Chapter15

316 36 2
                                    

*GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

           *🅿️15*

"Da kafarsa ya gangara zuwa Gidansu Sagir din Bai tsaya ma Daukan Mashin Din nashi ba domin kwana Biyu yafi jin dadin Tafiya da kafarsa fiye da ko yaushe,kwana Biyu bai Fita Jogging ba yana jin Jikinsa wani iri Shiyasa yake Treeking da kafarsa Wani Lokacin.
Sai da yazo Kofar gidansu Sagir din yaja ya tsaya,Kuma ya leka Shagon ya Hangi Sagir kan keke yana ta Dinki Hankalinsa na kan Abunda yake yi,Bai ma Lura Da masu Shigowa da masu fita ba yau Dagashi sai Yaronsa Daya Sauran basu Riga sun zo ba shine ma yaga Lekowan Imran din ganin ya koma Shiyasa baima Sagir din mgana ba.
Waya Imran ya Lalubo Cikin Aljihun Jallabiyansa ya Lalubo Lambar Sagir ya Dokamai kira yana Tsaka Da Dinki Wayarsa Dake ajiye gefensa ta Dauki Neman agaji Ta Wutsiyar ido ya Juya yaga mai kiran Imran ne bai Daga ba Sai da yakai karshen Inda ya Fara Dinkawa kana ya dakata ya Daga Kiran Yana Fadin"Ya akayi ne..?
Imran Dake waje yace"Bansani ba..Mallam ka Fito gani a Kofar Shagon ka..!
Sagir ya Dakuna Fuska kamar Imran na Ganinsa yace"To kai meye ya Hanaka Shigowa..? Ka Shigo mana Ina Dinki ne ba Zaune nake ba kamar kai..!
Imran yace"Ban ga Daman Shigowa bane..Kuma Dake min Gorin Zaman banza Ka samo min aikin yin ne kaga nace bazan yi ba..?
Sagir Dayaji Haka ya Mike yana Fadin"Ta kwana Gidan Sauki Indai aiki ne Ina dashi..Bari na Fito..!
Yafada Lokaci daya yana Katse Kiran Yaronsa yayi ma mgana kafin ya Fita ya Iske Imran din Tsaye ya Tusa Duka Hannayensa Cikin Aljihun Jallabiyansa
Yana Jiransa yayi mamakin ganinsa yau baya Busa Hayaki Shiyasa yana Zuwa yace"yau Watarana Abokina yazo baya Shan Sigari..?
Imran ya kallesa kamar bazai yi mgana ba sai Chan yace"Zan Busata kuwa..Ta karemin ne jiya Cikin Dare..Yanzu kafin na Shiga Gida Zan Siya..!
Sagir ya kada kai kafin yace"Don Allah Ka Daina Shan Sigari..Wlh Sam Shanta bai Dace Dakai ba ko alama..!.
Batare Daya Kallesa ba yace"Daman masu Shanta din ta Dace dasu ne..?
Sagir yace"Eh gsakiya Majority din masu Shanta Zaka ga sun Dace da Shanta Din ammh kai Fa kalleka Daga Sama Har kasa Duk da bansan komai akan ka ba na Tabbata kayi Ilimi mai Zurfi Tundaga na Zamani har na Boko Wanda bai ma Zauna Dakai ba Zai Fahimci U are a Luky Ballatana ni da na sanka Gaskiya Shan Sigari bata Dace Dakai ba Abokina Don Allah ka Daina Shanta Sam bana jin Dadi..Kalli bakin ka Har ya Fara Baki..!
Imran yayi Shuru yana kallon Sagir Allah Sarki zai Rage shan Sigari ko Domin Abba da Sagir sun Damu Dashi kwarai Kuma Shi Mutun ne Da baya Juyama masu kaunarsa Baya Kota Halin Kaka sai ya Rama musu Alherinsu gareshi..!
Ganin yayi Shuru yasa Sagir ya Dafa Kafadarsa yana Fadin'Kayi hakuri in mgana ta bata maka rai..Ina son Naga rayuwarka Ta Dawo Tamkar yadda kowa ke Rayuwa ne..Am sorry..!
