da amana."
"Nagode sosai Baban riko Allah ya biya ka da mafificiyar Aljarnarsa."
"Bakomi _Umar_ yiwa kaine amma ina shawartarka da ka rage zafin rai kaji?"
"ni fa babban riko bana da zafin rai"
"ka fara Kenan ai kai matsalata dakai ba'a fadama ka gaskiya ka yarda,a ko da yaushe kai ne kan dai-dai"
"to nidai naji amma ko a yanzun ban yarda ba kaga ma ana ta kirana bara na dawo"
ya fada yana barin wurin cikin sassarfa ya isa kan dan_da malin da manyan sojoji suke sama,abun magana aka bashi ya fara magana cikin harshen turanci tamkar ba ture ya yi godiya da karin matsayin da aka masa tare da karramasa bisa Kwazon sa da himmarsa wa kasarsa.Kallo na kare masa fari ne mai dogon hanci ga sumarsa kamar balarabe ya yin da ya yi wani shegen aski irin nasu na sojoji at all gayen ya hadu sosai,kakinsa na duba naga an rubuta sunansa U.F.S {Umar Farooq Soja}wannan shine cikakken sunansa.
Bayan an Kammala bukin kowa ya wuce masaukinsa haka ma Umar da Alhji mu'azzam(baban riko) suka wuce hotel in da nanne baban riko ya sauka, a cewar Farooq shi wai bazai kwana a barrikin sojoji ba.Ba tayadda babban riko baiyi ba yace inaa shi yariga da yayanke hukunci kuma bazai chanza ba,haka ya fita batunsa suka taho tare domin ba yadda ya iya,Umar ya fiye taurin kan tsiya.
A barikin sojoji kuwa bayan an watse manyan wurin suka bukaci ganin Farooq Soja amma ko ina anbincika ba ya nan ma'ana kenan ya tafi ba tare da permission ba kuma hakan laifi ne.
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Sokoto Birnin shehu
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆"nifa Ihsan shi kadai nake Muradi bazan iya son wani ba bayan shi"
"to ya zakiyi ne Ilham ke da kanki ce kika fara furta kalmar ku rabu ki ka bashi zabin da kika san baza ya aikata ba ke kanki ya dace ace kinfi kowa sanin wanene Umar ke ya dace ace kin ba wani labarin halinsa"
"ta ya ko nafi kowa sanin sa Ihsan? Miyasa ya boyemin ainahin aikin da yake?
"ni Ilham wani lokaci kece ma ke bani haushi ma wallahi,shin mine ne illar aikin Soja ne eyye?nifa banga aibun aikinsa ba rayuwarsa fa ya bada yana kare kasarsa,waima tsaya kinsa ko adadin matan da ke crushing din Umar kuwa?yaseen yarinya kinyi sakaci yanzun haka kilama wata lady tayi wuf dashi"
Ihsan ta fada tana mata dariyar shakiyan ci."Stop!
tafada cikin karaji..☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Da safe bayan ya yi sallama da baban riko da zai koma Kano shi kuma ya nufo barikin sojoji cikin shigar shi ta Soja wadda tayi masa bala'in kyau apartment nasa ya nufa yana cikin tafiya ya hadu da wani Soja shine yake sanar dashi cewa General Babangida na nemansa,
"ok badamuwa inshaallah yanzun zanje"
Room dinsa ya shiga ya yi zamansa domin yasan bazai wuce ace laifi ya yi ba sai da ya kwashe kusan minti talatin sannan ya nufi office din sir General Babangida.......
©️♤♡ Zeesardaunerh
YOU ARE READING
MURADI {SOJA}
Fantasia💓💓💓💓🔥💓💓💓💓 MURADI {SOJA} 💓💓💓💓🔥💓💓💓💓 Labari akan wani matashin soja mai zafin ran tsiya,akwai ban dariya, soyayyah,takaddama tsakanin D'a da kuma Uba. Wannan littafin na MURADI free book ne ya yinda DIYAH ya k...