*AMINTA* 💘💘
_Na_
Sumaiyya Babayo Abdullahi.
(Sumiee B./Oum Sumayya)*...Reposting*
*DIAMOND CREATIVE WRITERS ASSOCIATION (DCWA)*
_...Promoting Good Writing For Better Society._
Click on the link below to follow our Facebook page
👇
https://www.facebook.com/DIAMONDCREATIVEWRITERS/Telegram... 👇
https://t.me/+GlKUWnWSKJ0LTgEk
Wattpad @ Sumiee_bArewa Books @sumieeb
*GODIYA*_ _Ina godiya ga Allah (S.W.T) da ya bani ikon fara fadakar da al'umma ta sigan rubutu. tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga fiyayen halitta annabi Muhammad (S.A.W) iyalansa da sahabbansa_
*GARGADI* _ƙageggen labari ne, banyi don cin zarafin wani ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane, zuwa gariruwa dama duk wani abu da yake ciki, ƙirƙira nayi domin na nishaɗantar, fadakar,game da ilimintar da mai karatu. Don haka ban yarda wani ko wata ya juya min wannan labarin ta kowacce siga ba tare da izini na ba. Ayi Hattara._
*SADAUKARWA_* _Na _sadaukar da wannan littafin ga Babbar YAYA AUNTY *AISHATU BABAYO* Mrs_ _Abubakar Yakubu_ _*(MASTER*) Allah ya ƙara_ _kauna da_ _fahimtar juna ya_ _azurta ku da zuri'a masu albarka._ _Amen_
*JINJINA* _Iyayena har abada banda kamarku ina alfahari daku, tare da jinjina muku wajen namijin kokarin dakukayi wajen tarbiyantar dani tare dabani kariya arayuwata. Allah yasaka muku da gidan Aljanna._
*GAREKI* Aminiya ta gari bazan manta dake ba Mrs. Hajiya Ummukhulsum Saeed. Allah yabar kauna
_Akaron farko Dana dau Alkalami da sunan rubutu zanyi farinciki matuka idan nayi kuskure aka gyara min ta siga mai kyau. Domin Dan Adam ajizi ne._
_Ina mai kira ga makaranta da ku ɗauki abinda yake daidai mai amfani, ku yi watsi da sauran._
_Ubangiji Allah 🤲🏻 yabani ikon rubuta abinda zai amfani al'umma. Ya kareni da rubuta abinda zai zama kalubale gareni. Amen_🙏Page 1
_Bismillahir Rahmanir_ _Rahim.............✍🏻_
Cikin nutsuwa take tsara kwalliya, wanda ta ƙwashi tsawon mintuna hamsin tana yi fuskarta ya ɗau shaiƙi, inda take fitar da wani irin annuri a lokaci guda farin ciki dake ranta ya bayyana ƙarara a fuskar tata. Duk da kwalliyar ba mai nauyi bace, amma tayi mutuƙar dacewa da tsarin zubin kyakkyawar fuskar tata tare da fito mata da kyawunta na ainihi.
Vibration ɗin wayar ta ne yasa ta dakatawa da abinda take yi, sannan ta miƙa hannu ta ɗaga tana mai kara wayar akunnenta.
Cikin sassanyar muryanta mai cike da nutsuwa ga duk mai sauraro ta furta
"Assalamu Alaikum."
"Wa'alaikis Salam my Malama." aka amsa ta ɗaya bangaren.
"Ke kaɗai a ke jira, da fatan kin gama duk wani shiri naki?"Farin ciki ne ya sake ziyartar zuciyarta, jin abin da ya ce, cikin murmushi ta gyaɗa kai kamar yana ganin ta. Kana ta amsa, "Ina nan tafe my prince, insha Allahu in the next 30 minute I will be there with you."
"OK my Princess." ya amsa"Feedy da Feena sun iso kuwa?" ta tambaye shi.
"Eh! sun iso, ke kawai muke jira." ya bata amsa
"Okay, sai na ƙaraso." ta faɗa a gaggauce game da katse wayar ba tare da ta jira amsawar sa ba.
Cikin hanzarin ta tashi tare da buɗe akwatin kayan ta. fitowa ta yi da riga da wando wanda jarumin nata ya tanadar mata su musamman domin wannan ranar.Rigar ya kasance pink color, inda aka ƙawata gabar rigar da sunan 'Princess' cikin wasu fararren duwatsu masu mutuƙar sheƙi da daukar ido. Wandon fari ne ƙal, wanda ake mishi laƙabi da pencil gaba ɗaya jikin shi crazy
A gagggauce ta zura kayan nata, inda tsayin
wandon da kaɗan ya wuce gwiwarta, haka rigar ya zauna ɗas a jikinta kai kace domin ta aka fidda shi injin. Ɗan kunne ta sa game da sarƙa da suka kasance farare masu sheki da daukar ido, wanda sarƙar yaka ɗauke da harafin *A* a jikin sa, agogo da awarwaro duk fararene masu sheƙi da ɗaukar ido. Sun mutuƙar dace game da fito da ƙwallaiyar tata. Gashin kanta daya sha gyara yake ta sheƙi ta ƙara gyarawa game da sake feshe shi da oil shen. Takalmi da jaka sun kasance farare inda takalmin ya kasance mai rufaffen sama da tsini.
YOU ARE READING
AMINTA
Action*AMINTA* Ƙirƙirarren labari ne, da ya yi dubi da abubuwa da dama da suke faruwa a cikin wannan zamanin. labarin AMINTA ya taɓa fannoni daban-daban na rayuwa daya haɗa da tsantsan amintaka, sadaukarwa, nusar da iyayen kan ƙara kaimi dasa idanu kan ta...