Page 2

6 0 0
                                    


"Asalin labari"

Mai martaba ya kasance shine ɗa na farko a wurin mahaifiyarshi, mahaifinshi sarki Abdulsalam ya kasance adalin sarki wanda suke su uku wurin iyayensu amma ko wanne da mahifiyar shi,shine na farko sai kanin shi Muhammad sani sai na ukun su jafaru ,a lokacin da mahaifinshi ya rasu sai mulki ya koma wurin Abdulsalam ,an kai ruwa rana kafin a bashi sarauta saboda ko wanne cikin su ya yunkuro yanaso amma sai aka sanya gasa a fada duk wani wanda ke rayuwa a cikin fada indai ya haura shekara 15 zeyi zabe,Hakace ta kasance cikin ikon Allah kuma sai Abdulsalam ya lashe wannan gasa."

   Sannan ƴan'uwan shi aka basu matsayi a fada suma,shi Muhammd sani aka bashi Galadima sai jafaru kuma waziri,babu yanda suka iya haka suka amsa amma zuciyoyinsu cike take da bakin ciki.

  Bayan wasu shekaru Abdulsalam har lokacin Allah be bashi haihuwa ba matan sa biyu sai kwarkwarori amma shiru-shiru babu, ko batan wata babu wacce ta taba yi hakan ne yasa wani abokinshi a cikin katsina attajirin mai kudi ya bashi auren ƴar shi da shigowarta kuma Allah ya nufeta da samun ciki amma ko wata biyu beyi ba ƴan 'uwanshi suka shiga suka fita aka zubar dashi daga nan sai da aka shafe shekara kusan biyar tana ɓari duk ciki babu wanda Allah ya bada ikon fitowar shi duniya a haka ne wata tafiya ta kama mai martaba zuwa garin zazzau akan wani taro daza ayi da sarakuna,ashe tafiyar sa'a ce don kuwa zuwan shi garin zazzau Allah ya hada shi da ƴar sarkin zazzau Gimbiya Zeenatu be dawo garin daura ba sai daya tabbatar ya auro Zeenatu sannan."

 

    Bayan ya dawo yake sheda wa matar shi da ƴan'uwan shi auren da yayi sannan zata tare nan da sati biyu,babu wanda be girgiza da wannan aure ba don ko sanin kowa ne da karfin Masarautar Zazzau a nigeria yin wannan aure da Sarkin Abdulsalam yayi kamar kara wame karfi,karfi ne,matan sarki ko wacce ta bazama,mai zuwa wurin boka nayi masu bin malamai nayi, a haka suma su galadima da waziri suka sake canza wa matar sarki ra'ayoyinsu akan sarki"

   " Rana bata karya don ko Amarya Gimbiya Zeenatu ta tare Gidan mulki duk wasu aikin sharri anyi amma ba wanda yayi tasiri saboda itama iyayenta ba hakan nan suka barta ba amma su magunan tsari kawai suka yi mata wanda babu shirka a ciki kuma ita kanta Gimbiya Zeenatu tsayayya ce a fadar su batada tsoro bare shakka wani dan adam,yakasance ma daga sarkin zazzau sai ita wani lokacin ma ita ke zartar da hukunci a masarautar".

  Bata wuce wata 'daya ba ta samu ciki amma ganin mai martaba bai taba haihuwa ba kuma tun zuwanta ta fahimci mugun abun da wasu ke nufin ta dashi shiyasa ko mai martaba bata sanar dashi cikin da take dashi ba,a lokacin da cikin yakai wata biyar yafara fitowa har mai martaba ya fahimci haka amma ta roke shi kar ya bari kowa ya sani ba karamar farin ciki yayi da hakan ba.

  

   "Ya kasance ta killace kanta daga fitowa bame kaninta,dama kuma ba zaman lafiya take da matan sarki bare su shigo mata,jakadiya ce kadai ke shigowa itama ta lura tana da wani kuduri a ranta don haka tun bata fi sati biyu ba a gidan ta hanata shigowa Sasanta".

   Tunda cikin nan ya shiga wata biyu tayi aike masarautar zazzau a aiko mata da unguwar zoma da dukkanin abunda take da bukata na rainon danta saboda sunyi magana da mai martaba akan takoma can garin zazzau ta haihu ya hana don gani yake kar tafita a bita a kashe ta saboda wani irin sonta da Allah ya daura mishi,zuwan baƙin zazzau shi yaja hankalin maƙiya har suna dasa ayan tambaya akan haka,hankalinsu bai kwanta ba har sai da suka gano cikin da Gimbiya Zeenatu ke dauke dashi,wanda wani taro da aka sanya ta harbi a masarauta kuma Gimbiya tun fil'azal tana yaki,harbi da sauransu don kusan a yanzu akace za'a kawo mata hari zata iya kare kanta saboda mace ce mai kamar maza, son irin wannan gasa shine dalilin daya sata fito wa gani duk da ta nuna sha'awan yin gasan amma Sarkin abdulsalam ya hanata shine ta fita gani,a nan ne cikin ta dan wata takwas da kwana goma ya bayyana.



Muje zuwaa💃🏼

Kar a manta da sharing

More comments,more typing ❤️

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 21, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

GIDAN MULKIWhere stories live. Discover now