Dafe kansa dake barazanar tarwatse masa ya yi, tare da taune lips ɗinsa na ƙasa cikin taurin zuciya.Likitan da ya je nemo yarinyar bai ganta ba ya dube shi, cikin girmamawa da son kwantar masa da hankali ya ce. "Ka kwantar da hankalinka Sir, Insha Allah, za'a ganta"
Runtse idonsa ya yi, gently ya ƙara buɗe su yana kallon su ya ce. "Where is my phone?"
Likitan ya ce. "Tana nan tare da uniform ɗinka, da za'a yi maka surgery ne aka cire su." Bai ce komai ba sai alama da ya yi masa da hannu akan ya kawo masa wayar. Likitan ya sara masa sannan ya fice. Gyara masa kwanciya ɗayan Likitan ya yi, shi ma ya fice.
Lumshe idonsa ya yi yana tuna Jamil da Danniel cikin jini a kallon ƙarshe da ya yi musu, sosai mutuwar su take dukan zuciyarsa. Numfashi ya fesar mai zafi lokacin da ya tuno fuskar ƙaramar yarinyar da ya gani, bai san me yasa ya ji ya damu da ita ba a cikin zuciyarsa, ji yake yi kamar ya fizge drip ɗin hannunsa ya fita ya nemo ta da kansa. A fili ya furta
"Where is She?What kind of situation is she in? who will take care of her?" Ya yi maganar cikin damuwa. he just felt worried about the little girl.
General Ibrahim A.M ne yake ta kaiwa da komowa a cikin office ɗinsa, shi kaɗai cikin tsananin ɓacin rai. Lokaci ɗaya ya koma mazauninsa ya zauna yana fesar da wani numfashi mai zafi, duk da kasancewar office ɗin da A.c amma gumi ne kawai yake tsatstsafo masa ta ko'ina a jikinsa. Hannunsa dafe da kansa sai karkaɗa ƙafafuwansa yake yi.
Da ƙarfi ya buga table ɗin gabansa tare da faɗin. "Damn it!"Wayarsa ce ta fara ruri tana neman agaji, tsaki ya ja har kiran ya katse bai bi ta kan sa ba, dan ba ta shi yake ba. Sai da aka yi masa 4 missed call sannan ya janyo wayar cikin ɗacin rai a fusace ya ɗaga ba tare da ya duba mai kiran ba.
Daga cikin wayar wata shaƙaƙƙiyar murya ya ce. "An samu bacin rana!"
Ajiyar zuciya General Ibrahim ya sauke yace
"Har da na Inuwa ma duk an samu Gwaska."Gwaska ya ce "Ba a taɓa mun
Ɓarna irin wannan ba tunda na fara harkan nan, ya akai haka ta faru?." Cikin ɓacin rai General ya ce. "Ba za ka gane baƙin cikin da nake ci da wannan Nasara da yaran nan suka samu ba, ban taɓa tunanin hakan za ta faru ba, a yanda na san ka na san taƙadirancinka ko rundunar sojoji million aka turo za ka iya gamawa da su, na baka komai a tsare, umarnin harbin da aka basu ne ya ɓata komai, kuma aka shirya wata rundunar aka tura ba tare da sanina ba, shiyasa su suka yi galaba a kanku. Babban baƙin cikina da wancan yaron Khamal ya dawo a raye ba, kuma na san duk nasarar da aka samu sanadiyyar sa ne, dan ba ƙaramin jajircewa ce da shi akan aikinsa ba, yana aiki ne da jikinsa gami da zuciyarsa, He knows the value of his work, especially if he wears military uniforms on his body, he feels like he is carrying the whole country in his shoulder, gaba ɗaya yanzu idan manyanmu a kansa yake".Gwaska ya yi wata shegiyar dariya ya ce. "Indai kere na yawo, zabo na yawo wata rana za'a haɗu, Wallahi sai na ɗauki fansar kisan yarana da akai mun da kuma harsashin da ya huda jikina, zan yi ɓarnar da sena girgiza ƙasar nan girgiza ta gaske makuwa, kuma dole a sakarmin yarana da aka kama ko kuma aga abunda ba'a so" Cikin mamaki General ya ce. "What? You mean kai ma sun yi nasarar harbin k......,"
kiran da ya shigo cikin wayarsa ne ya katse masa abun da yake cewa. Janye wayar ya yi daga kunnensa ya duba, ganin Chief of Army staff ne yasa cikin sauri ya cewa Gwaska "Ina zuwa, I will call you later." Bai jira amsarsa ba ya ɗaga kiran Chief ɗin.
Ƙamewa ya yi kamar yana gabansa with so much respect ya ce. "Morning Sir." Daga ɗaya ɓangaren Chief ya ce. "Morning General, ka shirya kai da sojoji kamar 20 anjima za mu zo mu je mu dubo yaranmu na Naija state, sanann mu jagoranci miƙa yaran nan ga iyayensu "