*💥GUNTUN GORO..!💥*
_Zainab habib(Mom Islam_
Domin samun complete a arewa books danna wannan links ɗin👇
https://arewabooks.com/u/momislam22Free page 9-10
Ƙirar Tecno Pova Neo "Wannan kuma fa"
Momy ta tambayi Ibrahim tana kallonsa,
"Na Ilham ne, momy kar a mayar damu ƙananan mutane kinsanfa babban taro zamuje"
Momy tayi murmishi kafin tace "to shikenan"
Ibrahim yace "akwai sim card a ciki nayi register "
Zai ƙarayin magana yaga Mubin ya fito
cikin takunsa na ƙasaita, yana sanye da shadda mai ruwan sararin samaniya, yayi kyau matuƙa, kama daga shaddar jikinsa takalmin ƙafarsa da zobunan hannunsa uwa uba wayarsa, zakasan nera ta zauna.
Sai da ya gama aikamin da saƙon harara sannan ya nemi guri ya zauna yana gaishe da momy,
Cikin sigar tsokana Ibrahim yace "ai dana sani anko nayi mana"
"Walhi zakaci ubanka mtsw"
Mubin ya faɗa yana miƙewa a hassale,
Ƙarfe 9:11am muka fice daga gidan,
Kasancewar jirgi muka hau, muka isa nan na nan,
Daga airport mota tazo ta ɗaukemu zuwa anguwar Agege, kasancewar acan M.M Chicken republic ɗin yake.
Gurin yayi kyau sosai ba wani jimawa mukayi ba, muka wuce inda ake taron, kasancewar har an fara.
Muna isa bayan drivern dake jigila damu yayi parking a harabar gurin taron, muka fito, Ibrahim ya dawo da baya cikin ƙasa da murya yace "ka riƙe mata hannu pls karsu fahimci wani abu" mtsw" Mubin yaja tsaki kafin ya kalli momy da batasan wainar da suke toyawa ba yace "I B wallahi zanci uwarka ni zaka kunyata kuma ka jamin raini a gurin wannan banzar?"
Tabbas wannan kalmar tayimin ciwo amma sai na daure sbda gudun saɓa alƙawarin Abbana,
Wata mata mai suna Amanda, wacce a ƙalla zatakai shekaru 35 itama babba ce a gurin siyar da abincin nasu, ta taho cikin girmamawa taɗan durƙusa tace "good afternoon mah" bayan momy ta amsa ta juya ta gaishe dasu Mubin harda nima da naketa rarraba idanu.
Hannuna ta kama dana Mubin ta haɗe guri ɗaya, momy ta miƙomin hand bag da bansan ma anzo da ita ba, muka shige ciki, su momy na biye damu a baya.
Da shigarmu gurun ya ɗauki tafi,
A wata ƴar madai-daiciyar kujera muka zauna, wacce jikina da nasa na gogar juna, banso hakan ba sbda ina tunanin kamar hakan bai daceba, shiba muharramina ba amma nake biye musu.
A ɓangaren Mubin kuwa yayi kicin-kicin darai, inda kasan an aiko masa da ranar mutuwarsa,
A ɓangaren momy da Ibrahim sunata waya, Naji momy na cewa "idan kun iso ku sanar dani sai in fito"
Sai kuma naga ta miƙe, bata jima ba ta dawo da wasu mata su uku, da alamu daga Kano ko wani garin suke, dan naga ɗaya tayi kama da Ibrahim.
Bayan sun zauna akaci gaba da gabatar da taro akan abinda ya taramu,
Wani Hamshaƙin mai nera yana ɗaya daga cikin masu faɗa a ji a garin ya miƙe, bayan an miƙa masa abin magana speaker yayi bismillah kafin ya fara jawabi..