Imran ya Saki Mirmishinsa kafin yace"Bakamin komai ba..Zan yi kokari na Rage shanta ko Saboda kai da Abba..Ku din wasu Mutane ne masu Muhimmanci a Rayuwata bazan bari Rashin jina da Taurin kai na ya Bata Muku Rai ba..Ammh kasan sai a Hankali..Kamar yadda na Koyi Shanta Rana Tsaka Haka zan zo Rana Tsaka Kaga na Daina Shanta kwakwata..!.
Cikin Farinciki Sagir yace"kai naji Dadi..Allah ya amsa..Ammh wai a ina ka Koyi iya Shanta ne..? Kwarewarka fa yasa na Fara Tunanin Any ba Kwalejin masu Shan Sigarin ka Shiga ka Samu Kwarewa ba..?
Wannan karan Sai da Fararan Hakoransa suka Bayyana Saboda Dariya Wanda ba kasafai ake ganinsu ba Dukan Kafadan Sagir yayi yana Fadin"Ashe kai Dan iska ne..?
Sagir na Dariya yace"Yaushe na Tashi Daga Banzan..?
Imran yace"Duka kai ne...ga ka Banza ga ka D'an Iska Daman ai Telan Mata ai Dan iska ne..!
Sagir ya Harareshi yace"Haka Dai Kace..Miya Hada Telan mata da Iskanci..!
Imran yace"Baka na Gwadasu ba..Ranar fa ina ganinka Kasa Abun gwajinka kana gwada wata yarinya..!
Ya karishe Fada Cikin Zolaya Lokaci Daya kuma Fadin yarinyar Dayayi sai ya Tuna da Abunda ya kawosa nan da nan ya Hade rai Shi Sagir bai ma Lura ba Dariya ya Kwashe Dashi yana Fadin"Ashe Shurun Shurun nan naka Mugun Dan saka ido ne kai a Fakaice..Wlh bana Gwada kowacce Mace sai dai ki kawo Measurement dinki,Wacce kaganta Yaro na ne yake Gwadata bani ba ta mtsa sai an gwadata ne ammh Ni kowa ya sani bana Gwada mace Saboda Kiyaye Addini da Mutumcina..!
Imran bai cemai komai ganin haka yasa ya Dagi kafadansa yana Fadin"Yauwa kace na sama maka aiki ko..?
Kai Tsaye Imran Daya Kagara mganar ta Kare yace"Eh..!
Sagir yaji Dadi nan da nan yace"To kazo na samar maka aikin yi..Kazo zan Koyamaka Daukan Measurement Din Duk Macen Data Dake son sai an Gwadata ga Measurement Imran nan bata da Damuwa..!
Wani Kallo ya Jefama Sagir kafin yace"Kutumar Uba ne..Wlh nafi karfin Wata mace ta Tsaya na gwadata..Baka Tashi bani aikin ba indai hakane..!
Sagir na Dariya yace"Da gaske kake kenan..?
To kazo Gobe sai muga da Abunda Zamu Fara Ni dai kaga Wajen Sana"ata Dinki ne kuma Alhamdulillah Dashi Nake Rufama Kaina asiri Da Mama..!
Imran ya Kada kai kafin"Dakyau..!
Sagir ya Bude baki zai yi mgana kenan Imran yace"Who is She..?
Sagir yaji kamar bai jisa ba Cikin mamaki yace"She naji kace..wa..?ita wacce Zaka fara gwajin a kanta..!?
Karamin Tsaki Imran Yaja kafin yace"Kai fa Banza ne..Wannan Yarinyar ta Jiya Data Kalleni ta Kiramin Tsarin Shedan sannan ta Toshemin Hanci ta Tofar da Miyau Don Ubanta Wari nake ko kuwa Tsabar Raini ne ko Wulakanci..!?
Sagir daya Manta da Abunda ya Faru Tsakaninsu da Inteesar Jiya sai yanzu da Imran din ya Tunamai gabansa ya Fadi Cikin Mamaki yace"Wai Daman baka manta ba..?
