shafi na shidda

2 0 0
                                    

*HANNU ƊAYA*
(Ba ya ɗaukar jinka)

*Rubutun Haɗakar Marubutan Kainuwa*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Shafi na shida*

'''Wannan shafin sadaukarwa ne ga masu yi mana sharhi, musamman Munaya, Maimunatu Omar, Asil, Ummu Araby, Amin Bash, Sadeeya da sauran su'''
'''Masu sharhi da guda-guda za ku ji sunayenku saman feji. Fatan alkairi ga kowa da kowa our fans, muna alfahari da ku irin sosai ɗin nan.'''

*Alƙalamin Muntasir Shehu ✍️*


Da safe misalin ƙarfe takwas Hajiya Amina ta kammala shirinta tsaf na fita aiki, yadda ta tsara kwalliya sai a yi zaton taron fid da gwanar kyau ta duniya za ta je. Babu wanda zai kalle ta a karon farko ya amince ita ce ta fitar da su Shaheed daga jikinta, kullum ƙuruciya ce ke bayyana a jikinta.
Tana riƙe da makullin motarta a hannu ta nufi ɗakin Shaheed don duba shi kamar yadda ta saba.
Yana kwance ringingine a bisa luntsumemen kyakkyawan gadonsa, kafceciyar wayarsa tana hannunsa yana ta shafa ta yana zuba uban murmushi.
Da a ce wani zai yi katarin leƙa wayar don ya dubo abin da ke ƙawata zuciyar tashi yake wannan murmushi to da ya yi mummunan gani, domin kuwa irin shafukan yanar gizon nan ne da suke ɗora hotunan baɗala da na tsiraici shi yake kalla hankalinsa kwance.
Jin shigowar mutum ya sanya shi azamar juyawa ya kifa a gaggauce tare da tura wayar ƙarƙashin filo. Hajiya Amina na tsaye tana kallon yadda ya bi ya rikice, alamun rashin gaskiya ƙarara a tattare da shi.
‘Tabbas wani abu yake aikatawa na rashin gaskiya.’ Wani sashe na zuciyarta ya ba ta tabbaci, amma sai ta ƙi yarda hakan ya tasirantu a cikinta, cikin rashin ɗaukar hakan da muhimmanci ta ƙarasa gare shi tare da dafa ƙafaɗunsa.
“My dear lafiya kuwa?”
“Ƙalau Momi, me kika gani?”
“Na ga kamar kana aikata wani abu ne da ba ka so a gani.”
Da murmushin yaƙe a fuskarsa ya yunƙura ya tashi zaune, “Momi kenan, babu wani abu da nake aikatawa… chat kawai nake yi da mates ɗina na school.”
Ta ɗan yi shiru, duk da a ranta ba gamsu ba, amma ba ta jin za ta tsananta takura masa sai ta san abin da yake ɓoyewa, don haka ta saki zancen ta kama wani.
“Ƙarfe takwas yanzu har ta gota, na san kuma ba lallai ne ma in ka yi brush ba balle a kai ga maganar break fast.”
Ya yi shiru cikin kai tunaninsa wani sashe daban.
Ta sake dafa shi, “Ka dinga ƙoƙartawa kana cin abinci a kan lokaci Son idan ba so kake ulcer ta yi maka mugun kamu ba, ni yau da wuri nake son fita ka ga kuwa babu lokacin da zan tsaya serving ɗinka, don haka ka tabbata ka tashi yanzu ka kimtsa ka je ka yi break.”
“To mom.” Cikin alamun nuna gajiyawa ya furta. Daga haka kuma bai ƙara ko motsi ba bare ta saka ran zai tashi, shi kuma jiran ta yake ta fice ya samu ya ɗauke wayarsa yana tsoron kar ya tafi ya bar wayar ta kunna ta ga abin da yake kalla.
Ta miƙe tsaye, ba ta tafi ba ta ɗan tsaya jim tana ƙara nazarin sa yayinda shi kuma yake jin kamar ya angiza ta ta bar ɗakin. Ta kaɗa kai ta fice.
A falo Shahuda ce ta harɗe kafafu a saman doguwar kujera tana aikin da ya zame mata al’ada wato chatting, a haka Hajiya Amina ta fito ta same ta.
Ba tare da Shahudan ta ɗaga ta kalli mahaifiyar tasu ba gaishe ta.
“Good morning mom.”
“How are you my dear?”
“I’m Ok.”
Duk hakan ya faru ba tare da Shahuda ta ko ɗaga gefen idanunta ba balle ta kalli mahifiyar tasu ta ba ta girmamawa.
Hajiya Amina ta kaɗa kai ta wuce sashen mai gidan ba tare abin ya dame ta ba.
“Kar ki damu, ai ina jin mun kusa kawo ƙarshen wannan matsalar… haba ai kin wuce duk yadda kike zato a gare ni, ok oook zan kira.” Ya yi saurin katse kiran jin shigowarta.
Yadda ta zuba masa idanu sai ya da ji gabansa ya faɗi, amma dayake shi ma ƙwalon kansa ne sai ya girgije duk wata fargaba ya basar ya washe baki.
“Sarautar Mata an fito kenan?”
Taɓe baki ta yi cikin shanye takaici ta ce, “Na kammala shirin fita, muna da mitin kafin shiga office ne.”
“Ok to shi ke nan, sai kin dawo Allah ya tsare.”
“Amin.” Ta amsa tare da juyawa ta fice daga gidan gaba ɗaya.

