Episode 002

20 0 0
                                    

*KE NAKE GANI...!*
'''Book 1'''

By
_Hafsat A Garkuwa_✨🌹

*Sadaukarwa*
_Adda Ramlat Mai_Dambu_🦋

'''Wannan page kyauta ne a gareki Asee Beauty kiji daɗin ki ta wajena'''😘🫰🏻

002

Cike da mamaki yake kallonta yace "Azraa me kike nufi ni kike tambayar waye ni? ya faɗa yana nuna kansa tare da kamo hannunta,  kamar an tsikare ta  da sauri ta wacce hannunta ta ture shi yayi baya ita kuma ta bar wajen a guje ta nufi ward ɗinta, Adeel miƙewa yayi daga durƙushen da yake cike da mamaki cikin sassarfa ya mara mata baya, tana shiga ward ɗin ta sanya key a ƙofar tana sauƙe tagwayen ajiyar zuciya da sauri Hajiya Khalida ta iso gareta cikin tashin hankali tace"Azraa ina kika je? Da sauri ta riƙe mahaifiyarta cikin kuka tace "Mami me muke anan me yasa me ni me kalula yake yi a hannuna don Allah ku faɗamin... Ta ƙarasa tare da fashewa da matsanancin kuka, Abee ne ya ƙara so gareta tare da sanyata a jikinsa yana bubbuga bayanta a hankali da alamun rarrashi yace "ki nutsu Azraa yanzu likita zai zo zai miki bayanin komai ba a ɗauki lokaci ba dr asim ya shigo tare da Adeel a hankali ya fara mata bayani ya ƙara da cewa "sakamakon haɗarin da kikayi yasa da yawa abun da ke ƙwaƙwalwarki kin mance amma a sannu in har ana tuna miki da abun za ki tuna su a hankali cike da mamaki tace "ni fa har yanzu ban fahimta ba ta faɗa tare da kallon Dr Asim murmushi yayi yace "shekara biyu da suka wuce kin yi haɗari wanda kika kusa rasa mahaifinki ke kuma kika shiga doguwar suma cikin hukuncin Allah muka samu nasarar ceto Mahaifinki  ke kuma muka kasa yin hakan sai yanzu da Allah yasa kina da nisan kwana yanzu kuma da kika dawo hayyacin ki sai kika mance da abubuwan da suka faru dake a shekara biyu baya a likitance dai muna ƙiran wannan abun da mantau na ƴan lokaci. Gaba ɗaya sun shiga damuwa musamman Adeel yafi kowa shiga damuwa dan yanzu ne ya gane manufar Azraa da ta nuna sam bata san shi ba kenan shima ta mance da shi kenan? Ya tambayi kansa wasu hawaye masu zafin suka zuba akan fuskarsa nayi addu'a tuƙuru ba dare ba rana akan Allah ya baki lafiya a yanzu kuwa zan duƙufa wajen ganin kin tuna da ni cikin zuciyarsa yake wannar maganar, cike da tausayinsa Abee ya kallesa da sauri Adeel ya juya ya fita yana goge hawaye Mami ne ta riƙe hannun Azraa da ke kuka itama kukan take haka Abee ma yace "Azraa mun cire tsammanin za ki rayuwa sai kuma gashi kin dawo... Muna matuƙar ƙaunarki Azraa babu abun da za mu cewa Allah sai godiya ya faɗa yana shafa kanta. Cikin kuka tace "Wai taya na kasa tuno da duk abun da ya faru.washe gari 6:00am a bakin ward ɗin Azraa Adeel tayi masa magana suke da Dr Asim da ya barshi ya ga Azraa amma Dr Asim yace "Adeel ko ka shiga Azraa baza ta tuna ka ba saboda ta mance da kai kayi haƙuri... "Ta ya za ace ta manta da ni... Ya faɗa cike da ɓacin rai daidai nan Abee ya fito ya riƙeshi cike da tausasawa yace"Adeel kayi haƙuri da gaske Azraa ta manta da kai sai dai ba wai hakan yana nufin ta mance da kai gaba ɗaya ba akwai ranar da za ta tunaka in sha Allah ranar tana zuwa gaba ɗaya jikinsa yayi matuƙa sanyi gaba ɗaya ya rasa nutsuwarka Mami ne tace "Adeel kada ka rasa ƙarfin gwiwar ka don Allah kasa Allah a zuciyarka za ka ga komai ya daidaita cikin ɗan lokaci. Kansa kawai ya iya ɗaga mata bai samu damar magana ba gaba ɗayansu suka nufi ɗakin da Azraa take a daidai wannan lokacin Azraa kwance take a hankali