Laila ba ma'abociyar heavy makeup bace shi yasa kwalli kawai ta sanya a idonta sannan ta mike wajan bakkon kayanta domin dauko kayanda data sanya wanda baze takura mata ba. Aikuwa cikin sa'a taci karo da wata yar doguwar riga me dankaren laushi wanda aunty Saudat ta kawo mata shi a matsayin tsaraba lokacin data dawo daga Dubai. Dauka tayi ta zura ajikinta sannan tafito waje Bata saba dacin abinci da sassafe ba amma yau ta farka da wani irin azababben yunwa kamar ana yakin badar a cikinta
kasancewar yau weekend neh kuma ba makaranta sannan bazata je catering classes dinta ba abun ba karamin dadi yamata ba dan yaune zata cika alkawarin data daukar ma saratu nazuwa mata hira. Da murnarta ta dauki waya takira Saratu, Seda yakusa yankewa tukunna tayi picking"Hello yar ustaz" shine abunda Saratu tafurta
se yanzu kikaga daman daukar mun waya ko
"ke banza yi hakuri maida wukar yanzunnan na fito daga bathroom wanka nakeyi. hala yau kinyi mafarkina neh"
Ooh wato kiran danayi ma nayi laifi kenan
"Ni ba haka nake nufi ba yanzu ya ake ciki "
Kina gida neh yau?
"Eh ina nan"
To maybe zanzo anjima idan wannan matar bata hadamun munafurcinta ba
"saura kimun wannan zuwan minti talatin din naki wlh ko kofar gida bazan rakaki ba"
Se Nafasa zuwa ai
"sorry my love wallahi daman dazu su aunty nusaiba suka tafi, kinsan tunda tazo arba'in bata koma ba gashi har babynta yayi wayo. To yau mijinta yazo se suka koma tare gabaki daya zaman gidan ya isheni sannan kadaici yamun yawa gashi umma....
To naji karki cikani da surutu se kin ganni kawai. Mijinda ze aureki baya bukatan radio a gidanshi dan ke kadai ma kin wadatar.
Yar murmushi tayi sannan katse wayar dan tasan halin saratu sarai idan zasu kwana suna waya ba gajiya zatayi ba
Kamar kullum tafito daga daki taje ta gaida Inna sama sama tawani amsa gaisuwar amma inda sabo tasaba da wannan halin nata. Baba kam dama ba ma'abocin zama bane yayi tafiya dan haka ko zuwa dakinshi batayi ba
Ganin abun bana kare bane yasa taje kitchen domin duba wacce wainar Ladidi take toyawa. Ga mamakinta kuwa babu wata tukunyar da aka daura akan wuta gashi gaushin har yakusa cinyewa. Yadda takeji idan takara minti biyar ba tareda tasa wani abu a cikinta ba zata iya sumewa yasa kawai ta dauki kettle domin ta jona ruwa koda tea neh tasha. Dasauri taja baya dan ganin abunda ke cikin kettle din... "Ladidi" ta kira sunanta da karfi sannan taja baya, a guje ta taho saura kiris Ladidi ta bankadeta tanata wiki wiki da idanu...
YOU ARE READING
Laila Kabeer
RandomThis story is based on love, hatred, envy, arrogance and lots more. ❤️😭😘🎉😍🤗🤧 Get your hankerfchiefs ready because you're gonna wipe an ocean of tears 😉