Wayarta ta zaro daga jaka ta soma lalubar lambar marubuciyar da suka fara ƙulla alaƙa. Bayan wayar ta shiga an ɗaga ta ce
“Ummu Asmin, mun tashi ƙalau?”
Daga can ɓangaren marubuciya Salma wacce take ɓoye sunanta da Ummu Asmin ta amsa. “Lafiya sumul ƙalau Hajiya, ya gida ya nishaɗi?”
Hajiya ta lumshe idanu cikin jin daɗi, shauƙi na fizgar zuciyarta.
“Hmmm, ai nishaɗi kullum cikin samun shi muke, yanzun ma kiran ki na yi in faɗa mi ki jiya na yi sabon kamu.”
Daga ɓangaren Ummu Asmin ta gyara kwanciyarta kan makeken gadonta tare da sauya wa wayar kunne. “Ina jin ki Hajiya. Allah Ya sa dai kifin ruwa kika kamo.”
“Danƙwalele ma kuwa, irin yaran nan ne da wawayen mazan nan ke aura suna tafiya ci-rani su bar su da jaraba a zuciya, mu kuwa kin ga dama damar da muke jira ke nan, shi ne jiya suka zo in shige musu gaba a raba auren.” Cewar Hajiya bayan ta buɗe motarta ta shige.
“Da kyau Hajiyata, ai ni irin waɗancan sakarkarun mazajen kullum addu’a nake yi sun riƙa tafiya suna bar mana kifayen da za mu riƙa samun na gashi, ko ba haka ba Hajiya?” Daga ɓangaren marubuciya.
“Haka ne kam ƙawata, kuma tun a jiya na fara tura mata da ‘yan aike, ga dukkan alamu kuma akwai nasara, shi ya sa na kira ki in faɗa miki da zarar ta faɗa tarko zan kawo miki ki kwashi naki ganimar bayan na kwashi nawa.”
“Ai ko na ji daɗi matuƙa, don kwana biyu babu sabbin hannu.”
“Yawwa, yaushe za ki fara mana sabon novel ne? Kin san muna buƙatar sabon darasi."
Cikin murmushi Ummu Asmin ta yi juyi, “Jiya na fara typing sabo, kuma in ba ki labari daga jiya zuwa yau har na samu kiran wasu yara ɗanyu sun nuna suna son a nuna musu harkar, abin da suke karantawa yana shiga cikin kansu.”
“Da kyau ta wajena, ina son biyu daga ciki kuwa.”
“Ayya! Ki yi haƙuri Hajiya, tun jiya Hajiya Barira ta yi maganar tana son biyu, da ma yaran su uku ne, ni kuma nake son yin amfani da ɗayar.”
Dogon tsaki Hajiya Amina ta ja, “Ban san me ya sa Barira take min shigar hanci da ƙudundune ba, amma wallahi idan ba ta yi wasa ba sai na ba ta mamaki mts.” Ta ƙare da tsaki. Ta kashe wayar ta yasar gefe sannan ta tashi motar ta fice a tamanin.
Tana isa ofice da Grace ta fara cin karo, hannaye biyu ta ɗaga suka rungume juna a matsayin gaisuwa, Jamila ta fito daga nata oficce ita ma tana zuwa Hajiya Amina ta rungume ta tana shafar gadon bayanta, duk dai a tsarin yi wa juna maraba.
Mu’azzam tare da Nura da suka zo wucewa ganin yadda Hajiyar ke rungumar mata sai suka yi tsaki a tare.
“Wannan matar na rasa me take ji a rungumar juna da suke.” Cewar Nura.
“Lalacewar zamani da koyon ɗabi’ar Yahudawa mana.” Mu’azzam ya amsa.
“Bayan hakan ma ba za a rasa wata manufa ba idan an tona.” Cikin nuna ƙullaci Nura ke faɗar haka.
Mu’azzam ya kalle shi a kaikaice, “Kai fa ka ƙi jinin matar nan, na rasa me ya sa.”
“Ka sani mana Mu’azzam, ai kowa ya san yadda matar can ta tsani mazan gurin nan, babu wanda take mu’amalanta da peace of mind, amma ka ga yadda take yi wa mata… ni wallahi wani abu nake zargi.”
“Kul! Kar ka sake ma ka fara wallahi, babu ruwanka da sabgarta.”
