🍒LAILA KABEER🍒
Da sunan Allah me rahama me jinkai
Sadaukarwa
Na sadaukar da littafin LAILA KABEER neh ga malamina kuma Dan uwana Mr Ibrahim da kuma wayanda suka bani karfin gwiwa kuma suka jajirce wajan ganin na cimma burina wajan wallafa wannan littafin. Allah ya saka muku da dumbun alkhairansaGargadi
Wannan littafin mallakina neh kuma labari neh kirkirarre wanda na zauna na rubutashi da kaina. Ban yadda wani ko wata yayi amfani dashi ba ta kowanne hanya ba tare da izini na ba.Tunda ya zauna yake kallon hotonta, ji yake kaman ana soka mishi kibiya a tsakiyan kirjinshi. Zuciyanshi yana mishi wani irin kuna me radadi. Be taba jin hakan game da ita ba, sannan ya kasa gaskata abunda kunnuwansa sukeji. Kokarin tashi yakeyi amma ji yake gaba daya dakin yana juya masa.
Babu shawarar data rage a gareshi illa abunda zuciyarsa ta dade tana saka masa. Da wannan tunanin bacci barawo ya sace shi.Da kamar baze dauka ba amma ganin sunanda ke yawo akan screen din wayar shi yasa yayi saurin amsa kiran tareda kara wayan a kunnansa. "wato ka maidani dan iska ko? Ashe kayi girman da kafi karfin nasa doka kabi ko. To wallahi Nasir ina shaida maka idan har mahaifiyarka ce take saka kakeyin abubuwanda kakemun, katuna cewa zakayi aure kuma zaka haihu. Sannan idan kana ganin abunda kakeyi daidai neh kaci gaba. Zaka gani a kwaryan cin tuwonka. Abba wallahi... kitt yaji an katse wayar kafin ya iya cewa komai.
Lokaci guda yaji gabaki daya kansa ya daure, fushin mahaifinshi ba karamin tayar mishi da hankali yakeyi ba. Sannan ba komai bane yake mishi ciwo irin ace mahaifinsa daya kamata ace yafi kowa kusanci dashi a matsayinshi na da namiji shine akullum yake cusa masa bakin ciki.....
Karar knocking din kofar da Ladidi tayi shi yayi sanadiyyan katsewar baccinta. "aunty Laila na dora sapagetin" abunda Ladidi tafada kenan. Ba tareda ta shirya ba, ta fashe da wani irin dariya me kayatarwa wanda hakan yasa dimples dinta suka fito wanda yafito da tsantsan kyanta.Ita ta rasa gane Ladidi wacce Irin mutum ce, ace shekara da shekaru tana zaune a birni amma har yanzu bata waye ba. "to nagode" abunda ta iya furtawa kenan wanda har a lokacin bata dena dariya ba. Murmushinda ke dauke akan fuskarta kadai ya isa ya tabbatar maka da irin farin cikin data farka dashi wanda ita kanta batasan dadilinsa ba.
Saukowa tayi daga kan gado tafara rage kayanda ke jikinta, sannan tafada toilet tareda kunna shower. Babu abunda ke sanya mata nutsuwa kamar taji ruwa yana zuba a gashin kanta. Seda tagama wankanta tsab kafin tafito ta zauna a bakin dan madaidaicin gadonta tafara tsantsame ruwan dake diga daga dogon gashinta wanda ya kwanta har gadon bayanta.
(I dedicate this chapter to my lovely fans 😍 you guys are always my first priority.
Your votes and comments are highly appreciated 🙏)
YOU ARE READING
Laila Kabeer
RandomThis story is based on love, hatred, envy, arrogance and lots more. ❤️😭😘🎉😍🤗🤧 Get your hankerfchiefs ready because you're gonna wipe an ocean of tears 😉