window dake ɗakin ya fara buɗe wa wani irin iska na bam mamaki ya fara ratsata wani irin baƙin inuwa kamar hayaƙi ya fara fitowa ta window cat ɗin dake ɗakin  a take ta fara kuka da ƙarfi hakan yasa Azraa da ke bacci farkawa a firgice a hankali ta sauƙo da ƙafarta ta nufi inda cat ɗin take wanda har yanzu ba ta daina kuka ba tana kallon window ɗagata tayi tana faɗin "P'A mai ya faru ina bacci kin ta dani? me yake damun ki haka? Cat ɗin har yanzu ba ta daina kukan ba a hankali Azraa ta fara jin wani irin sanyi ta harɗe hannayenta a ƙirjinta ji tayi sanyin na ƙaruwa ta sanya hijabi amma duk a banza wani inuwa take gani a jikin window a hankali ta fara juyawa ba takai ga ganin me yake window ba Abee suka shigo da sallama tsalle P.A tayi ta isa window tana cigaba da kuka Abee ne yace "Sahil maza fitar da P.A ka maida ta gida tun da ta ga uwar ɗakintan dan naji tun kan mu iso take ta kuka, da sauri Sahil ya ɗagata ya fice da ita Mami tace "Azraa ya jikin na ki? Mun yi waya da Nanne sun ce zuwa gobe za su iso da cewa tayi ma gaba ɗaya mu dawo tun da ba mu da kowa a garin nan amma da ƙyar Abeenki ya lallasheta kin san ta da rigima. Murmushi Azraa ta yi tana jin ƙaunar ahalinta na ƙara ninkuwa a zuciyarta Abee ne yace "Azraa ya jikin naki da sauƙi Abee "kin samu isasshen bacci ko? Eh Abee sosai ma yanzu ma P.a ce ta tashe ni murmushi Abee yayi yace "masha Allah lafiya ta samu Allah ya ƙara sauƙi suka amsa da amin.
Ya ƙara da cewa "Akwai abun da nake so na faɗa miki kin mance komai na baya na tsawon shekara biyu gaba ɗayan mu ba musan mai ya faruwa ba amma kuma Adeel ya sani musamman na cikin jami'arku don Allah ki daure ki sauraresa ko za ki iya tuna baya daga haka suka fice shi da Mami ya rage daga Azraa sai shi.
A hankali ya ƙaraso ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake ward ɗin cikin dakiya yace Sunana Adeel... Da sauri ta kallesa yayi murmushi tare da ɗaga mata gira yace "kiyi haƙuri na samu ƙarfin gwiwar gabatar miki da kaina da ni dake muna karatu a jami'a ɗaya hakan yasa mun kasance abokai a cikin jami'ar na kasance ina muradin yin waƙa ke kuma kina son rubutun waƙa duk wasu waƙoƙina ke kika rubuta su da kalamanki na ke kammala waƙata tun daga lokacin da kika shigo rayuwata na daina jin kaɗaici mun zama abokai abokai na ƙwarai sai dai wannan abotar tamu a ƙarshe dai ta rikiɗe zuwa soyayya gabaki ɗayan mu mun kasance cikin shauƙin juna duk da kafin ki amshi soyayyata sai da kika ba ni sharaɗi akan har in ina sonki da gaskiya to fa dole sai na bar addini na na dawo addinin gaskiya wanda kike ciki  ba ɓata  lokaci  na amince duk da iyayena sun so su dakatar da ni amma na nuna musu  zan iya rabuwa da su akan wannan addinin ganin da gaske nake kuma basa so su rasani domin ni kaɗai suka haifa yasa suka amince min ba tare da ɓata lokaci ba na karɓi  kalmar  na zama cikakken musulmi a ranar mu ta ƙarshe a wannan makarantar kin sanar da ni "rayuwar mu ta makaranta tazo karshe wannan shine lokacin da ya kamata iyayen mu su shiga maganar mu munje za mu haɗu da iyayen ki a hanyar mu ta zuwa kuma mukayi haɗari... A hankali ya juyo yana kallonta tun da ya fara magana ta zuba masa idanu tana son tunawa sai kuma ta ji kanta yayi wani irin sarawa a hankali yace "Azraa kin fara tuna wani abun? Ya tako har bakin gadonta ya zauna tare da kama hannunta yace "kin ware daga doguwar suma bayan shekaru biyu yayin da ni kuma a halin yanzu nake jiran ki tuno da soyayyata wanda bai kamata ace kin manta da ita ba.
