*ILHAAM*

16 3 1
                                    

🎀 *ILHAAM* 🎀
      

                 by

Sadeeyah Abubakar maru
             (sadeey)

*SADAUKARWA*
Na sadaukar da Wannan littafin ga mahaifiyata abun alfaharina Allah ya jikanki ya gafarta miki yasa mutuwa hutuce.

wow sister Aysha Wannan nakine halak malak  kiyi yadda kikeso dashi INA godiya da comments dinki mai tsundumani cikin kogin farinciki, INA farinciki sosai💏💏💃💃💃💃💃

Page 71-80_______________________
***************
5 years back

A  shekaru biyar  dinnan abubuwa da yawa sun faru ciki harda  Karo karatu wato masters da phd, da Ahmad yayi Wanda ya kara masa girma a office dinsu, yanzu fa Ahmad ya yayi kudi ba laifi domin har ya sayi  fili yayi gini mai shegen kyau, gidane mai mai side guda biyu,wato shi da kaninsa Usman kenan,Amma kuma sai bai dawo ba a cewarsa. yana tare dasu malam, haka Kuma yana taimakawa yan uwansa na Kauye, inda har yayi renovating gidansu ya tsantsara mudu  gini na ganin na fada,yayi musu family hause, Wanda babu irin sa a fadin  garin.

wannan kudin da yan garin suka ga yayi yasa aka fara kana nan maganganu akan rashin haihuwar ta, Wanda yasa ran Mlm modibbo baci  matuka kuma yayiwa tufkar hanci.

A bangaren zamansu
babu Wanda ya taba jin kansu, ba'a taba ba ko musu bai taba hada suba ballnetana wani raini ko Fad'a.

a Duk tsawon wadannan shekarun ko batan wata Fatima bata taba ba ballen tana bari haka suke zaune duk da yana damunsu Amma ba'a ganewa gwara ma ita Fatima kasancewarta mace mai rauni, Kuma kowa yasan rashin  haihuwa matsalace babba.

Fatima tana kiyaye duk abunda tasan zai batawa gwarzon mijinta rai.

zamansu zama ne na amana da fahimtar juna, Alhamdulillah Yanzu zan iya cewa zaman masoya suke ba na yan biyayya ba.

Haka ma addah surkuwar kirki ko tari  bata taba ba akan rashin haihuwa surkunanta saboda tasan Allah shine mai bayarwa kuma shine mai hanawa, duk da tanason  ganin yan jokokinta Amma kuma ko a fuska ba'a gani, ita  dai cewarta  nata  addu'a ne kawai,

matar Usman wato mayro  itama shuru Kaman an shuka  dusa  domin yanzu  aurenta  yana daukan shekara goma Amma Shuru kake ji,

bayan auren su Fatima da shekara daya shima mus'ab ya auro mata mai suna zainab wacce ya dauko daga bauchi.

************
Tashi tayi ta tsaya domin ko ba'a Fada mata ba tasan Yanzu mijin tane ya dawo don time din dawowarsa yayi, sallah man da taji ne yasa ta gane ya iso, barka da zuwa ta masa tare da karban jakar office din dake hannunshi, amsawa yayi tare da kai idonsa kanta ganin yadda tadan fada a kwana biyunnan shuru yayi kawai   ya nufi hanyar sida  dinsa don kimtsawa.

juice da ruwa sai kuma food flaks ta hada a akan Dan madaidaicin tray kana tayi hanyar side dinshi.

Da dare bayan sunci dinner suna kallon TV,Kaman bazaiyyi magana ba sai kuma chan yace " Fatima!
dagowa  tayi tare da cewa Na'am cikin sanyin murya, kallon 2 seconds ya mata yace me yake dumunki? baki ta bude da niyyar cewa bab..... kafin ta karasa ya daga mata hannu tare da cewa " don't tell me babu please, Shuru tayi tare da sadda  kanta kasa,
tambayar ya sake maimaita mata cikin sanyi irinna wacce bata jin dadi tace " wlh yaya nima bansaniba kawai dai nasan banajin dadin jikina a kwana biyunnan,
kallon ta yasakeyi kana yace jeki dauko veil dinki kizo mu tafi asibiti, kaman zata Musa sai dai kasancewar musu baya cikin dabiunta  yasa ta tashi,

'Daki taje dauko gyalenta  ko da ta fito bata ganshi ba hakan yasata bin hanyar waje, tana fitowa ta ganshi zaune a cikin mota har yayi rivers tana shiga ya tada motar suka fita a gidan.

