*HANNU ƊAYA*
(Ba ya ɗaukar jinka)*Rubutun Haɗakar Marubutan Kainuwa*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________**Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da Ya samar da alƙalami, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga ango Aisha miji ga Kadija, Shugabanmu fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW) tare da iyalen gidanShi.*
*Wannan littafi hakkin mallakar Kainuwa Writers Association ne, ba a yarda a juya shi ta kowacce siga ba ba tare da izinin kungiyar ba.*
*Shafi na ɗaya*
*Alƙalamin Muntasir Shehu✍️*
*G.R.A KANO*
Yammacin cike yake da sassanyar iska wacce ta ke zarce fatar jiki ta tafi har zuwa cikin ƙashi ta samar da daddaɗan yanayi ga jikin duk wanda ya rabauta da kasancewa cikin yanayin.
A wannan yammaci a daidai lokacin da duk wasu ma’aikatan gwamnati ko kuma ‘yan kasuwa suke haramar komawa zuwa gidajensu, daidai lokacin motar Hajiya Amina ta faka a kafceciyar harabar gidan nata wacce ta kwashi sarari mai yawa da zai iya wadatar talakawa a ƙalla guda goma su gina matsugunnin da za su rayu har ƙarshen numfashi.
Ta fita daga motar a hankali cikin nutsuwa, ga duk wanda zai kalli allon fuskarta a lokacin, take zai karanto kwantacciyar damuwa da ta mamaye fuskar, wacce hakan ke nuna alamun zuciyarta ma a jagule take, tun da an ce labarin zuciya a tambayi fuska.
Kai tsaye ainahin ginin gidan ta nufa cikin takunta na isa, wanda duk tsanani ba ta iya raba kanta da shi, mukullin motar tata da ke riƙe a hannun hagunta ta ke karkaɗawa a hankali har ta isa ƙofar shiga falon.
Ta danna ƙaraurawar da ke aika sanarwar isowar baƙo daga waje. Yaranta biyu Shaheed da Shahuda da suke zaune a falon suna kallon tashoshin turawa a tauraron ɗan Adam suka ɗaga kai lokaci guda suka kalli bakin ƙofar.
Shaheed ya mayar da duban sa ga agogon da ke manne a bangon falon sannan ya dawo da kallon nasa ga Shahuda.
“Momy ce fa, je ki buɗe mata.”
Shahuda ta miƙe ta je ta buɗe ƙofar.
“Momy! Ashe dai ke ɗin ce, yau kin dawo da wuri fa.”
Hajiya Amina ta yi ƙoƙarin ƙawata fuskarta da murmushin ƙarfin hali.
“Haka ne my dear, yau mun samu sassaucin aiki ne.”
Daidai lokacin Shaheed ya ƙaraso wurin shi ma, suka rungume ta kamar yadda ya zame mu su al’ada.
“Ya school ɗin naku? Ina fatan dai babu wata matsala.”
“Babu matsalar komai Momy, idan ma akwai ai muna da ke a matsayin maganin dukkan damuwoyinmu.” Cewar Shahuda.
Suka yi murmushi duka, sannan suka rankaya zuwa cikin falon.
Shaheed ya koma mazauninsa da ya tashi, yayin da ita kuma Shahuda ta nufi ɗakinta don dubar wayarta da ke caji.
“Hajara! Hajara!”
Hajiya Amina ta shiga ƙwala wa mai aikinta kira, a gaggauce Hajarar ta fito daga sashensu na masu aiki tana amsa kiran.
Bayan ta rusuna gaban Hajiyar ta umarce ta da ta shirya mata abinci a dinning.Ta kai aƙalla mintuna goma tana juya cokali cikin haɗaɗɗen girkin da ke fitar da azabar ƙamshi amma ta kasa kai koda rabin loma ne bakinta, da gaske take jin damuwa na yi wa zuciyarta luguden duka, yayin da ƙwaƙwalwarta ta toshe tsaf ta kasa samar mata da zaruruwan tunanin da za ta saƙa. Wannan yanayi da take ciki shi ya haifar wa da jikinta kasawa a kan duk wani aiki da jiki ke yi a kullum, ta ji sam ba ta son cin abincin gidan, komai ma na gidan ba ya burge ta.
