Shafi na daya

2.4K 63 5
                                    

*GURBIN IDO*
         _Ba ido bane_

*Mallakar*
*Safiyya Abdullahi huguma*
*Arewabooks username*
*HUGUMA*

©️®️ *ZAFAFABIYAR*

*ƊANƊANO*
*Page 01*

         Faffada kuma yalwataccen daji ne iya ganinka,wanda ya wadatu da korayen tsirrai da kuma shukoki nau'i daban daban,masu tsaho da kuma gajeru,ciyawa tafasa da sauran tsirrai da ubangiji ya huwace musu su wanzu a wajen,wanda wasu ma dan adam bai san meye ba,wasunsu kuma magani ne da garkuwa ga jikkunan dan adam.

          Yadda sararin yayi kore shar da nau'in tsirran da kuma yawaitarsu kadai xai bayyana maka cewa muna lokacine na yawaitar saukar ruwan sama wato lokaci na damina,duk da da cewa gurin waje ne mai cike da ni'ima da kuma albarka,albarka data sanya mawuyacine ka samu wajen a bushe ko kuma a qafe.....wannan dalili ya kawo wanzuwar fulani wajen a muhallin,suka kafa bukkokinsu suka kuma tashi gagarumar ruga a wajen....saboda waje ne daya dace da muradinsu da kuma buqatar dabbobinsu,wanda buqatar dabbobin nasu sama take da tasu buqatar.

         Yammaci ne lis,wanda daqiqu kadanne ne zasu ratsa magariba ta shiga,lokacine da kowanne makiyayi yake qoqarin kada kan dabbobinsu zuwa gida inda zai turkesu saboda gabatowar dare,daga cikin wannan dajin mabanbantan tawagar shanu wani lokaci harda raguna da akuyoyi ke kutsowa cikin ainihin wajen da suke kira da gari a wajensu,kowanne tawaga na tafe ne da masu kula da ita,mutum biyu uku hudu har zuwa biyar idan sunyi yawa,yawancinsu maza ne,matan dake ciki daidaiku ne.

          Da sannu sannu wadan nan dabbobi ke wucewa zuwa guraben da muhallinsu yake,kamar sun gama wucewa.....saiga wani garken na daban na bullowa a hankali.

         Kyawawan shanu ne tunkiyoyi raguna da kuma awaki masu tarin yawa da daukar hankali,ba komaine ya kawo haka ba sai yanayin qoshi da kuma tsaft da garken keda yashi,kusan duk dabbar dake ciki fara ce.....sai wasu daga ciki dake da ratsin ruwan qasa......duka ba wannan ne abun mamakin ba,abu mafi daukar hankali shine Kyakkyawar matashiyar dake kara kaina daga hagu tsakiya xuwa daman dabbobin tana saita su,da fari zaka zaci ba ita daya ke wannan aikin ba,amma idan ka tsawaita dubanka a kanta zaka fahimci ita kadai dince,dauke da sanda guda daya tak.

        Kyakkyawa kyau na musamman kuma na asali koda cikin fulanin,irin kyan da zaka tsammaci half case ce,maimunatu nada wani irin kyau na daban wanda ke sanya duk wanda yake baqon gani a gareta ke bata lokacinsa wajen binta da kallo,saidai kuma.....duk da wannan kyau nata babu mutum daya daya aboceta wajen tahowa gida,kusan kowa ya kado dabbobinsa ya barta,babu koda mutum daya ma cikin wadanda sukayi gaba dake waiwayota ko duba halin da take ciki bare yayi niyyar tayata ta samu ta iso gida da wuri.

            Kusan itama hakan bai dameta ba,duk da tanashan wahala,amma ya zamar mata jiki,ta kuma saba da yanayin......sanye take da baqin saqi maimakon farin saqi da akasan mafi akasarin fulani na tu'ammali dashi,zaka iya hangen yadda kayan suka dangale mata sosai fiye da dangalewa ta al'ada da aka saba gani tattare da fulanin,don kuwa koda rigar maimunatu tayi dagewar da banda baqar rigar yadi data saka daga ciki,babu abinda zai hana mutum ya hango albarkatun qirjinta da suka fara tasawa,sai kuma yalolon baqin mayafin data sake rufe qirjin nata dashi,duk kuwa da cewa ba wani kauri ne dashi ba,bashi da maraba da abun tace koko,hakanan bashi da tsaho,don ko mazaunanta baikai ba,tun abun yana da girma da kuma kaurinsa take amfani dashi,amma har kwanan gobe ta kasa rabuwa dashi,saboda dumbin tarihin da mayanin yake dashi a gareta da kuma rayuwarta gaba daya.

           Zanin jikinta shima a dage yake sasai,kanta na sanye da Hular kaba irin wadda fulani ke yawaita amfani da ita da suke kira da(malafare)sakamakon yawaitar zafin rana ko kuma tunanin saukar ruwan sama,wadda ta baiwa doguwar jelar gashin tsohon kitson dake kanta bayyana sosai,kitson DOKA inji hausawa,su kuma suce dashi(BIƊEJI)(mai tudu daga tsakiya)shine a kanta,don haka jelar ga sauko dama da hagu na fuskarta da kuma bayanta,abinda ya qarawa kyakkyawar fuskarta kyau da kuma bayyana asalin yarenta.

GURBIN IDOWhere stories live. Discover now