_ -~ASMA'UL HUSNAH _
NA
__HAFSATOUAMJAD __ASMA'UL HUSNAH na kudi ne it's just 400 call or chart 08100312134 for more enquiry
~FREE PAGE~
02
—————— ✍️Da sauri Momy tasha gaban shi ranta abace tace "Ahmad me kake nufi da ka fasa auren Asma "? Kallon ta yayi tare da shafa kwantaciyar sumar shi yace "Yes Momy I mean it na fasa auren ta " gyara tsayuwar ta tayi cike da takaici tace "So kake ka maida mu kananun mutane ,toh wallahi na cire hannu na daga zuwa nemar maka aure wannan ne karo na karshe dazan taka kafa da kafa inje gidan su wata da sunan nemar maka aure ,ka raina mana hankali Ahmad baka san ciwon kanka ba yanzu ya iyayen yaran da kakeyi wa haka zasuji ,ko kuwa nema kake ka hana kanwar ka aure ka bata mana suna Agari wallahi baka isa ba " Momy ta karasa tana share hawayen da suka zubo mata "Abun naka yayi yawa karo na hudu kenan se an kai lefe an saka rana kace ka fasa aure ,mun bincika lafiyar ka an tabbatar da babu wata cuta ko shafar Aljanu tsagwaran rashin mutunci ne da nuna isa kana amfani da sunan mahaifin ka kana abunda kaga dama agari babu wanda ya isa ya maka magana Toh ka sani duk abunda Ka aikata se anyi maka tsoro na daya kar alhakin ka ya fada akan kanwar ka "
"Wai to Momy kinsan me ya hadamu da yarinyar ne da kika hakikance kike ta fada harda kuka ,? To yarinyar nan bin maza take taqadiriyar yar iska ce Allah ne ya Toni asirinta akan me zan auri yarinyar da zata ba tamin future na impossible "
Nasreen dake sakkowa daga stairs cak ta tsaya jin abunda Ya Ahmad yake jifan Asma dashiDa sauri ta karasa saukkowa tun kafin ta karaso tace "Wallahi Momy Queen of beauty bazata aikata haka ba ,yarinyar da magana bata dameta ba komai na rayuwar duniya baya gaban ta Momy aide kinga Asma ko kuma kema da kanki In Kinyi judging wallahi baza ki sakata a layin masu aikata alfasha ba mutuniyar arziki ce "
Cike da bacin rai Ahmad ya wanke Nasreen da zazzafan Marin daya saka ta tsugunnawa batayi niyyah ba "Wallahi idan Ina magana kina sakamin baki wataran sena hallaka ki ,na fasa auren nata Dan ubanki kiyi abunda zakiyi "
Momy ce ta dakatar dashi cikin tsananin bacin rai tace "Kar ka kuskura hannun ka ya kuma tabamin 'Ya kaje duk abunda kaga zakayi kayi dakai da mahaifin naka daya daure maka gindi kake taasar da kake so ,kuma gaskiya ta fada Asma bazata aikata koda kwatankwacin hakan ba saboda mutuniyar arziki ce,kaje Allah yana ganin ka " tana gama fada ta ja hannun Nasreen dake kuka sukayi sama tana takaicin halin Ahmad duk mahaifin shi ne yaja ,shi yasaka shi a Wannan yanayin saboda tsantsar soyayar da yake mishi ko fada baya son amishi yanzu wa gari ya waya ?Sosai Nasreen take kuka tana jin kunyar Asma ,saboda itace sanadiyar haduwar ta da yaya Ahmada juyowa tayi ta kalli Momy tace "Momy yanzu kawayen mu da sukayi anko me zan ce musu Dan Allah ,Ya Ahmad ya kunya tamu wallahi senaji daman be kasance yaya na ba Ina tantama akan yaya Ahmad akwai abunda yake aikatawa "
Dakatar da ita Momy tayi tace "Duk abunda yakeyi Allah yana sane dashi kuma kidena fadan haka duk lalacewar Dan uwa dan uwa ne Addua kawai zaki ringa mishi "
Batare da tayi magana ba taci gaba da kukan ta tana danasanin kiran Asma da tayi zuwa su gaisa da shi tun suna school
Lokacin da aka cire mata drip din bacci take dan haka yana ganin haka ya fito,Direct Office din likitan ya wuce zama yayi bayan ta bashi umarnin zama
Kallon ta yayi sannan yace "Sallama nakeson ki bamu ,zata karasa jinyar agida "Itama kallon shi tayi tana son tace ya bari ta kara samu sauki amman ganin ba hurumin ta bane yasa tace "Akwai gashin da zaa mata yanzu sede in an gama "
Gyada kai kawai yayi ya mike ya fice batare daya ce uffan ba ,bin bayan shi tayi da kallo tare da girgiza kai taci gaba d aikin ta.