*Specialist hospital* suka nufa, da isarsu sukayi office din doctor muktar (family Doctor )kasancewar ya kirashi kuma shine da night duty that why suna zuwa sukayi hanya daya, kana suka shiga bayan yan gaisuwa da zolaye-zolaye sannan Ahmad ya fada masa abunda yake faruwa.
kallonta kawai yayi yace madam yadai? Fatima tace bakomai, Ahmad ne yace" Wlh doctor batajin  dadi kuma idan na tambayeta sai tace "Babu"
murmushi kawai doctor muktar yayi kana ya sake kallonta a karo na biyu,
tambayarta yayi, me dame  takeji?   Fada masa tayi,ganin haka  yasa  doctor kiran daya daga cikin Nurse din asibitin, fada mata abunda zatatiwa Fatima yayi,

Bayan an kawo. Result doctor ya gane Fatima na dauke  da cikin 2 months,
cikin zumud'i doctor ya fada masa Abunda yake faruwa,

Fadan farincikin da Ahmad yake ciki bata lokacine, sauka yayi akan kujeran ya kalli gabas yayi "suduju shukur"

haka itana Fatima taji abun ka.an a mafarki wai yau itace da ciki rasa me za'ayi tayi kawai sai jin domin Abu tayi aka kuncinta nan ta gane Ashe hawayene.

Godiya yayiwa doctorn kana suka dawo gida,

Duk da yanajin  kunyan fada Amma haka bai hanashi kiran iyayensa ba, modibbo,
  
Baya. Sun gama gaisawa sai kuma yayi shuru, modibbo daya San cewa akwai magana sai yayi gyaran murya, kana yace " amadu akwai wani Abu ne?

Sosa keya  Ahmad yayi kana yace dama Dama
Umm...... Fatiiiii...ma ce  sai kuma yayi shuru, modibbo yace "uhum  inaji cigaba, cikin kunya mahaifinshi yace"  dama Fatima doctor yace tana da cik.....
Kitttt! Ya kashe  wayan.  Kana ya tafi wajen Fatima domin jin me takeji.

murmushi yayi tare da godewa Allah,  cikin gida ya shiga ya samu addah, addah dai ganin fuskan sa washe yasa ajiye rairiyan hannun ta  tare da kade hannun ta, kana tace malam lafiya naga kana murmushi zama yayi akan taburman da ta shumfuda masa kana ya kwashe komai ya fadawa mata, addah tayi farinciki sosai sannan ta hodewa Allah da Wannan abun farinciki sai ga hawaye yana zuba  a idon  hannu ta malam ya rike kana yace Rukayyatu ba kuka zakiyi ba, kuka ba godiya bane, ki gode masa shi Kuma sai  ya Kara, hanu  ta daga sama kana tace"Allah na gode maka, har dai yanzu hawaye basu daina zuba a idontaba, hannunsa yasa ya wiping mata hawayen kana ya fara  rarrashinta tare  da fada mata kalamai masu sanyaya  zuciya,nikam nayi nan.

maganan ciki babu inda bai je ba a cikin kauyen jarkum anata  nanatawa akan Fatima na dauke  da ciki, masu farinciki nayi haka ma masu hana ruwa gudu

Addayi ( mahaifiyar Fatima) itama tayi farinci sosai akan Wannan lamarin sannan ta gode wa Allah ko ba komai zata huta da maganganun mutanen garin.


kaiwa take da komawa a tsakar   dakin kai Kace safa  da marwa take yi,huci take kaman wata zakanya cikin muryan da yake   nuna zallar bakincikin da take ciki tace" Wlhy bazata  sabuba wai bindiga a ruwa chappp Wlhy Fatima kinyi kadan wane ke Wlh ko addayi bata isaba  ballen tana ke ni komai nasa  a gaba bana nasara chapp ay wlh idan an haifi Wannan shegen cikin ladiyo shegiya ta haifeni, ni ya kamata na samu Wannan Abun ba keba kullum arziki  binki yake Amma ni  Shuru yarinya karama kanwar bayana kaiii da sakel wlhy........

Hmm masu karatu waye kuke  tunani mai wadannan maganganun?

shin anya Fatima zata haifi Wannan cikin kuwa?

Ku biyoni don jin yadda zata kaya💃💃


please following me on watpaad at sadeeey0002

#Comments
#vote

09139216255
sadeey

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 19, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

     *ILHAAM*Where stories live. Discover now