*FATEEMAH TA*
written by meeerarh
*page 5*
ELEGANT ONLINE WRITERS
🌹🌹🌹🌹
Ai daga Umma har Mom duk sai dai aka gansu akasa sume,ba karamin tashin hankali Aryaan yashigaba bayan an shigar dasu dakine Aryaan yazauna ya dirji kukanshi son ranshi...
wani likitanne yafito daga dakinda su Khaldoon suke, yaga Aryaan agurin zaune yana kuka, sai , yaga yakamata ya fada mishi abundq ke faruwa dadukan su biyu din...
karasowa kan kujeran da yake zaune yayi tareda dafa kafadunshi, abokina Doctor din yafadi , Aryaan najin haka yayi saurin dagowa yana goge hawayen dake kwance a fuskanshi...
kafadunshi Doctor din ya dago tareda taimaka mishi ya tashi, Aboki na kataso muje office i really need to tell u something about this patients dinnan da aka kawo...
Ai da sauri Aryaan yatashi yabi bayan Docton...
🌹🌹
koda suka shiga office din dakyar doctor din yasamu Aryaan ya zauna yashiga yimishi bayani..
agaskiya bazan boye maka ba yakamata ka sani dan da alamu kai nakusa dasune sosae, kuma ganin halin da iyayenku suka shiga yasa bamu fada musu ba saboda suma da alamu zasu iya rasa rayukansu...
nafahimci kaidin kana da hankali shiyasa zan fada maka,, inaso kasan duk wata kadara da zata samemu daga Allah ne , inason ku dauki kadararku ta alkhairi kota sharri....
Allan daya fimu sonsu ya karbi kayanshi, Allah ya amshi rayukansu ta hanya mafi sauki batare da sun sha wahala ba Allah yajikan musulmi inaso kasama ranka hakurin rashi, nasan rashin abunda kakeso ba abu bane mai sauki.....
Aryaan dai tunda yaji doctor ya ambaci mutuwa yayi sumab zaune a inda yake, saida doctor ya dafashi sannan ya dawo hayyacinsa..
aranshi yake magana, meyasa Khaldoon zai mishi haka, mezesa yatafi yanxu dasuke ganiyan kuruciyansu , and Fateema meyasa zasu tafi ..
meyasa tun kafin labarin soyayyansu yafara mutuwa zatayi musu hakan,,
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN...abunda yake iya maimaitawa asaman labbanshi...
sosae doctor ya tausayawa halin da Aryaan yake ciki..haka doctor yaita bashi baki, dakyar dai ya tattaro 'yar sauran jarumtarshi ya mike tareda fitowa daga office din yana tafiya gaba daya duhu ya mamaye idanuwashi...
tunaninshu daya yanzu taya zai fuskanci Umma da Maman Fateema da wannan labarin...
dakin dasuke yashiga ya karasa bakin gadon Khaldoon ya tsaya yana kare mishi kallo, idan kaganshi zakace barci yakeyi...
fuskanshi cikeda annuri , sai lokacin hawaye suka zuba a idanuwanshi, yafara magana, haba Muhammad Aibaan meyasa zakayi mun haka, har yanzufa bamu shiryaba, katuna nace maka zan tafi amma zan dawo , gani na dawo dan Allah Khaldoon katashi yakakeso nayi da tawa rayuwan, kana tunanin zan iya coping batare da kaiba abokina, please katashi Umma na bukatarka arayuwanta kaga Abba ma bayanan dane kakesi taji...
gatacan a gadon asibiti dun kafin taji meya faru daku kaida Fateema..sai yajuya inda gadon Fateema yake yana magana cikeda rauni, haba kawarmu har nafara tunanin yanda rayuwar soyayyarku zata kasance har naga 'ya'yan ku sunzo gidana weekend yaza'ayi mutuwa tayi mana haka ...
haka yaita sambatu har doctors suka shigo tareda Abban Khaldoon sgima hankalunshi atashe, yana Kaduna aka kirashi aka fadamishi abunda ke faruwa baimasan sun rasuba andai fada mishi sunyi accident..
yana shigowa inda Khaldoon yake yanufa yayi mishi magana kawai yaga babu alamun rai a jikinshi...
dab'as ya zauna akasa zuciyarshi namishi wani irin zafi, yanzu haka mutuwa zata mishi danshi kwalli daya da Allah yabashi , yanzu gashinan ta dauke mishi ita...
kallon Aryaan yayi tareda fadin, Aryaan kaga yanda Aibaan zai mana ko, yacemun fa idan na dawo zai nuna mun FATEEMAN SHI yace mun FATEEMA TA kyakkyawa ce Abbana, idan kaganta kaima zaka sota....
karasowa inda yake Aryaan yayi tareda rungumeshi cike da sarewa yake magana.....
Abbana WANNAN ITACE KADDARAR MU dole mu amsheta hannu biyu....
gaka FATEEMAN SHI itama akwance labarin soyayyansu ya kare tun kafin ya fara...
sai lokacin Abba ya dubi gadon da take tareda tasowa zuwa bakin gadon...
Allah sarki FATEEMAN MU Allah yakai haske kabarinku tabbas soyyayyanku sai a ALJANNA ina fatan Allah ya kaddari saduwanmu a gidan gaskiya...
daga haka aka cika duk wasu formalities din da yakamata aka dauki gawawwakinsu har lokacin su Umma basu tashiba....
haka aka yi musu sallah aka kaisu gidansu na gaskiya..Allah ubangiji yajikan magabatanmu...
kaddara abace dababu wanda ya isa ya guje mata kowa da irin tashi kaddarar wasu soyayyarsu kan kaisu har aure wasu kuma har tsufa amma su kaddararsu ta kasance marar dadin ji....
SOYAYYARSU TA KARE TUN KAFIN TA FARA .....
is a true life story ......😭😭😭
Tammat bihamdillah......anan na karasa littafina mai suna FATEEMAH TA ina fatar abun damukayi daidai Allah ya sa mu amfana dashi wanda mukayi ba daidaiba Allah ubangiji ya yafe mana.....
na sadaukar da littafina gaba dayansa ma 🌹FATYMASARDAUNA🌹aminiyar kwarai
YOU ARE READING
𝐹𝑎𝑡𝑒𝑒𝑚𝑎ℎ 𝑇𝑎
Romancesayayya abace da ko wane mutun zai so ya fada acikinta,wasu sin san sanda suke fadawa wasu kiwa basu saniba.