Tsawon mintuna goma Aasim yana zaune a falon shuru shi ɗaya don sauran sun mayar hankali kan hirar da ƙaramin cikinsu yake musu, sai babbaka dariya suke da Aasim yasan duk don su baƙanta mishi ne.
Aasim ka sa jurewa ya yi ya miƙe tsaye ya nufi ƙofa, ya riƙo handle zai buɗe ya ji muryar Ammi tana cewa.
"Aasim ina zuwa?"Juyawa ya yi yaga Ammi ce ta fito a ɗakinta. Sakin handle din ya yi ya koma cikin falon, kujeran da ya tashi akai ya sake zama.
Ammi ta zo ta zauna a gefensa tana faɗin.
"Da ban fito ba tafiya za ka yi?"Girgiza kai ya yi fuskarsa ɗauke da murmushin da tun zuwansa sai yanzu ya yi.
"Sauri nake Ammi, zan nemi ticket ne don ina son komawa da wuri don ayyukan da na bari.""Hakan ya yi? Ya biki da hidama."
"Allahamdulillahi ya ƙare, sai fatan zaman lafiya."
Aasim ya faɗa yana miƙewa tsaye, ya cigaba da faɗin, "zan wuce gobe zan shigo.""Allah ya taimaka."
Ammi ta faɗa mishi. Cikin murna ya ce.
"Amin Ammina."Daga haka yabar falon. Ammi juyawa ta yi ta kalli sauran samarin, rai ta haɗa ta fara faɗin.
"Yaushe za ku nutsu? Kuna kallon ɗan uwanku amma tamkar wanda ku ka ga maƙiyi."Babban cikinsu ne ya miƙe tsaye sannan ya ce.
"Ammi shi da ya shigo bai fara mana magana ba sai mu. Don yana taƙama yana da arziƙi, to ya yi kaɗan.""Dalla rufe min baki! Bana son wannan abin da ku ke yi, shi ma ganin kun nuna baku sanshi ba yasa ya muku haka, amma zan mishi magana."
Ammi ta faɗa cikin nutsuwa, tana son ganin yaranta sun haɗa kansu, su ne ɗaya, babu wanda ya kaisu kusanci.
...Aasim yana fita ya tafi neman ticket, cikin ikon Allah ya samu jirgin da zai tashi nan da kwana uku. Daga nan eatery ya biya ya ci abinci ya biya kafin yabar wajen, gidansa ya koma ya cigaba da huta gajiya.
***Ƙarfe biyar Fatima ta baro islamiya ta nufo gida don an tashe su. Ita ɗaya take tafiya tana kewar Ammabuwa, tasan da yanzu tana nan suna tare. Murmushi ta yi don tuna warhaka tana can maƙale da mijinta.
A haka ta shigo layinsu, tun daga nesa ta hango Babanta zaune da Malam Sunusi a dakalin ƙofar gidansu, mutum mai ɗan arziki a cikin unguwarsu duk da wasu sun linka shi, suna shiri da babanta sosai.
Kanta ta sunkuyar ƙasa ta cigaba da tafiya har ta iso ƙofar gidansu, ta duƙa ta gaishe da su ta ce.
"Ina wuninku.""Lafiya...lafiya lau."
Ta ji muryar Alhaji Sunusi ya amsa da sauri, Baba ma ya amsa. Daga haka ta wuce cikin gida.
Da kallo Malam Sunusi ya bita, da yaga ta shige ya ɗauke kai yana mayar hankali kan hirar Baba. Sam ya daina fahimta don zazzaƙar muryar Fatima yake ji har lokacin a kunnuwansa, idanuwansa kuwa suna kallo mishi kyakkyawar fuskarta duk da ta sunkuyar da kanta hakan bai hana shi hango kyakkyawar fuskarta ba.
Tsaye ya miƙe kamar an tsikare sa, har Baba ya tsorata ya miƙe yana cewa.
"Lafiya Malam?"Cikin sauri Malam Sunusi ya ce.
"Lafiya lau, karka damu.""Ka haƙura na biyaka nan da ƙarshen watan?"
Baba ya faɗawa Malam Sunusi jin dagaske ne ya ce kar ya damu. Ga mamakin sa ya sake ji Malam Sunusi ya ce.
"Eh karka damu.""Na gode sosai."
Baba ya faɗa cikin murna.
Malam Sanusi babur ɗinsa ya hau ya kunna yana ja yabar wajen.
Baba ganin haka ya shiga gida, dama sallamar Malam Sanusi yasa ya fito, kafin zuwan Fatima haƙuri yake ba shi akan rashin kai mishi bashin kuɗin da yake binsa, sai kuma abin mamaki take Malam Sanusi ya kawar da maganar.
YOU ARE READING
SILAR YARDA
RomanceYarda abace mai wuya. A lokacin da ka ɗauki yarda ka ba mutum, a lokacin zai zamto maka fitilar rayuwa, hasken duniya, jagora ga al'amurranka. Completed a ArewaBook akan N250 naira Through account N500