Daidai nan suka iso inda su Hajiyar ke tsaye. Jamila ce ta fara gaishe su, suka amsa babu yabo babu fallasa, Grace ma ta gayar da su, ita kuwa gogar ban da hura hanci da shan ƙamshi babu abin da take, a sace ma wani wulaƙantaccen kallo take auna musu ta wutsiyar ido.
Cikin gajiyawa ta saki hannun Jamila ta wuce ofis tana faɗin “Sai anjiman ku.”
Bayan ta shiga ofis ɗin ta sake buɗe wayarta ta kira lambar Nafisa.
Nafisa na can gidanta cikin tarin damuwa, tsoro da kuma fargaba duka. Tun jiya da Hajiya Amina ta turo mata hotunan banza hankalinta ya kai ƙololuwar tashi, gabaɗaya ta ruɗe ta rasa inda za ta saka ranta. Haka ta kwana tana saƙawa da kwancewa
A wannan safiyar ma ta kasa kataɓus ɗin komai, ta kuma kasa kiran ƙawarta ta sanar da ita abin da ke faruwa, kan ta ya kulle tsam yadda  wani tunani ko na je-ka-na-yi-ka ne ya kasa samuwa.
Wayarta ta soma ruri, gabanta ya faɗi ras, fargabarta ta ninku, yayin da zuciyarta ta shiga rawa. Ta duba sunan mai kiran, Hajiya Amina.
Ta kasa ɗaga wayar, maimakon hakan ma sai ta shiga rarraba idanu tamkar tana tsoron wani zai shigo ya gan ta, har wayar ta katse ba ta iya yin kyakkyawan motsi ba balle ta taɓa wayar. Wani kiran ya sake shigowa, wannan karon ta yi namijin ƙoƙarin kai hannunta da ke rawar ɗan mazari ta ruƙo wayar, saura ƙiris wayar ta sufce ƙasa saboda rashin kyakkyawan ruƙo.
Ta ɗaure ta ɗaga kiran, cikin ɗaukewar numfashi ta ƙara wayar a kunnenta.
“Hello.” Aka faɗi.
Ta kasa amsawa.
“Hello Nafisa ba kya ji na ne?”
“Ina…. In… Ina jin ki Hajiya. Ina kwana?” Cikin rawar harshe Nafisa ta yi maganar.
“Lafiya ƙalau Nafisa ya muka kwana?”
“La.. Lafiya lau Hajiya.”
“Jiya kin ga saƙona ko?”
Ta yi shiru.
“Ki yi magana mana Nafisa, ko ba ki gani ba?”
“Na gani Hajiya.”
“To yaya kika ji a ranki?”
Ta sake yin shiru.
“Look Nafisa, ki kwantar da hankalinki ki sa nutsuwa a ranki, babu wata matsala ko abin damuwa cikin lamarin, mafita kika zo a nema miki, ni kuwa ina ganin babu wata mafita da ta wuce ki san kan ki kike nema wa hanyar samun nustuwa ta wata hanyar tun da shi wanda yake da ikon hakan gare ki ya gagara.”
Duk suka yi shiru. Nafisa na saƙa a ranta Hajiya Amina na son warwarewa da kalamanta.
“Kina jina Nafisa?”
“Ina ji ki Hajiya.”
“Ba shiru ya kamata ki yi ba, na fi so mu fuskanci juna ni da ke, ki fito ki faɗa min ra’ayinki da duk wani abu da ke ranki, babu dole a wannan harkar, amma ki sani ba ki da wata mafita da ta wuce wannan, ta haka ne za ki sama wa kan ki ‘yanci.”
Tasirin maganganun Hajiya da kuma rawa da sheɗan ke ta takawa a zuciyar Nafisa ya sa ta fara gamsuwa da tayin Hajiyar, har ta fara ji a ranta za ta gwada ta gani ko da gaske ne akwai biyan buƙata cikin haka.
Farin ciki matsananci ya cika zuciyar Hajiya Amina na wannan nasara da ta samu, nan ta ci gaba da hilatar zuciyar Nafisa da kalaman yaudara har dai ta amince ɗari bisa ɗari za su haɗu gobe a otel amma ba tare da sanin aminiyar Nafisan ba.

HANNU ƊAYA (BA YA ƊAUKAR JINKA)Where stories live. Discover now