Imran ya kara Hade Ransa yana Fadin"Ta ina Zan manta..? Aini bana manta Cin fuska ko Raini..Ni Imran ba Wanda mace Karama irin wannan yarinyar  Zata Raina bane..Ka Fadamin Wata Mara Mutumcin ce So nake na Koyamata Hankali in ta Takamarta Rashin kunya Nine Zan Gyara mata Zama..!Kila Cikin yan iskan matan nan ne masu Zuwa kawo Maka Dinki ko..?
Sagir Yayi Saurin Cewa"A"a Wlh..Don Allah kayi Hakuri Bata sani bane..Kuma Bata san Warin Sigari ne baka gani ba..Wlh sai da Tayi amai fa..!
Shekeke Imran yake kallonsa kafin yace"Oh Daman Duk kana Sane da Abunda ya Faru kenan..?
Sagir yace"Eh Nidai Sorry on Behalf on Her..Kanwatace fa..Diyar kanwar Mama ce Inna Salaha ta Kaduna Shekaranjiya iyayenta suka Kawota Wajen Mama suka Damka Amanarta awajenta Karatu Ta Fara nan Jami"ar Bayero.!
Kamar Imran bazai yi mgana ba sai Chan yace"Naji Dadin cewa ma kanwarka Ce..Zan fi Cimata Mutumci Dakyau..Ai ni Yayanta don Ubanta Kuma ka Fadamata Kada ta yarda mu Hadu Duk Ranar da muka Hadu sai na Toshe Bakinta na Dura mata Hayakin Sigarin sai na Tabbatar Daya Shiga Cikinta,In Aman kayan Cikinta Zatayi Sai dai Tayi..Hukuncin Toshe Hanci Agaban Imran kenan..!
Yana Gama Fadin haka ya Wuce ya Fara Tafiya Cikin Sassafarsa Na koda Yaushe Sagir ya saki baki yana Kallonsa Kafin ya Sauke Numfashi yana Fadin"Inteesar Ta Taro ma kanta Macth bata da yan wasa..Kayyasa..!
Daga haka ya juya ya koma Cikin Shagosa ya Tuna Yadda Imran ya Tsani yana Shan Sigari a toshemai Hanci ko Dashi ne sai sun Hau Sama sun Fado Koma miye bazai bari ma Su Kara Haduwa da Inteesar ba yasan Halin Imran bai da Mantuwa Akan Abunda akayimai.
Koda Imran ya koma Gida ya Iske Abba ya Gama Karatun Qur"anin suna ta Hira da Safiya kamar sun Shekara da Haduwa yana ta Bata Labarin Yanayin Jami"ar Lagos da yanayin Karatunsa Dayake suna Hira ne kan Jami"o"i
Bai ce musu komai ba ya Shige Dakinsa Ammh Tabbas yana Cikin Farimcikin ganin Abba ahaka kan gado ya zauna afili yana Fadin"Abba ba Mahaukaci bane..Abba da Hankalinsa Baffa Kabiru..!
Yafada Lokaci Daya yanajin Suyan Tuna Wasu kalaman da akan Jefe Abbansu dashi na kalmar Mahaukaci.
Wanka ya Shiga bayan ya Fito ya Shafamai Ya saka wani karamin Wando bai ko Saka riga ba,Ya Hau gado yan jin Zuciyarsa Ta Danyi Sanyi Tunda yabama Sagir Sako ya Tabbata kuma Zai gargadeta Bai damu da yadda suke ba Shi Raini ne baya so kuma Ko Munari ce tamai Haukan nan Sai ta gane bata da wayau ballatana Wata Chan Dabam
Yayi alkawarin sai  ya koyamata Hankali,Ya gama Lura Rashin kunya ce da Iyayi na yaran da suka Shiga Jami"a ba Bayero take ba Ko Duka Jami"ar Duniyace akanta Tunda ta Shiga Gonarsa He will Teach Her a Lesson a Big lesson din da Bazata manta ba.
Saboda bacin rai ma yasa ya manta bai Siyo sigarin sa ba Tsaki kuwa yajasa yafi a kirga saboda Haushi.

GIDANMU(OUR HOUSE)Where stories live. Discover now