*------------------------------------------*Sintiri take hannu goye a bayanta,tsakanin dakinta ,takai ta komo ga zufa sai zuba yake a jikinta,shigowar wata mata shi yasa ta tsaya tare da dago jajayen idanuwanta da suka koma ja sai kace garwashi,da hanzari ta nuna matar da dan yatsa sannan cikin tsawa da nuna tashin hankali a muryar Tace"Jakadiya karki cemun aikin dana shafe shekaru kusan ashirin da biyu ze tashi a banza,ban son jiiiiii bansooooo"Ta faɗa tana toshe kunnuwan ta gaba ɗaya haɗi da wani jijjiga jiki,zufa ya jika ta sharkaf.
Wacce aka kira da Jakadiya kuwa ta durƙusa a gaban ta kanta sunkuye cikin alamu nuna alhini ga abinda uwargijiyarta ta faɗa, Tace"Fulani ki kwantar da hankalin ki babu dalilin daze sa aikin mu na tsawon shekaru ya warware rana daya tal,kin manta irin aikin da akayi mana shi,kin manta kasadar da mu kayi wajen ganin aikin nan ya tabbata taya rana daya kice ze war..."
Katseta wacce aka kira da Fulani tayi tana zaro dara-daran idanunta Tace"Jakadiya ba kida idon gani ne? Ɗana KASHIM nake so ya zama sarki ,na hana wa kaina kwanciyar hankali don ganin na ɗaura shi a kan kujeran mulki,taya mai martaba zai dawo mun da aikina baya ,aikin da mu kayi ya tashi a banza kenan,idan har mai martaba ze san ya gasa a tsakanin 'ya 'yan shi to tabbas mun kashe maciji ne bamu sare kanshi ba."
"Amma ranki shi daɗe abinda mai martaba ya yi yau nasan munafunci wannan malamin fadan ne dan shi yake so ya canza wa mai martaba ra'ayi a kan KASHIM,ba yanda za'a yi sauran yan'uwan KASHIM su samu daman jiyo kamshin mulkin Daura bare kuma wannan ɗan buzayen da kowa ya manta dashi bame tambayarshi ma bare a sako shi cikin lissafin magadan gidan nan"
Cewar Jakadiya.
Wani numfashi Fulani ta sauke tana mai da hannuwanta bayanta sannan,Tace"Idan har malamin fada yana daga cikin masu mun zagon ƙasa to tabbas lissafin kwanan mutuwarshi ya matso domin can yafi cancanta dashi"
Murmusawa Jakadiya tayi a zuciyanta tana faɗin 'Zanje fi tsuntsu biyu da dutse daya'.
*******************************************
Kiran sunan Ummi yake tayi tun daga bakin ƙofar sashanta har ya shigo palon ta,tashi tayi tare da rangwaɗa guɗa hadimanta suna mata kirari kafin taja hannun shi zuwa uwar 'daka ta kullo ƙofa,rungume ta yayi cikin farin ciki da annashuwa wanda ya kasa barin fuskan shi sannan,Yace"Ummi nime sa'a ne ,Ummi ina godiya da Allah daya bani ke a matsayin mahaifiyata a jiya na riga na cire rai da mulkin daura amma bayan abinda mai martaba yayi yau nariga nasa a raina ba gudu ba ja da baya"
Murmushi ta ƙara saki wanda a kallo zaka ɗauka ba zata iya aje 'da me shekaru ashirin ba duba da ƙaramin jikin da take dashi ,hannun shi ta riko,Tace"Shalele babu abinda ze gagareni ni Fulani Mairo indai ina da rai da lafiyata kai ne magajin fadan nan,amma fa Shalele duk wasu tuggu da makirci ba wanda ban yi ba amma ba nasara narasa yanda akayi me martaba ya canza ƙudurinsa na ɗaura KASHIM a kan kujeran mulkin nan bayan kasan duk masarautar nan ba wanda be san cewa KASHIM shine yarima me jiran gado ba"
"Nidai Ummi koma me nene a daɗin mu sannan dole mu sake shiri dan ganin cewa nine wanda aka zaba matsayin sarkin Daura"
*Muje zuwa*
*Mrs Deerah*
*Share & comments fisabilillah🙏*
YOU ARE READING
GIDAN MULKI
General FictionƘirƙirarren labari ne daya kunshi soyayya,makirci,da kuma daukar fansa...💃🏼💃🏼💃🏼karku bari a baku labari