Chapter 1

12 1 1
                                    

🌪️ ASHRAF___JAHAAN🌪️

Story & Written
        By

🌪️ Ashoush.

EPISODE 1

KAUYEN BANKURE.

__________Duk da yanayin da ake ciki na muku_mukun sanyi, haka bai hana ta watsa mata ruwan sanyi a jikinta ba, cikin fada take magana, "Ke dan uwarki ki tashi yanzu_yanzu ki wanke min dan kanfaina, kinsan da cewa Halliru yana jira na, wacce irin dakikiyace ke".

Yarinya ce kwance kan wata ya mutsastsiyar tabarma, duka_duka yarinyar b azata wuce   shekara 10 goma ba, cikin nutsuwarta da kuma sanyin jiki, ta mike, tana rawar dari "Kiyi hakuri yanzu na kwanta, kuma yunwa nakeji, ban...." bata karasa zancen ba aka zuba mata wani gigitaccen mari, " ni zaki fada wa kina jin yunwa??? to ina ruwana, ki mutu mana ni ko damuwa bani da ita" ta karasa maganar cikin hargowa da hayaniya.

"Zaki wuce ko sai na hallaka ki???" sum sum sum yarinyar ta juya wacce tun da Hanne ta mareta bata dawo cikin nutsuwarta ba.

Wajen rijiyar da take gidan ta nufa zata debi ruwa, "ke ke kee matsiyaciya kada ki kuskura ki taba wannan gugar, Idan ba haka ba sai na lahira ya fiki jin dadi, shasha sha mara hankali, ki wuce rafi kije ki debo a can".

"To Baaba, ita yarinyar ta fada, tana share hawayen da yake zubowa a kuncin ta, daukan babban tulu tayi, kana tayi waje, ga sanyi sosai ko wanne yaro yana daki a killace amma ita kuwa tafiya take tana tangadi a hanya, saboda hajijiya da takeji, a haka har ta k'arasa har bakin Kogin da yake garin.

tsugunnawa tayi ta nufin d'iban ruwan, santsi yaja kafarta, "Innalillahi wa'innailahi raji'un" ta fada da karfi tana daga hannayenta sama, tanjamm ta afka cikin kogin da ya ke gabanta, bulum_bulum ta fara yi aciki tana daddaga hannayenta, domin neman taimako, wasu samari daga can nesa da suka hango abunda yake faruwa, da gudu suka tawo wajen kogin su kawo mata dauki.

Afkawa cikin kogin daya daga ciki yayi, cikin zafin nama ya janyota, tare da fito da ita.

Tari take cikin shakewar numfashi, kuma tana waige_waige, a lamun neman wani abu mai muhimmanci a wurinta, a can nesa ta hango shi a fashe, kuka ta saki "wayyo na shiga uku na mutu na lalace tulun Baaba ya fashe 'yau ya zanyi' ta k'ara rushewa da kuka.

Ganin kukan yayi yawa, ya sanya wanda ya cirota a ruwa tambayanta "menene yake faruwa?"  shiru tayi masa don bata jin zata iya fada masa halin da take ciki, sai cewa tayi "tuluna ya fashe na shiga uku".

Hakuri ya bata tare da cewa "muje na bawa Baaba hakuri, nayi mata bayan cikin kogi kika fada" kai ta daga kana ta tashi, tana kakkabe jikinta.

Hanyar gidan suka nufa, tana tafiya a hankali cikin nutsuwarta, har suka k'araso wajen kofar gidan, jimmm tayi ta tsaya, kallonta yayi yana cewa "meyasa naga kin tsaya??? ko nan ne gidan??" kai ta daga masa tana goge kwallar da ta sulalo mata.

Sallama Adamu yayi jin shiru ba'a amsa ba ya kara bude baki ya kwantsama sallama.

"Kai dalla wane yake damun mu, ai munji ko, koma waye saika jira azo ai ko" Hanne ta fada tana fitowa daga cikin gidan.

Rike baki Adamu yayi, "haba Hajiya daga sallama kuma sai abun ya zama laifi?? me yayi zafi shi ba wuta ba!".

"Eh dallah malam naji me ya kawo ka?? sauri nake" kallon sama da kasa yayi mata, ya jijjiga kai, "to dama wannan yarinyar na rako, ya fada yana nuna Indo wacce take kara labewa a bayansa.

"Ohhh iyyeh fito dan ubanki, iskanci kika je??? ina dan kanfaina da zaki wanke???". Hanne ta fada tana janyota, tare da kai mata duka.

"A'a Malama meyasa kike dukanta kuma???na fada miki cewa kogi ta fada ai ko??".

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 23, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ASHRAAF_JAHAN🌼Where stories live. Discover now