Chapter 2

359 18 8
                                    


Jin sautin harbin da ya sake tashi ne, ya sa yarinyar fitowa daga cikin Motar da sauri ta tsaya tana kallon Captain.

Jini ne ya shiga zuba a gadon bayansa, ga na cikinsa da yake zuba shi ma, cike da jarumta irin ta soja yake ƙoƙarin tsayuwa kan ƙafafunsa, ya kuma ƙoƙarin ya yunƙura ya ɗaga ƙafarsa, sai dai yaji jikinsa yai masa nauyi, ga wani danshi da yake ji ya jiƙa masa kaya, sai a lokacin ya fuskanci harbi ne, a nan take duhu ya maye gurbin hasken ranar da ya haska dajin a idon Captain, a hankali yai baya ji kake timm ya faɗi ƙasa.
  
  Sam ba ta san me ya faru da mutumin ba, wanda ya karɓo ta a hannun waɗan nan mutanen, sai dai ta zuba masa manya manyan idanunta, sai jujjuya ƙwayar idanunta take a kansa.
Sautin Wani harbin ne ya kuma tashi, cikin azama wani soja ya fito daga cikin Motar, ya danƙi yarinyar ya kwantar da ita flat a ƙasa, ya shiga danna nakiyar ta sa bindigar shima a saitin in da ƙarar harbin ke tasowa.
  Sautin Command ɗin Commander Land army ya jiyo nesa kaɗan da in da suke, yana bawa tawagar sojojin umarni, cikin dakakkiyar muryarsa dake amsa kuwwa a dajin, tare da ƙarar motocin sojojin na yaƙi, hakan ya tabbatar masa, da an turo wasu sojojin domin kawo musu ɗauki.

Nan da nan ƙarar harbi ya sake cika dajin, tamkar za'a tsaga dajin.

Tai lamoo a ƙasa, duk wannan ba ta kashin, da ƙarar bindigogin da ke tashi, can ƙasa ƙasa take jiyo sautin kaɗan kaɗan a cikin kunnenta.

Gaba ɗaya hankalinta yana kan mutumin nan da ya ɗakko ta, da yake kwance a ƙasa, ba ya ko motsi.

Ba tare da tunanin komai ba, ta miƙe zata nufi in da yake ƙasa a kwance, sojan nan da ya kwantar da ita flat a ƙasa, ya fizgota cikin tsawa yace "Lay down before they shoot you" shiru tai tana son gane me yake cewa.

Ya sake kwantar da ita a ƙasa, hellcopter nan kuwa tuni ya tashi ya fara shawagi a sama, suna communicating da sojojin dake ƙasa.

An kwashi kusan awanni biyu ana wannan musayar wuta a tsakanin 'yan ta'addan da kuma sojojin, wanda a ƙarshe Allah ya bawa sojojin nasarar fatattakar maharan, suka kashe na kashewa.

Sai bayan da ƙura ta lafa, sannan Lieutenant Faruk ya migirna a hankali, saboda harbin shima da akayi masa a dantsensa.

Cikin jarumta ya miƙe tsaye, sai dai jiri ne ke ɗibar sa, saboda jini da yake zubarwa a dantsen nasa, yana tashi ita ma yarinyar ta tashi tsaye, sannu a hankali ya ƙarasa in da Captain yake kwance a sume cikin jini, ya durƙusa ya ɗago shi, tare da kara kunnensa a saitin zuciyarsa, can ƙasa ƙasa yaji bugun zuciyarsa alamar yana da rai.
Bin su kawai take da ido, tana sake zura kai tana kallon Captain da idanunsa ke rufe.

Tawagar sojojin da suka shigo dajin kawo musu ɗauki ne suka fara ɓullowa, suna ta tattara gawarwakin 'yan uwansu, da wanda a kaiwa rauni.

Cikin hanzari suka ƙaraso in da su Captain suke. Lieutenant Faruk na zaune rungume da Captain a jikinsa, Chief Commander yace "Are you ok?"

Faruk yace "Yes sir, but Captain K Buba needs first aid, he is seriously bleeding"

"Is he alive?" Ya sake tambayarsa.

"Yes, but am not sure"

Nan da nan aka ɗauki Captain zuwa inda aka kwantar da wanda suke buƙatar taimakon gaggawa, wanɗanda akaiwa rauni.

Nan Army doctors, likitocin sojoji suka rufu akan Captain dan ceto rayuwarsa, aka fara ƙoƙarin cire bullet ɗin dake cikinsa.

Sun yi nasarar cire na bayansa, amma na cikinsa ba su samu cire shi ba, sukace sai an koma can Barack za'a iya cire shi a Asibiti. Nan su kai ƙoƙarin tsaida jinin da ke zuba a jikinsa.

Lieutenant Faruk ma an cire masa bullet ɗin da ke damtsensa, an saka bandage an nannaɗe masa hannun.

"Hey, what this little baby is doing here?" Chief Commander ya faɗa yana nuna yarinyar da Captain ya tsinta.

DARE DA DUHUWhere stories live. Discover now