4

1.6K 37 4
                                    

*_DEEN MARSHAL_*
_Mamuhgee_

4
Anan gurin hajjo tayi niyar kwana Dan Haka Babu wata damuwa Kamar yanda tasaba rayuwarta na rashin riqe damuwan Abu ta sakewarta musamman dayake tanada daki daki me zamanta agidan a cikin babban palon hajjon wanda dakin Babu abin daya rasa najin Dadi da tsari musamman irin na rashin hayaniya da akasan Naj din batada ita Wanda hanifa ma anan dakin take yanzu idan tana gidan sbd tabaro part dinsu Dad dinsu tunda Babu kowa a part din.
Tanada Yan wasu kayan sawa a gidan Dan Haka Kai tsaye bayan sun Gama cin abincin dare Bata tsaya doguwar Hira ba Shirin bacci tayi bayan tayi sallah ta kwanta sai lokacin tabi misscalls din Sarah da Kira cikin nutsuwa tagama sauraran bayananta na aikin data bar Mata kafin ta Dora da cewa"

Ummm Naj dazu bayan tafiyarki Abaas yasake dawowa yasa an fiddo Masa da dukkanin record dinmu na aiki tun na January ya soke wasu daga ciki tareda fidda Kura kuren dazasu Iya bamu matsala Kuma Yana maganar a sauyani daga gurinki.

Dan sanyi muryarta tayi cikin bayyanarda rashin Jin dadinta tace"

Naj kiyi magana dashi please abarni agurinki sbd Ina barin gurinki na tabbatarda korata aikin zaiyi gabaki daya.

Ajiyar zuciya Me sanyi Naj din ta sauke tana tareda bude Baki cikin muryarta me Dadi Kai tsaye tace"

Karki damu zanyi magana dashi gobe
Kawai dai ki ringa kiyaye Masa tunda Kinga yanayin kalar fushinsa baya tunani me kyau idan ransa ya baci.

thank you Naj.

Ok then see you tomorrow"Naj din tafada tana kashe wayar tareda ajewa gefe tana Dan zamewa daga jingine datake akan gadon ta kwanta tana lumshe fararen idanuwanta ta rufe tana Dan yin bacci.

Hanifa dake zaune tana kokarin Kiran wayar mijinta tana sauraron wayar da Naj din keyi ta Dan saki guntin tsokin baqin cikin Abaas din datakeson koyawa zuciyarta Aminta dashi amatsayin mijin 'yar uwar tata tun yanzu.
Kashe wayarta tayi tareda miqewa ta zagayo tahau gadon ta kwanta tunda takasa samun Isma'eel din ga Naj shegen miskilancinta wani lokacin baya barinsu yin wata doguwar fira.

Qarfe 8 na safe ta fito wanka daure da towel me kauri tanaji wayarta na ringing Taki ko kallon inda take ta nufi gaban madubi tafara shafa Mai Wanda dama kusan komai product daya suke amfani dashi itada Hanifan.
Shiryawa tayi cikin doguwar riga maroon ta daura qaramin gyale akanta ta fito tana qamshin turaren Vivian rosalle har lokacin Hanifa na kwance sbd ciwon wuya data tashi dashi Wanda dama kullum cikin ciwuka take sbd sikla ce lafiyarta qarantacciyace sun Saba da rauninta shiyasa qaninta marshal baida wani abinda yafi komai so a duniyarsa bayan ita sai kakarsa tukuna mahaifinsa.

Dakin hajjo tafara zuwa har lokacin hajjon Bata farka ba itama Dan Haka Kai tsaye ta wuce kitchen su ruqayyat na ganinta cikin girmamawa sukace"

Ina kwana Anty.

Lafiya kalau ruqayyat
Please ku hado breakfast din Hanifa akawo daki batajin dadi.

Fridge ta qarasa ta bude ta dauko madara ta zuba a cup tareda zuba ruwan zafi aciki tayi dumi ta zuba Zuma kadan aciki ta dauka ta shanye ahankali tareda aje cup din ta koma ta  diba dabino uku taci ta fice daga kicin din su ruqayyat suka bita da kallo Kamar dai yanda suka Saba sbd mamakinta har kullum Baya sakinsu na yanda take komai nata cikin wani irin burgewa da qaidojinta da nata ita ta shardantawa kanta su sbd maintaining rayuwarta.

Kalar abincin datake duk da gidansu ba masu halineba ta qayyade abinda take ciwa cikinta Wanda yake kamar dieting ne takewa kanta sbd gabaki daya rayuwarta batason abinci me nauyi tun tana yarinya Haka take idan taci abinci me nauyi sosai Yana wahalar da ita shiyasa data girma ta San yancin kanta tanada abubuwan datake ci kawai da wainda bataci Wanda shima yake qara bayyanarda miskilancinta da burgewarta da wasu ke gani acikin gidansu kuwa suna daukan hakan amatsayin nuna wayewa da nuna kudi Wanda yasa mazan ke ganin tafi karfinsu Ana samun matsalar fasa aurenta Kashi Kashi Kuma Sam Bata nuna damuwar hakan shiyasama ta tabbata dai itace Bata tashi aurenba inji su Dadah da Dattijo.

DEEN MARSHALLWhere stories live. Discover now