Chapter 3-4

71 5 0
                                    

*💥GUNTUN GORO..!💥*

_Zainab Habib(Mom Islam_

*✨TEAM GAWURTATTU BIYAR*

Dama gareku masu son a tallata musu hajarsu cikin sassauƙan farashi suyi magana ta wannan number 08141799224

Free page 3-4
Cikin tsananin damuwa na fice, kai tsaye shagon Dauda dake kallon ƙofar gidanmu na nufa, ina zuwa na samu da mutane na nemi kan dogon bencin dake ajiye a gefe na zauna tare da rafka uban tagumi, leƙowa Dauda yayi cikin zolaya yace ",ƴar Abba me kikeso nasan dai bakya wuce kayan kwalliya .kasancewar yana siyarda su cosmetics ne,
Niko nafara nisa a tunani sbda a halin yanzu Abbana kawai nake tunani, tunda naga dare yayi.
Ganin bance komai ba,
Cikin ɗaga murya Dauda yace "ƴar Abba...
Da sauri na ɗago jajayen idanuwana na kallesa kana nace "na'am ",
"Akwai damuwa ne na ganki haka ƴar Abba.."
Nace "ɗazu na fita nabar Abbana a gida, nadawo kuma na samu baya nan ",
Na ƙarashe magnar ina share hawayen dake sintiri a fuskata tashi ɗaya.
Gani nayi Dauda ya fito ya zauna can nesa dani sai naji yace "haba ƴar Abba ai da kin kirashi a waya da kinji inda yake ",
Nidai burina kawai inji abinda ya sami Abbana sbda kwata-kwata hankalina ba a kwance yake ba.
Dauda yace "ai wani Alhji ne yake taimakawa marasa lafiya shine Abban naki suka tafi shida Malam Ahmad, sbda akwai babban asibiti a cikin gidan bayan haka ma ina tunanin yabawa Abbanki gida a cikin gidan nasa, kinsan gidan kamar gari guda yake ",
Tunda Dauda ya fara magana nake jin zuciyata na zafi, duk da nasan taimakawa Abbana za'ayi to ni me yake nufi dani ?,in zauna a gidan ni ɗaya ko kuma kawai ya daina sona ne, bayan kafin in tafi sai da nace masa na amince zanje aikatau ɗin.
Maganar Dauda ce ta dawo dani daga tunanin dana fara tafiya, na miƙe jiki a sanyaye nace "to na gode barin koma gida ",
Tsabar baƙinciki ne ya hanani kiran Abba a waya, na koma gida naci kuka na godewa Allah, haka na kwanta banci komai ba,
Kiran sallahar asbha tare da ruwan da naji anfarayi ne ya tasheni, sbda tashi ɗaya gari yaɗau sanyi, abin rufa na ɗauka tare da fitila naje nayi alwalah na dawo na kabbara sallah, ina idarwa nayi adu'oi na ninke sallahyar tare da komawa na kwanta dan ji nake kamar bani da lafiya.
Bani na tashi ba sai da gari yayi haske sosai na miƙe ina salati, na ɗauko dankali na da na kasaci tsabar bakinciki, ba tare da na yi masa komai ba, na juye a kwano nasa miyar Allah ya taimaka batayi tsami ba na faraci.
Ina gamawa na ɗauraye kwanukan naje na hura wutar ruwan wanka, wutar na kamawa na ɗora ruwa, cikin ikon Allah yayi zafi na juye naje nayi wanka, ina fitowa na wuce ɗaki da gudu sbda sanyi da akeyi.
Duk da bacin ran da nake ciki bai hanani yin kwalliya ba, duk da yau ba wata kwalliya nayi ba, bayan mai dana shafa sai powder da tozali dana sanya a idona, na nufi gurin kayana na ciro doguwar rigar ta atamfa mai ratsin blue da fari tana ɗauke da manyan flowers, anbi kowanne gurin ado da stone fari mai ƙyalli, kasancewata mai jiki amma ba can ba, da tsayi dai-dai misali yasa rigar tayimin ɗass dama ɗinkin agwada ne.
Bayan na gama shirina na nemi guri na zauna na fara tuno maganar Dauda mai shago, dayace min wai Abbana yana gidan wani Alhji kuma zai taimaka masa,
"Shin Abban yasan Alhajin ne? ko kuma ciwon ƙafar ne ya ishesa ",ni kaɗai naketa sumbatu na haɗe da fashewa da matsanancin kuka.