"Wannan wani irin shashanci ne"  d fisge hannunta da tsawan da ta dakamasa da kuma miƙewarta ban san wanne ya riga wani ba ta ƙara da cewa"kana tunanin zan yarda da kai ne wato shine za kayi amfani da wanann damar za ka iya zuwa ka shashantar da iyayena amma ba ni ba cike da damuwa yazo zai riƙeta ta ja baya da sauri ta ja hannunsa ta nufi ƙofa da shi ta turashi waje tace "zuciyace mai kamuwa da soyayya ba wai tunani ba, sannan tunani ne ke mance soyayya ba wai zuciya ba ni ban yarda da kai ba ɓace min da gani daga haka ta rufe ƙofar tun da ta fara magana yaji zuciyarsa na wani irin tafarfasa tausayin kansa ya cikasa ji yake ina ma zai mutu ya huta da irin wannan abun da yake gani a yanzu har dare yana wajen yana tunanin kalaman da ta gaya masa ɗazu gaba ɗaya ya rasa ta yadda zai ɓullowa al'amarin idanunsa ya matuƙar sauyawa kana kallonsa za ka san yana cikin tsananin damuwa Mami da zuwan su kenan suka ganshi tsaye a wajen cike da tausayi suka nufeshe Abee ne yayi ƙarfin hali ƙiranshi yace "Adeel" da sauri ya juyo fuskarshi da murmushi kamar ba shi ba ya ƙara da cewa "Ina fata za ka ƙara hakuri akan wanda kayi Adeel ban san mai yasa ubangiji yake ta jarabtarka ta wannan hanya ba Azraa ta samu lafiya amma kuma ina ganin kamar ta mance da soyayyarka amma nasan duk daren daɗewa zai zama alheri a gareka da mu baki ɗaya Mami ne cikin ɗacin zuciya tace "Adeel wai har yaushe ne za ka iya zama a cikin wannan yanayin har yaushe ne za kayi ta jira kafin tunanin Azraa ya dawo?.. "Har izuwa ƙarshen rayuwata Mami ko dai ta tuno da rayuwarta ta baya ko kuma ta faɗa wata sabuwar soyayyar za mu dawo da komai daga farko babu amfanin ace dole sai ta tuna da abun da ta mance a baya za mu iya kafa sabuwar soyyaya mu gina sabon yanayi abun da kawai ta mance shine tsakanin mu ne da kuma soyyayarmu ba ta mance iyayenta ba murmushi yayi ya ƙara da cewa ya kuka yi shiru ku da za kuyi farin ciki da farkawar ƴarku ya faɗa dan son kawar musu da damuwa ya ƙara da cewa "tabbas ni dai nasan baza ta mance ni cikin sauƙi haka ba inaaa bazai yiwu ba ycn saboda soyayyar da muke yiwa juna ya zarce wacce kukayi a lokacin samartakan ku ya faɗa cikin zolaya da dariya dan su samu su saki zuciyarsu suma dariyar suka yi saboda yanayin da yayi maganar dole ya sa su dariya Mami tace "Allah ya maka albarka Adeel
"Amin Mami"
Abee ya dafashi yace "ina fatan Azraa ta tuna da soyayyar ku a ƙanƙanin lokaci amma kafin nan ka je gida ka kwanta ka huta, da sauri ya girgiza kai yace "A'a Abee ban yarda ba kwana uku kenan ba kuyi bacci ba gaba ɗayanku zai iya haifar muku da matsala kawai yanzu ku tafi gida ku huta ni kuma zan zauna da sauri Abee yace "Adeel ka saurare ni... "Don Allah Abee kar kace komai kuje gida ku huta babu yadda suka iya hakan yasa suka tafi suna sanya masa albarka shi kuma ya musu sai da safe sannan ya dawo wajen da yake ya zauna duk wannan abun da ke faru akan idon Azraa da ke zaune tana hangensu ta window ya faru ita kaɗai take faɗin "mai hakan yake nufi shin in karɓe sa a hakan ko kuwa kuma dai ni na kasa tuna komai na rayuwar mu glass ɗin window take hango wani irin farin abu sai ƙara girma yake a hankali ta taka cike da tsora ta isa bakin window hannunta na rawa ta taɓa taji wani irin sanyi sai kuma ya gauraye gaba ɗaya window wani irin suffa ya bayyana ta cikin glass ɗin window wani irin ƙara ta saki ta koma baya...