"Alhmdulilh naji daɗin wannan taron da aka shirya, duba da taimako da gudun mawa da wannan M.M ke bayarwa, muna sane da zakka da ake cirewa duk shekara da sadaƙatul jariya kana da ziyartar marayu da marasa lafiya, munji daɗi sosai muna godiya" aka hau tafi raf-raf-raf,
Yaci gaba da cewa "Bazan taɓa mancewa da wata rana da Iyyana bata da lafiya, bana nan gurin da naje babu network, kuma lokacin ban taka muƙamin dana taka a yanzu ba, in taƙaice muku zance anyita neman taimako akan tiyatar da za'ayi mata a cire mata wani ciwo daya fito mata a cikinta an rasa, kaf faɗi da girman garinnan babu wanda ya taimaka mana, bayan na dawo muka je gidan TV neman taimako, ko za'a dace, washe gari mukaji alart na sama da kuɗin da muka buƙata, a take a gurin muka turawa masu hospital, washe gari aka shigar da ita ɗakin tiyata, cikin hukuncin ubangiji anyi da kwanabiyar muka san anyi cikin nasara, daga nan muka fara bibiyar mutumin daya turo mana da kuɗin, koda yace a ɓoye sunansa sai da muka dage da roƙon Allah mutumin ya baiyyana, ashe Alhaji Abdullahi Zakin naira, wanda sunansa yayi shura a ƙasar nan ciki harda ƙasashen waje",
Yana kaiwa nan ya fara kuka a abin magana aka fara tafi,
Haƙiƙa jikina yayi sanyi, maganar mutum da ya cigaba ne yasa na kuma nutsuwa sosai,
"Babban farincikina anan shine ganin tilon ɗansa wanda shima mukeda tabbacin ya yi halin mahaifinsa da nutsatsiyar mata mai hankali, dan koba'a faɗaba ɗanmu ya zaɓawa ƴa'ƴansa uwa ta gari.."
Ya ƙarashe maganar yana cire glass ɗin dake manne a idonsa yabar gurin da sauri,
Mai gabatar da taron ne ya fara magana cikin harshen YARBANCI yana cewa "Alhaji Nuru Mustafa ya bawa babban ɗan Alhaji Abdullahi tare da matarsa kyautar 500k"
Kowa ya hau murna, ƴan gulma nayi suna cewa "an ƙarawa mai ƙarfi-ƙarfi gaskiya bai dace ba, wasu na cewa yayi ne dan neman suna.
Bayan an raba kyaututtukan da aka tanadar da abinci order daga hotels, dasu drinks masha Allah anci ansha aka buƙaci momy ta fito, bayan momy ta fito tayi sallama tare da bismillah haɗi da godiya da karramawar da masana'antarsu ta samu, uwa uba gashi dubban mutane sun ƙara sanin da gidan abincinsu,
Daga nan Ibrahim ya tashi yayi godiya wa Alhj Nuru,
Aka buƙaci Mubin daya fito yayi nasa jawabin ya kuma faɗi abubuwan da suke so dakuma wanda suke shirin aiwatarwa.
Sai yayimin sana'ar tasa wato harar, mutane sun ɗauka kallon love ne har suna tafara, yana tashi ya isa gurin kafin ya fara magana yace "A matsayina na ɗan Alhaji Abdullahi Zakin Naira ina mai yi muku albishir wanda zamu fara gabatar dashi end of this month amma ba lallai in sanar muku da abinda muka shirya ba, zadai a sake yin wani sabon taron a ƙarshen watannan"
Daga nan ya ƙara da cewa "ina miƙo godiyata ga Alhj Nuru kuma uba a gurina akan kyautar da yayi mana nida wify ɗina",
Nan da nan gurin ya kuma ɗaukar shewa da tafi, Ibrahim ya matso kusa da Mubin yace "ya kamata aɗan saka kiɗa mu taka",
Mubin tsabar haushi da takaici bai ko kallesa ba, cikin rashin tsammani da suɓutar bakin da baiyi zaton idan ya furta za'a sami damuwa ba yace "kiɗa me kake...
Ashe a speaker yayi maganar aiko aka sake kiɗan yarbawa, Ibrahim ya kwashe da dariya, Momy da ƴan uwanta dake kallonsu duk dariya suke, banda ni da na faɗa kogin tunanin Abbana.
Hannuna da aka kama ne yasa na kalli wacce ta kama hannun naga ba matar ɗazu bace wata ce, amma da 'alamu musulmace duk da bata sanya mayafi ba,
Har gurin Mubin ta kaini ta haɗa hannuwanmu guri ɗaya, na kalli wasu mata da miji da suketa tiƙar rawa ko kunya babu, nudai nace Allah ya kayauta ban taso naga anayi ba, maganar haɗe hanuwan nan ma ina gaf da in dakatar,
Mubin ne ya tuno da kyaututtukan da masana'antarsu ta samu, banda na alhji Nuru, ya zage yana wani rawa dani har wani rungumeni, naji babu daɗi sbda bawai na saba da irin wannan abin bane, bayan an gama hidimar aka tashi, mun sami gifts sosai, dan nawa ma sai wata ce ta riƙemin.