Sallamar malam ahmad ne ya sanyani miƙewa ina share hawayen fuskata da hannu badan zanyi tunanin hodar dana shafa ta goge ba sbda ina cikin damuwa.
"Wa'alaikumussalam"
Na amsa masa fuska a tamke, a iya tunani ne shine yayiwa Abbana hanya, tunda gashi shi ya dawo amma Abbana yana can.
Har cikin gidan ya shigo ya tsaya a bakin ƙofa yana mai kallona haɗi da cewa ",Ilham Abbanki ne ya aikoni, yace wai ki shirya za'azo ɗaukarki da misalin ƙarfe ɗaya na rana ",
Kallonsa kawai nake sbda, tsanarsa da nakeji yasa magana ma na kasa yi masa tunda haka ya zaɓarwa Abbana duk da nasan Abban ba yaro bane.
Cikin takaici na buɗi baki kamar mai koyon magana nace "to"
Na koma ɗaki, shima ya fita.
Ina nan zaune a ɗaki in saƙa in warware har lokaci ya tafi,
"Nakasa gane inda Abba ya dosa, yana nufin zamubar gidannan kenan mu koma gidan wani?, wannan ai ƙasƙanci ne ",
Na faɗa ina mai jin ciwon tafiyar da Abbana yayi.
Kiran sallahar ƙarfe ɗaya danaji anyi ne yasa gabana tsananta faɗuwa na miƙe ina ambaton sunan Allah, gashi kaf garinnan babu danginmu sai ƴan uwa da abokan arziƙi, "to gurin wa zani ?wazai taimaka min ?" da wannan tunanin naje na ɗauro alwalah na dawo na kabbara sallah, ina idarwa na dinga kwararo adu'a akan idan tafiyar nan tawa ba alkairi bace Allah ya wargatsata.
Horn ɗin mota da naji a ƙofar gidanmu ne yasa gabana tsananta faɗuwa na miƙe kamar mara gaskiya ina ta zancen zuci.
"Aslamu alaikum " naji an rangaɗo sallama batare da nasan maiyin sallamar ba, na amsa da wa'alaikumus salamu "na yafo ƙaramin mayafina na fito domin inga mai sallamar.
Ina fitowa naga wani matashi hannunsa riƙe da mukullin mota yana kallona, nima kallonsa nake daga ƙarshe "nace kana son wani abu ne ?"
Drivern yace "dama ance inzo mu tafi ne " mtsw naja tsaki, a hassale nace inji wa ?nifa babu inda zani kaje ka cewa Abban ni babu inda zani karma ka kuma dawoww idan ka sake dawowa wallahi sai nayi maka ihu ince waiyo ga kwarto ".
Dajin haka driver ya haɗe hannayensa
biyu alamun ban haƙuri yace "naji bazan kuma dawowa ba, amma kizo o mu tafi jikin mahaifinki ya tsananta ",
Abinka da ɗa da uba nayi sauri na shiga ɗakina na ina kuka na ɗauko wata ƴar ƙaramar jakata wacce ke ɗauke da kaya kala huɗu sai hijab biyu da niƙab da safa na fito ina cewa "muje "muryata har rawa take.
Bayan drivern ya shiga nima na shiga gidan gaba muka shilla titi.
Cikin hukuncin ubangiji muka iso Sharaɗa, a baki wani tangamemen gida naga drivern ya ɗan tsaya yana danna horn alamun a buɗe masa, niko sai ƙarewa tsarin gidan kallo nake, har ga Allah gidannan ya haɗu, sai kace ba'a talauci a duniya ?" na tambayi kaina ina daɗa ƙarewa gidan kallo kamar ƴar ƙauye .
Tafiyar da motar naji tanayi ne ya sani, mayar da hankalina ga inda muka dosa,
Muna shiga sai na raina kaina, sbda iya haɗuwa gidan ya haɗu, gashi ƙato ga flawoyi masu kyau ga gurare daban daban, kama daga gurin wanka harda gurin lilo, can gefe kuma wata haɗaɗɗiyar kujera ce mai masifar kyau.
Bayan drivern yayi parking yayi min izini da in fito, na fito da ƴar jakata wacce na ɗora a kan cinyata tun shigata mota,
"Biyoni muje ciki"
"To "nace masa ina bin duk inda naga yayi.
Wata hanya mukabi wacce ta sadamu da haɗaɗɗen palon gidan, nanfa naci gaba dabawa ido abincinsa ta fannin kallon kujerun dake zagaye a palon, daga ganin tsarin gidan zaka tabbatar da naira tayi kuka, balle ka shigo ciki,
"Kizauna "
Drivern yace min na zauna kamar inda ya faɗa.