***********

A hankali take motsi tana juye juye ita ɗaya kan gado yayin da ta so ma buɗe ido a hankali (nurse) ta ke gani dishi-dishi ƙoƙari take taga ta miƙe, nurse ce tayi saurin isowa gareta tace "yi a hankali Amrish! Ɓata fuska tayi tace "Anti a kullum sai na tambayeki wa ya kawo ni nan ina son ganin sa don Allah ki kai ni in ganshi wai ko dai ni ba ni da kowa ne?" Tana kaiwa nan ta fashe da kuka. "Saurare ni Amrish dai na kukan wanda ya kawo ki na gaya miki a kullum sai yazo bacci kike shiyasa ba ku taɓa haɗuwa ba kar ki damu kina buƙatar hutu har yanzu".
"Ba ni da wani hutu Anti in ban ganshi ba hankali na bazai kwanta ba" ta sauƙa daga gadon ƙofa ta nufa kai tsaye nurse ɗin ta bi bayanta tana ƙiranta tana faɗin "Amrish me yasa kin fiye rigima ne da taurin kai ina kika san zaki samo shi ina kika sani? "Zan nemo shi ko a ina ne ba dai a duniyar nan yake ba to zan nemo shi". Wani likita ne ya tare ta gami da riƙe hannunta "ina za kije? Maza ki koma an faɗa miki marassa lafiya na fita haka kawai ne? in wani abu ya faru da ke fa koma ward ɗin ki muje na duba ki. "Bazan koma ba" ta bashi kai tsaye. Shi ko likita ganinta yarinya ba wata babba ba yasa ya damƙe hannunta da niyar zai mai da ta tuni suka hau kici kici da likita nurse tayi ƙoƙarin rabasu tuni Amrish ta rikice musu "ƙyaleta!" Suka ji muryar Al'imash dake tsaye nesa da su kaɗan. Tuni likita ya saketa Al'imash ya ƙaraso a hankali in da suke ya kalleta fuska ɗaure tamkar ba a taɓa halittar dariya a fuskar sa ba Amrish ji tayi ta kasa jurewa kallonsa ko ba a faɗa mata ba ta san wannan shine wanda nurse take bata labarin shi ya kawota asibitin tsawon shekaru biyar tsoron sa da shakkarsa suka ɗarsu a zuciyarta gaba ɗaya ta ruɗe. Jikinta na rawa ta koma ɗakin ta hau kan gadon a tsorace ta dunƙule wuri guda tana zazzare idanu tana sauƙe ajiyar zuciya lokaci guda kuma ta fashe da kuka. A hankali ya shigo ward ɗin yana kallonta gefen gadon ya zauna tare da janyota jikinsa kamar ko jira take ta faɗo jikinsa tana ƙara fashewa da wani sabon kukan ganin ba ta da niyar yin shiru ne cikin cool voice ɗin sa yace "to kukan ya isa haka mana Amrish ba ni dama kike son gani ba kuma ba gashi na zo ba pls yi shiru ki faɗamin mai yanzu kike so kin ji oya!"
