Episode 001

43 2 0
                                    

*KE NAKE GANI…!*
Book 1

By
_Hafsat A Garkuwa_✨🌹

*Sadaukarwa*
_Gaba ɗaya wannan littafin sadaukarwa ce a gareki Adda Ramlat Mai_Dambu ina matuƙar alfahari dake abar ƙauna na gode sosai da karamci Allah ya ƙara girma._😍

001

2:30am
*…* Dare mahutar bawa a wannan lokaci kowa na kwance a matsugunin da Allah ya hore masa, duk da akwai wasu da basu iya rintsawa sai sun gana da ubangiji, musamman mabuƙata domin su roƙeshi ya biya musu buƙatun su na alkhairi, domin a wannan lokaci ne yafi sauraren kuken bayinsa, hakan yasa da yawa daga cikin bayin sa suke shafe dare wajen bauta masa   duk wani bawa musamman mabuƙaci ya kan tashi a wannan daren domin samun dacewa ga abun da yasa gaba, haka shima *ADEEL* yana ɗaya daga cikin waɗan nan bayi masu kai koken su wajen ubangiji domin ya biya masa buƙatar sa, durƙushe yake kan sallaya, idanun sa a rufe hawaye ne suke zuba tamkar famfo, haɗi da ɗaga hannayensa sama alamar roƙo,cikin muryar kuka yake faɗin "Ya Allahu, ya rahamanu, ya rahimu, ya muminu, ya jabbaru ya zuljalali wal'ikram! Allah ka dubeni ka amshi addu'ata ya Allah, a da ni kirista ne! banyi imani da kai ba, ban taɓa yin bauta a gareka ba,hakazalika ban taɓayi maka sujjada ba, ban kuma taɓa haɗa hannaye na a domin na roƙi wani abu daga gareka ba, a yau gashi duk waɗan nan ɗim ina aiwatar wa tsawon shekara uku kenan inayi, a ko da yaushe  takan faɗa mini cewar kada na taɓa faɗa wa ubangiji na  ƙuncin rayuwar  da nake ciki, a kullum na kasance me godewa ni'imarka tare da nuna jin daɗi na a gareka, duk wannan abun ya wadatar, amma a tsawon shekaru ukun nan ita kaɗai tasan azabar da take sha,tana yawan faɗa mini cewa
"ADEEL! a duk lokacin da ka shiga cikin wani ƙunci ko wata musiba, ka tunkari ubangijin ka domin shi a kullum yana saureren kukan bayin sa, yana kuma biya musu buƙatun su, ko da kuwa ba a lokacin da suka bukata ba. "Gani  na durkusa a gabanka ina roƙanka da ka ceci rayuwar *AZRAA* tana chan kwance cikin mawuyacin hali, tana numfashi amma kuma bata a raye, *Azraa* wacce ta kasance tana rayuwa a yau gashi mutuwa za tayi nasara a kanta, Likita ya faɗa mana cewar mutuwa Azraa zatayi bayan kuma Azraa tana raye ne a domin ta bauta maka, to amma gashi rayuwar nata tana a hannunka, zuciyata haɗe take data Azraa, ni kuma gani a durƙushe a gabanka a saboda Azraa ya ubangiji ina roƙonka da ka ceci rayuwar Azraa…ya ƙarasa faɗa tare da fashewa da kuka me ban tausayi tamkar ƙaramin yaro, ya jima a haka sai ƙarfe 4:00am bacci ɓarawo ya ɗaukesa.

*AS-SAHL HOSPITAL GOMBE*

Wasu dattijai ne Mace da Namiji ke zaune a gaban Docter Asim Macen kuka take kamar ranta zai fita cikin kulawa Docter Asim yace 
"Hajiya Khalida a gaskiya haƙuri za kuyi, domin ceton rayuwar Azraa abun ne mawuyaci, a hankali a hankali  ƙwayoyin halittar ta sun samu gaggarumin matsala sama da shekara uku kenan bata san inda take ba kuma kunsan manyan likitocin da suka rinƙa dubata amma abun yaci tura.
Cikin kuka da zafin zuciya Hajiya Khalida tace
"Amma zuciyarta ai tana aiki, kuma har yanzu tana numfashi bata mutu ba har yanzu tana raye.
Ta faɗa da ƙarfi tare da nuna Docter Asim da yatsa ta fashe da wani sabon kuka, da sauri Alhaji Arshad ya riƙota tare da sanya ta a jikinsa yana ɗan bubbuga bayanta ya kalli Docter Asim yace
"Ka kalleta fa Dr. Asim ita ka ɗai tasan irin ciwon da take ji, ya faɗa tare da nuna Azraa wacce take kwance bata ko motsi na'urori ne kala-kala a jikinta tun daga hancinta har izuwa singalalin hannunta ya ƙara da cewa
"Gashi baza ta iya faɗa ba,bata motsin da za ta iya bayyanawa.
"Khalida ba iya Azraa ba mu kammu muna yaƙi a domin rayuwarta kukan da kike bashi da wani amfani tun da bazai tada mana da Azraa ba, abu ne mafi ciwo ace iyaye suna tsaye da ƙafafuwansu a gabar ƴar su ace baza su iya sama mata lafiya ba, a haka har ta mutu ba tare da mun iya aikata komai ba.
Ya faɗa wasu hawaye masu zafi suna fitowa daga idanunsa.
Cikin kuka Hajiya Khalida tace
"Abee Azraa baza ta mutu ta barmu ba!
"A'a Khalida kada ki yaudari kan ki Azraa baza ta rayuwa ba, ya faɗa tare da fashewa da wani irin kuka tamkar ƙaramin yaro.
"Wayyo Allah Ƴata kada ki tafi ki barmu baza mu iya rayuwa ba, Hajiya Khalida ta faɗa tare da sake rungume Mijinta gaba ɗaya an rasa me rarrashin wani.
Suna cikin haka Azraa taja wani irin dogon numfashi da ƙarfi ta sauƙe.
Da gudu suka nufeta ganin tana motsi, Dr. Asim ma tashi yayi cike da al'ajabi da mamaki domin babu yadda za ayi ace wanda ya kai wannan matakin zai rayu (Niko nace kum manta ikon Allah kenan?).
A hankali ta fara buɗe idanunta ta sauƙe su tar akan iyayenta mafi soyuwa a gareta, hannunta Hajiya Khalida ta kama tana sake mata murmushi me haɗe da kuka Dr. Asim ne yace
"Azraa!
A hankali ta juyo ta kallesa ta buɗe bakinta da ƙyar tace
"Na'am!
"Alhamdulillah!
Shine abun da suka faɗa gaba ɗayansu, da sauri Alhaji Arshad ya ciro wayarsa ya ƙira number Adeel.

KE NAKE GANI...!Where stories live. Discover now