1

448 20 3
                                    

Bismillahil Rahmanin Rahim

SILAR YARDA 1

Na Pharty BB


A hankali ya fito a cikin jirgi ɗauke da ƙaramin jakarsa a hannu, ɗago kai ya yi yana kallon filin da idanuwansa da suke sanye cikin gilashi baƙi, ya zauna a fuskarsa sosai wanda yake kewaye da kyakkyawar sajen da yake shan gyara, ya yi wa farin fatarsa kyau. Sanye yake cikin ƙananan kaya na farin riga da baƙin jeans, matashin saurayi da ya haura shekara talatin da biyu.
Cikin nutsuwa ya gama sauƙowa a matakalar benen jirgin, kai tsaye waje ya nufa yana barin cikin airport ɗin. Motar da take fake ya nufa, ƙofar baya ya buɗe ya saka jakarshi ya rufe sannan ya matsa ya buɗe gidan gaba mai zaman banza ya shiga.
Wanda yake jan motar ya juya yana kallon shi da murmushi ɗauke a fuskarsa.
"Sai ina?

"Gidana."
Ya faɗa yana yin baya ya kwantar kanshi don ya gaji sosai da zaman jirgin.
Wanda ya yi magana da farko ya kunna motar yana yin riverse suka fita a filin jirgin, sannu a hankali ya ci gaba da tuƙi suka hau kan titi babba. Hankalinsa akan titin ya ce.
"Ya aikin kuma? Ganinka ya yi wuya?"

Numfashi ya furzar yana kai hannu ya zare gilashin idonsa, ƙwayar idanuwan shuɗi ne (blue) sosai maimakon baƙi. Ajiye gilashin ya yi a saman cinyarsa sannan ya ce.
"Ya zan yi, komai ya kusa kammaluwa."

"To Allah ya taimaka."
Faɗin ɗayan yana ci gaba da tuƙi. Shi kuma kallon garin ya ci gaba da yi tamkar ba shekaru uku ya bari ba, ya ƙara kyau da gyaruwa.
Tafiya suke har zuwa unguwar da gidansa yake, a ƙofar gidan ya faka motar. Juyawa ya yi ya kalle shi ganin ya faka.
"Wai ba za ka shiga ba?"

Girgiza kai ya yi yana miƙa mishi mukullin gidanshi da ya karɓo mishi a gidansu, yana murmushi ya ce.
"Ina sauri. Amarya tana jirana."

Aasim baki ya taɓe yasa hannu ya karɓa, yana ƙoƙarin buɗe motar ya ce.
"Ka shiga uku da rawar ƙafa akan mace. Allah ya raka taki gona."

"Ba za ka gane ba ai, sai lokacin da ka tsinci kanka cikin yanayin da nake ji."
Jabeer ya faɗa yana dariya, halin Aasim yana ba shi mamaki, yana roƙar Allah tsawon rai yaga ranar da zai nuna mishi lokacin da zai kalli mace ta burge shi. A bar shi da bautawa aiki da cin moriyar wahalar bokon da ya yi, burin shi kenan kuma ya samu.
Aasim bai kula shi ba ya sauƙa ya rufe motar, gefe ɗaya ya buɗe ya ɗauki jakarsa yana nufan gidan, yasa mukulli ya bude get ya shiga. Falon ya nufa ya sa mukulli ya buɗe yana shiga, fes a gyare don jiya ya sanar da mahaifiyarsa yana hanya, yasan za ta turo a share a goge don ya jima baya nan, yasan zai yi ƙura. Upstairs ya nufa yana wucewa ɗakinsa, buɗewa ya yi ya shiga. Saman gadonsa ya ajiye jakarsa yana zama, sunkuyawa ya yi ya cire takalmansa sawu ciki, bayan ya gama ya yi baya ya kwanta don ya gaji, ruwa yake so ya watsa ko zai ji daɗi, ga yunwa, amma gajiya ya hanasa. Idanuwansa ya fara rufewa a hankali bacci ya kwashesa a yadda yake.
Sosai ya yi baccin har ƙarfe huɗu sannan ya farka ya ji gajiyar babu sosai, miƙewa ya yi ya wuce bathroom, ruwa ya watsa ya ɗaura alwala ya fito daga shi sai towel da ya samu duk a wanke sai ƙamshi suke.
Jakarsa ya buɗe ya cire jallabiya ya saka, gabar ya kalla ya tayar da kabbara ya hau yin sallah. Bayan ya idar ya yi addu'o'i ya miƙe, jakarsa ya ɗauka ya bude wardrobe ɗinsa ya saka, mukullin motarsa ya ɗauka ya buɗe jakar ya ɗauki wallet da ATM ɗinsa da yake ciki ya fita.
Parking space ya nufa ya buɗe motarsa ƙwaya ɗaya da yake fake ya shiga, kunnawa ya yi yana yin riverse, ya fito a motar ya buɗe get, ya koma motar ya fitar waje, ya dawo ya rufe get din, daga haka yaja motar yana fita.
Wajen cin abinci ya nufa mai ƙyau, bayan ya yi parking motar ya sauka ya shiga ciki. Empty table ya nema ya zauna, waiter ya zo anan ya faɗa mishi abin da yake so. Bayan an kawo mishi ya hau ci a nutse, bai kalli kowa ba balle yasan su waye a ciki.
Yana kammalawa ya miƙe ya isa wajen su ya biyasu tare da juyawa ya fita, motarsa ya koma ya shiga ya kunna yana ja yabar harabar wajen.
Kai tsaye unguwarsu ya nufa inda ahlinsa suke, yana kalle kalle-kalle na garin har ya shiga unguwar ya tsaya a ƙofar gidan, hon ya yi aka wangale get din ya shiga da motar. Parking ya yi wajen da motoci suke jere sun fi biyar, duk ya gano masu shi don yasan su.
Sauka ya yi ya nufi falon gidan, tura ƙofar ya yi tare da sallama ya shiga. Anan ya yi arba da mahaifiyarsa da ƙaninsa ɗan shekara shida, sai sauran samari uku da suka bi shi da kallon mamaki. Murmushi ya yi yana ƙarasawa wajenta jin ta amsa ita ma fuska ɗauke da murmushi.
Kusa da ita ya zauna yana jawo yaron ya ɗaura saman cinyarsa, yaron bai gane shi sosai ba, amma ba shi da ƙiwa haka ya zauna jikinsa. Fuska ɗauke da murmushi Aasim yana kallon Amminsa ya ce.
"Ammi ya gida da kwana dayawa? Sajeed ya yi wayo, kamar ma ya manta da ni?"

SILAR YARDAWhere stories live. Discover now