Tashi tayi daga jikinsa tana goge hawayenta ta haɗe fuska cike da zallan shagwaɓa tace "me yasa tsawon shekara da shekaru baka taɓa tsayawa na ganka ba sai dai duk lokacin da na farka na tambaya sai nurse ɗin can ta ce min wai ai kazo ka tafi wataran ma ku da yawa kuke zuwa haka take gayamin ni kuma ina so naga wasu nawa kullum cikin ɗokin ganinka nake yanzu ma da badan na musu rigima da haka za kazo har ka tafi ban ganka ba ta faɗa da iya gaskiyar ta.
Tun da ta fara magana ya tsare ta da ido salon yadda take maganar ne ya burgesa sosai musamman shagwaɓar ta da take yi bai san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba jin maganar da take faɗa bakinta ya kama ya ɗan matsa a hankali yace
"Baby Amrish rabona da ganin shagwaɓarki da kuma rigimar ki tun kina 6years sai kuma yanzu abun da yasa kuma ba ma haɗuwa shine a kullum ana miki allurar bacci ne saboda ki ƙara samun nutuswa da firgicin da kike shi yasa ba ma haɗuwa amma kuma gashi yau mun haɗu da baby rigimata. Ya faɗa yana ɗan jan hancin ta shagwaɓe fuska tayi tace "Noor to ina ƴan gidan mu ko kuma kawai mu biyu ne?" Murmushi ne ya suɓuce mar da yaji ta ƙirasa da Noor saboda ita ta raɗa masa da kanta kallonta yayi yace "Baby ba mu kaɗai ba ne akwai Didi akwai kuma su Aunty da Abba da kuma su Farrah da Afnan ko jiya sun zo kina bacci amma kar ki damu ƙila mu samu sallama a satin nan. Ya faɗa yana riƙe kanshi tare da faɗin "Ya Allah!" alamar ya ga ji da sauri ta riƙe hannunsa tace "Noor me ya faru?" Kamar bazai yi magana ba yace "ba kece kika saka ni nayi doguwar magana ba har kaina ya fara ciwo, da gaske yake domin a duniya babu abun da yake masa wahala kamar ya buɗe baki yayi magana rabon da yayi magana irin haka har ya mance watannin...

KE NAKE GANI is 100 via… Union bank 0134205910 Hafsat Ayuba ku nuna shaidar biyan ku ta lambar whatsApp ɗina… 08132761212, in kati ne kuma zaki turo MTN na 100 akwai Vip grp posting biyu a rana 300 za ku iya fara biya tun yanzu kafin na gama free page ku karanta cikin farin ciki ba tare da jin wani laifi ba.

Commen&share
*ONE LOVE*🤞🏻💞 
08132761212

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 03, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KE NAKE GANI...!Where stories live. Discover now