Gani nayi ya tafi ya barni, bakajin ƙarar komai sai na AC daTV, a halin yanzu kallonTV baya gabana sabda, burina kawai inji inda Abbana yake,
Na jima a zaune, kafin wata farar mata mai jiki a ƙalla zatayi shekaru hamsin ta fito, farace tass fuskarnan tata tasha fashin goshi, hannunta kuwa yaji zobunan gold, cikin fara'a ta ƙaraso ta zauna kujerar dake kallon tawa kafin tace "ashe har kun iso ",to waye ya faɗa mata?",
Katse tunanin nawa nayi da cewa "eh ina yini hajiya ",
"Lafiya lau ya karatu ya ƙoƙari ",
Na amsa da lafiya lau ina mai sunkuyar da kaina ƙasa.
Miƙewa naga hajiyar tayi taje gaban wani katon fridge mai rijiya ta ɗauko min ruwan gora, ta buɗe wani bokiti ta ɗibo min cincin da ta ajiyemin a gaban wani tabur dake gabana, har yanzu bata zauna ba naga ta wuce ciki, bata jima ba sai gashi ta fito hannunta riƙe da plet na abinci, mai ɗauke da shinkafa da miya da vegetable, ta ajiye a gabana.
"Kici ƴata nasan ba lallai kinci abinci ba "
"To "kawai nace na fara cakular abincin kamar wacce take koyo,
Ban wani ci da yawa ba na ajiye cokalin nasha ruwa, ina jira inji musabbabin kawoni gidannan amma har yanzu banji tace "komai ba ",
Sai da muka ɗau tsawon lokuta a zaune kafin naji tace "kece Ilham ko ?"
Na amsa da "eh hajiya nice "good babanki ne yasa a taho dake a bisa yardarsa akan cewar zaki fara aiki a gidannan, da kuɗin da za'a biyaki a kaishi ayi masa magani ",
Gabana na tsanannta faɗuwa idona ya kaɗa yayi jajir nace "eh na sani ina Abban nawa ?"
Hajiyar tace "yana hospital ana yi masa aikin ƙafar ",
"Wato har Abba yakai kansa batare da ƙara shawartata akan ko na amince da aikin na ko ?hmm lallai Abba ",
Na faɗa ina ce mata "to Hajiya ko zan iya ganinsa ?",
"Eh zaki iya ganinsa sai dai ba'a gidannan yake ba yana asibitin Murtala ", a razane na dafe ƙirji tare da cewa "asibitin Murtala kuma ashe abin yayi yawa, nida akace yana asibitin gidannan "na faɗa ina share hawayen da suke ambaliya a fuskata, Hajiyar ta ɗaga waya ta danna number driver, bai jima ba yazo ya durƙusa a gabanta, cikin bada Umarni Hajiya tace "ka kai Ilham asibitin da aka kwantar da babanta, driver yace "an gama hajiya taso muje "na miƙe jiki a sanyaye, dole nabar kayan anan na wuce muka shiga mota muka lula asibitin.
Muna isa, driver yayi parking tare da cewa "kiyi sauri lokacin ziyara ya kusa ƙurewa "nayi azamar fitowa, yana gaba ina binsa a baya, har muka shiga wani ɗaki mai lamba 5, muna shiga na hango Abbana a kwance an naɗe ƙafarsa da bandeji , iya yau ya rame sosai, nikam na rasa ganewa shin ciwon ne ya tashi ko kuma shine ya kawo kansa har yanzu ban sami mai bani amsa ba, tarin da naji yanayi ne ya sani ƙarasawa kusa dashi ina cewa "Abba sannu ya jikin "
Cikin murya irin ta marasa lafiya Abba yacemin "jiki da sauƙi na warke yau akayi aikin zuwa jibi idan sunga jikin ya warke sunce zasu sallamemu ",nace to alhmdulilh Abba yanzu gidan aikin kenan zan koma ?"Abba yacemin eh man ai sai kinyi na wata bakwai ",na zaro ido, saboda kar in tayarwa da Abbana hankali yasani ɓoye damuwata nace masa karka damu Abba, lafiyarka ta fiyemin komai a duniya, farinciinka shine nawa, samun lafiyarka itace farinciki na "Abba ya shafi kaina yana sanyamin Albarka, shigowar likitan dake dubashi ne yasa na koma kan kujera, sai yanzu driver yace "baba ya jikin dai ?" Abba ya amsa fuska a sake, "na sami sauƙi alhmdulilh ",