Da ƙyar ta wafci tunanin samar da shawarar barin gidan ta je gidan abinci ta ci a can, a ganin ta wataƙila idan iskar Ilahi ta daki gangar jikinta za ta samu sassaucin damuwar.
Ta miƙe da hanzari, hakan ya ja hankalin Shaheed ya yi saurin kallon ta.
“Mom lafiya?”
“Ina zuwa.” Ta ce bayan ta ɗauki makullin mota ta fice daga gidan ta nufi wani tsadadden gidan abinci na masu wadatar ƙumbar susa.
Saussauƙan abinci ta yi oda, ta fara ci kenan ta ji alamun tsayuwar mutum a kanta, da sauri ta ɗaga kai, suka haɗa idanu, ya sakar mata murmushi, ba ta san lokacin da ta mayar masa da martani ba.
“Kin san kuwa dama ido rufe nake neman ki Hajiya.”
Ta ɗan harare shi da wasa, “Ai kai ni mun kusa raba hanya da kai Alaji, na ga ka yayyafa wa wutarka ruwa tana neman yin sanyi.”
Ya ja kujerar da ke kusa da shi ya zauna, “No, kar ki ce haka Hajiya, lamura ne yanzu suke neman sauya salo, shi ya sa mu ma muke ƙoƙarin yi wa harkar garambawul, kin san an ce idan kiɗa ya canza, to sai a yi ƙoƙarin canza salon rawar ma yadda za ta tafi daidai da kiɗan.”
“Haka ne, amma me ya sa kwana biyu ba ka zuwa ofis? Don a yadda na ji labari ma cewa aka yi ba ka ƙasar.”
“Hmmm, wankiya ce kawai wallahi, amma tun da na gama aiwatar da aikin nawa, satin nan zan koma in sha Allah.”
Ta tura masa lemo gaban sa, “Ka ɗan jiƙa maƙoshinka mana.”
“No bari kawai, zan sa a yi min oda. wai me ma ya kawo ki gidan abinci kike cin abinci daidai wannan lokaci?” Ya sauya akalar maganar.
“Rabon haɗuwa da kai mana, ka san idan rabo ya rantse, sai kifi ya fito daga teku ya samu abinci a tsandaurin ƙasa.”
“Anya? Ni fa wannan falsafar taku caza min kai take yi yasin… any way, ya ake ciki ne yanzu?” Yana girgiza kafaɗa.
Ta kurɓi lemo, ta lumshe manyan idanunta saboda yadda sanyin lemon ya ratsa mata kwanya.
“Kai ya kamata in tambaya, na ɗauka ma da kyakkywan albishir za ka fara tara na cewar an samu sabbin kaji mu je mu ɗauka?” Ta ɗan harare shi.
“Wannan shi ne sara kan gaɓa, neman da na ce ina yi miki kenan fa tun farko.”
“Me ye amfanin lambata da ke wayarka?”
“Haba Hajiya, kin manta cewa tsautsayi na zuwa ba tare da an shirya ba, kuma idan zai zo ba sallama yake ba?”
“Haka ne…”
Ta duba tsadadden agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunta.
“ Lokaci ya ja, ya kamata in tafi, Daddyn su Shahuda na kan hanyar dawowa, zan kira ka da kai na in ji yadda ake ciki.”
Ta miƙe tana tattare komtsanta da ta barbaza a saman teburin.
“Ok, babu damuwa, bari in taka miki.”
Suka fito tare suna ci gaba da tattauna maganar har zuwa bakin motar Hajiyar.