Daga nan muka wuce hotel ɗin da aka kama mana,
Washe gari muka koma M.M republic chicken mukaci abinci mai rai da lafiya, har Ibrahim nayin guzurin wani a leda, muka hau jirgi muka dawo Kano.
Da isarmu gida na wuce ɗakin da yake a mazaunin nawa na cillar da wayar akan gado na rushe da kuka ina cewa "duk laifinka ne Abba ko kuɗi suka cika maka ? Abba kasa na aikata haramun, sun ɗauki rayuwar boko sun sawa kansu ni ban taso naga anayin hakan ba, mahaifiyarsa na gani yake wani rungumeni amma ko a jikinta saima wani washe haƙora take mtsw,"
Tsabar gajiya da nayi iya sallah nake tashi yi, sai washe gari na koma bakin aiki, a hakan ma sai da na nace aka kaini asibitin Aminu Kano gurin Abbana,
Cikin rashin sa'a akace ai an sallameshi har yana tafiya ko ina,
Bansan lokacin da na fara hawayen farinciki ba.
Ina komawa gidan su momy na samu tayi baƙi, waɗannan matan da sukaje lagos sune sukazo,
Cikin ladabi na gaishesu, suna tambayata ya gajiyar taro?" cikin jin kunya nace alhmdulilh"
Momy tace "bayan fitarki Mubin yake sanarmin an sallami babanki"
Nace eh wai yana gida,
Jira nake inji tace driver ya kaini amma batace komai ba, na koma ɗaki.
Agogo na duba ƙarfe 1:14pm na waro ido da sauri na shige kitchen, na duba jadawalin tsarin girke-girke, yau taliya za'ayi da vegetables dafaduka,
Cikin azama na haɗa komai nayi girkina mai daɗi duk da yabon ƙai babu kyau .
A dinning na jere su bayan na kammala zubawa a foodfkaks na kawo plet da fork da drinks wanda na ciro a fridge na ajiye, dady bai sami dawowa jiya ba, yau muke saran dawowarsa,
Ina shirin komawa kitchen in zuwa abincina, momy ta fito sanye da wata dakakkiyar shadda tasha aiki ga ruwan stone mai ƙyalli daya ƙarawa ɗinkin kyau, tace "Ilham harkin gama komai ne ?" eh" nace ina gyaɗa kaina,
"Kinga na mance kifinmu ya ƙare maza jeki kasuwa ki siyo mana na 3k dan Allah kiyi sauri"
"Tom"
Nace na ƙarɓi kuɗin, kasancewar koda yaushe bana rabuwa da hijab a jikina yasa na wuce kawai.
Ina zuwa parking space na samu driver yana waya, ban tsaya jiransa ba nace "dan Allah kazo ka kaini kasuwa Alhji ya kusa isowa"
Driver ya shige mota nima na shiga muka lula titi.
Bamu shiga cikin kasuwar ba, a baki-baki na sayi kifin muka dawo gida,
Ina kawowa momy na tafi gabatar da sallahar azhar, momy kuma ta shiga kitchen yiwa dady farfesun kifi, dama koda wane lokaci inhar yayi tafiya ya dawo, baya taɓa cin abinci sai yaci farfesun kifi da dankalin turawa da ƙwai.
Ina idar da sallahar na taho kitchen dan taya momy aiki,
"Gashi kin gaji ko zaki bari zuwa gobe kije ki dubo mahaifinki"
"Tom"
Kawai nace mukaci gaba da aiki,
Muna gamawa shima muka kai dinning.
Ƙarfe 4:3pm na yamma su Mubin da dady suka iso gida,
Da sallama dady ya shigo yana murmishi,
Momy taje da sauri tana cewa "ai dai kace muje mu tarboka a airport shine ka dawo kai kaɗai"
Momy ta ƙarashe maganar kamar wata ƙaramar yarinya.
Mubin daya shigo yanzu yana dariya shima yace "momy ni kawai dady ya sanarwa ni na ɗaukoshi"
Mubin ya wuce dinning ya bubuɗe abincin kafin ya mayar ya rife cikin ɗaga murya yace "momy nifa bazanci taliya ba, tuwon semo nakeso" momy ta kwalamin kira tana mitar Mubin ya cika fitina, da sauri na durƙusa haɗi da gaishe da dady dake zaune yana magana a waya, bai amsa ba sai da ya gama sannan na miƙe dan aiwatar da aikin da wannan sokon ya sani, sunan dana sanyamasa yau kenan ko ince mugu.