Driver yace "zamu wuce toh "babu inda na iya haka muka dawo gidan su Hajiyar, wannan karon na sameta ita da wani saurayi wanda nake tunanin kamar na san fuskar, nazari na shigayi tare da tinanin a ina na taɓa ganinsa ?",
Kyakkyawan saurayi ne dogo fari tass ɗan shekara 32yrs fuskarsa masha Allah, a taƙaice dai shiɗin ba mummuna bane,
Kansa na kan cinyar hajiyar yayinda gangar jikinsa ke kan kujera 3 sitter, da sallama na ƙarasa kafin nace "hajiya mun dawo "Hajiyar na faɗaɗa fara'arta tace "ƴata zoki zauna ", ta nuna min kujera mai zaman mutum ɗaya, yaron nata da naji ta kira da my son naji yace "momy wannan kuma wacece ?",hajiyar ta shafi kwantaccen gashin kansa kafin tace ",ka mance maganar da akayi da dadynka jiya akan ƴar aiki da kuma rashin lafiyar mahaifinta ?"gani nayi ya taɓe baki haɗi da galla min harara, nikuma sunan data kirani dashi ne yai mugun ɓatamin rai, wai ƴar aiki mtsw.
"Oh momy yanzu taje ta gyaramin part ɗina Ibrahim na nan zuwa anjima "waro ido nayi, sbda a halin yanzu na ganoshi sarai, ga kuma yanayin maganarsa kamar ta mace, wato shine ko ?"lallai zan gasa maka aya a hannu " na faɗa ina kawar dakai daga kallonsu.
Nasan shikam bai ganeni ba, amma ni na ganesa, sbda wannan ƙaton gilashin danasa wanda ya mamaye ilahirin fuskata, jira kawai nake inji hajiyar tace "tashi ki tafi ", amma shiru ina zaune kamar gunki, ganin hajiyar bata sake wai-wayata ba, yasani kallon TV badan ina fahimtar abinda akeyi ba, kawai dai mutanen dake drama nake kallo a tashar arewa24.
Bayan wasu sa'oi,
Najiyo muryar hajiyar na cewa "ke Ilham jeki gyara part ɗin my son anjima yanada baƙo "na amsa da toh "dama burina inbar gurin nagaji da zama agurinsu,
"Ina ne part ɗin?"
"My son oya jeka nuna mata yau tazo fa ",
Fuska a yamutse haɗi da kallon ƙyama da wulaƙanci, ya yaso bai cemin komai ba ya fita a ƙofar shigowa palon Hajiyar nima na bishi,
Mun ɗanyi tafiya sannan naga mun iso wata ƙofa mai ɗauke da mudubi, yana zuwa ya danna wani abu a jikin bango naga ƙofar ta buɗe, ya shiga nima na shiga, irin haɗuwar palon hajiya kusan iri, ɗaya da nasa, amma a nashi palon akwai wani tangamemen Frame mai ɗauke da photonsa wanda ya baiyanar da kyawun fuskarsa, gashi gunin ban sha'awa murmishi yake, niko nace "duk wannan cin maganin da yakeyi dama yana dariya ?",
"Inkin gama nuna ƙauyancin kizo ki wanke min toilet ki gyaramin ko ina nabaki 30mins "rai a ɓace na kallesa sai kuma na sunkuyar da kai, banason in nuna raina ya ɓaci ya sami damar turamin haushi, batare daya nunamin toilet ɗin ba ya fice yana waƙa ƙasa-ƙasa.
Zubewa nayi akan kujera tare da zuba tagumi nace "shikenan na ƙanantar da kaina na shiga uku, koma zagina mutan gidan sukayi haka zan daure Allah ka wadatamu ",
Cikin azama na miƙe na buɗe wata ƙofa wacce nake da tabbacin nan ne bedroom ɗinsa, sbda gado dana gani da mudubi da drowa, gadon na fara gyarawa kafin nace na wanke toilet nama rasa ya zanyi in tsara abinda zanfara, duk abinda yazo min shi nakeyi, tashi ɗaya na gama gyara komai cikin hanzari na kunna burner nasa turaren wuta ƙamshi ya game ɗakunan duka..!

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*
_Miss Hajo_

Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k

*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.

Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎....

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*

GUNTUN GOROWhere stories live. Discover now