Sai dai wani abu na rashin tabbas ɗin ƙarfen nasara sai motar ta ƙi tashi, ta yi yin duniya amma allamfur motar ta ce ba za ta ba da haɗin kai ba.
Kan Hajiya Amina ya ɗau caji sosai, Allah Ya sa abokin nata mai suna Mustapha wanda ake yi wa inkiya da Yawa bai fita daga gidan abincin ba, ta kira shi a waya ta faɗa masa.
Ya fito ya ɗauke ta a tashi motar suka nufi gida bayan ta yi wa masu kula da gidan abincin maganar za ta turo mai gyara ya zo ya ɗauki motar.
A harabar gidan suke tsaye suna ci gaba da tattaunawa motar mai gidan ta sako kai.
Engr. Sadam ya fito daga motar tashi, yanayin fuskarsa ba za a yanke mata hukunci ba, saboda babu wani saƙo da take ɗauke da shi daga zuciyarsa, ya ƙaraso har in da suke tsaye ya miƙa wa Mustapha Yawa hannu suka yi musabiha. Hajiya ta yi ma sa sannu da zuwa ya amsa ya wuce ciki ya bar su nan a tsaye ko a jikinsa, ganin wani gardi wanda babu alaƙar kusa ko ta nesa da matarsa kuma yake tsaye a daidai wannan lokaci tare da matar tashi bai dame shi ba, rayuwarsu irin ta kowa mai ‘yanci ne, babu mai shiga shirgin wani, babu wanda zai saita wani, kowa na fuskantar inda ya sa gaba ne.
Sun ɗan jima a nan suna ci gaba da tattauna harƙallarsu kafin su yi sallama ta wuce cikin gida cike da farin ciki tamkar ba ita ce a ɗazu damuwa ta yi wa kanta matsugunni a fuskarta ba.
A falon ta iske mai gidan nata tare da Shaheed zaune a kujera ɗaya suna yin magana kan karatunsu, Shahuda na tsaye a gefe tana amsa waya, ganin shigowar Momyn ya sa Shahuda ajiye waya ta dube ta da sauri.
“Yawwa Momy, fita nake so na yi yanzu da ma. Am wannan Abdul ɗin da nake ba ki labarinsa classmate ɗin nan nawa shi ne ya kira ni yanzu za mu zauna kan wani assignment da za mu yi na group, so zan fita yanzun, amma ba daɗewa zan yi ba.”
Ba tare da damuwar komai ba Momyn ta girgiza kafaɗa ta ce “Okay, babu damuwa, sai ki mayar da hankali don ki samu mark ɗin da ya dace.”
Shahuda ta juya ga Dadyn nasu, “Zan fita Dad, sai na dawo.”
Shi ma dai cikin halin ko-in-kula ya nuna babu damuwa, ta shige ɗakinta a gurguje ta shirya, kwalliya sosai ta tamfatsa, fuskarta ta yi ɗau da fentin hoda, kai da gani ka san wannan kwalliyar zuwa wajen shagali ce. Haka ta zo ta gifta su ta wuce bayan ta karɓi key ɗin motarsu ita da Shaheed.
Tana fita ta ɗau waya ta lalubi number Abdul saurayinta wanda da ma shi ne ya shirya mata wancan wasan kwaikwayon na yadda za ta fito su je gurin fatin da aka shirya gudanarwa a ranar. An shirya taɓara ta gaske a fatin don kowa da fushinsa na son nuna tsantsar tsagwaron fitsararsa ya je.
YOU ARE READING
HANNU ƊAYA (BA YA ƊAUKAR JINKA)
Fantasylabarin HANNU ƊAYA labari ne da ya samu rubutu daga tsaftataccen Alƙaluma na marubutan kainuwa, gamayya ce inda marubutan kainuwa suka haɗa hannu wajan zaƙulo muku wannan labarin, marubutan sunyi duba da abubuwan dake faruwa a wannan zamaninmu na ya...