Cikin ikon Allah na kammala na kawo na ajiye masa.
Zuwa yamma ina zaune a ɗaki ina ta danne-danne a wayar da Ibrahim ya kawomin, babu komai a cikinta sai number mutum uku, tasa data Mubin data momy, tsaki naja kafin na miƙe ina cewa "ƙila ma momyn tayi shiru ne tana jira in miƙo mata wayar,
Bayan anyi magrib da isha'i, dady da momy da Mubin suna zaune a parlo, dady ya fara tambayar anyi nasara kuwa?" momy batace komai ba, ta kalli Mubin yayi murmishi kafin yace "eh dady maƙudan kuɗaɗen da aka samu sunada yawa, momy ta ɗauko wayarta da akayi mata videos na taron ta kunna tare da ajiye wayar a jikin dady,
Dady na murmishi yace "wannan ce ƴar aikin ko kuma an samo mana suruka ne ?" cikin jin haushi Mubin yace "dady wannan yarinyar itace ƴar aikin gidanan"
Wani sabon murmishin dady ya ƙarayi wanda shi kaɗai yasan dalilin hakan.
Momy kam hankalinta na kan videon,
Sai da dady ya gama kallo tsaf harda kyaututtukan da muka samu,
Fara'a ce naga ta baiyyana a fuskarsa, cikin jin daɗi naji dady yace "kuɗin da aka kashe a gurin taron, ribar da aka samu jiya ta ninka wancan kuɗin, muna yiwa Allah godiya, Allah ya daɗa ɗaukaka mana masana'antarmu,
"Aisha kiramin ita yarinyar"
"Dady bafa kunya ne da yarinyar ba zata iya gwada maka halinta"
Ko kula Mubin dake magana dady beyi ba,
Momy ta miƙe ta kirani,
Ban wani ɗauki lokaci ba, na fito sanye d dogon hijabi har ƙasa, nazo gaban dadyn na durƙusa kafin nace "barka da dare"
"Yauwwa barka"
Yacemin sai naji ya kuma cewa,
"Gaskiya mun gode Allah ya saka miki da ma fificin alkairi, Allah ya baki miji na gari, Allah ya haskaka rayuwarki, gobe insha Allah zamuje mu dubo mahaifinki kinji"
"Amin" nace, kana na gyaɗa kaina na tashi nabar gurin.
Washe gari na tashi da murnar zuwa ganin Abbana, da wuri nayi aiyukan da nasan sun zamemin wajibi,
Ƙarfe 7:am na kammala haɗa breakfast na shiga wanka.
Ina fitowa na shafe jikina da mayukan da momy ta siyamin, ikon Allah jikina dai yayi laushi sosai, sai kace na jira jirai,
"Keeeee!!!"
Naji an dakamin tsawa,
Tsabar ƙaraji da hayaniyar muryar tasa na kasa gane waye ne,
Dan ubanki dama basaja kikazo yimana a gida?
Kinzo ki rama abinda akayi miki ne.!"
Cikin ƙarfafa gwaiwa da rashin nuna na tsorata nace "ban gane me kake nufi ba"
Ya ƙara magana cikin kakkausar murya yace "wallahi idan baki tattara kayanki kin bar gidannan ba saikin raina kanki, matsiyata kwaɗayi da rashin godiyar Allah yasa kika zaɓi aikatau, ko ince ubanki ya zaɓa miki, ai da nasan kece tuntuni da na ɗauki mataki, kafin in ƙirga uku kibar gidannan!!"
Cikin jin ciwon maganarsa nace "badan yiwa mahaifina biyayya ba, bakukai inzo in durƙusa yi muku aiki ba, badan ciwon daya damesa ba bazan wulaƙanta kaina ba, kuma ka rubuta ka ajiye daga yau har nan da wata shida ina zaune a gidannan har sai na gama aikin kuɗin da kuka biyawa Abbana na asibiti, kaga kuwa babu ranar tafiya"..!
*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_5_ *AUREN WATA TARA👩❤️👨*
_Miss Hajo_Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*
Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224...........🥚👩❤️👨💥🌎....
*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇Kina turawa zamu saki a grp
08141799224*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*