Bayan fitar sa massalaci ya wuce dan lokacin har an fara kiran sallar magrib,
bayan fitar shi nurse ta shiga dakin lokacin Asma ta tashi yanzu garau take jin ta se abunda baa rasa ba ,sannu da jiki nurse din ta mata ,amsawa tayi tanajin nauyi aran ta
Bathroom ta wuce ta hada ruwan ta saka duka abunda likitan ta sakata sanann tacewa Asma ta shiga babu musu ta mike tana tafiya dkyar seda ta tabbatar ta gasa ta yanda ya kama ta sannan ta fito , itama Asma fitowa tayi tana jin dadi sosai ajikin ta .
Ganin shi tayi azaune akujera ya kafeta da ido saurin sunkuyar da kanta tayi ta dauki veil dinta ta saka sannan ta zauna ,
"We can go " ta tsinkayi muryan shi yana magana dagowa tayi da mamaki a fuskan ta ,Gyada mata kai yayi yace "An sallame ki " , se a lokacin taji gaban ta ya fadi da sauri ta kalle shi muryar ta na rawa tace "Ya Noor Ina jaka na,nasan Mamy tana ta kiran wayana nashiga uku me zan cema Mamy "?
"Keep calm please princess everything will be alright,zomu tafi dare na kara yi "Babu musu ta biyo shi tana tafiya a wahale saboda dinkin da aka mata ,Tana tsiyayar da kwalla gaban ta na tsananta bugu,tunanin karyar da zata yiwa Mamy kawai take amman ko Ina ta kama seya warware kasan cewar ta bata saba karya ba muddin tayi kuskuren yin karya tabbas se Mamy ta gano ta shysa ta saba da fadar gaskiya aduk halin data ta tsinci kanta.
Seda ya tsaya a pharmacy ya siyo mata duka magungunan da aka rubuta mata sannan ,suka shiga Office din likitan tare ,umarnin ya jirata a waje ta bashi tabe baki yayi ya fito waje
Wurin zama likitan ta nunawa Asma babu musu ta zauna dkyar seda ta tattaro nutsuwar ta tace "Toh Malama Asma'u matakin da kika taka shine matakin da ko wacce mace take takawa arayuwar ta ta aure kuma kowa ahaka yake hakuri ,saboda shine tabbacin kin girma ki kara hakuri da mijin ki kuma ki kula da kanki ,an miki dinki saboda budewar da kikayi da yawa amman insha Allah inde kina Shan magungunan dana rubuta miki yanda ya kamata zasuyi matukar taimaka miki ,ki ringa shiga ruwan dumi kina gasa kanki yanda ya kamata dan Allah ,sannan maganin hausa ma ki nema masu kyau na karin Ni'ima da abunda baa rasa ba kinga dai yarinya ce Ke In bakiyi da gaske ba wurin gyara kanki ,mijin ki wani auren ze sake kinsan maza ba tabbas ne dasu ba kiyi hakuri Allah ya baki lafiya kinji "
Tunda likitan nan ta fara magana Asma take kuka ,kuka bana wasa ba ashe kallon Matar aure take mata ?yau inda zata fada mata ita ba matar aure bace bata hanyar sunna aka mata haka ba da ta tabbata bazata bata lokaci wurin bata wadannan shawarwarin ba , inama amatsayin matar aure tazo asibiti awannan lokacin ,rayuwar ta ta gama taggayara ya cuceta ya lalata mata rayuwa ya zalunce ta, meyai saura arayuwar ta? ,duk wani burbushin mutunci datake dashi yanzu babu ya gama yi mata fatali dashi,
Ganin irin kukan da take ne yasa jikin likitan karayin sanyi ,kamo hannun ta tayi ahankali ta cigaba da lallashin ta ,godiya tayima likitan ta fito wani jiri na dibar ta
A reception ta same shi da ledan magungunan ahannun shi ,yana ganin yanda ta fito ya tabbatar kuka tayi batare daya mata magana ba yayi gaba yana jin haushin likitan Dan babu mamaki ita ta sakata kuka ,bin bayan shi tayi jiki asanyaye.
®️Mamy duk yanda taso danne kukan ta hakan ya faskara ,sosai takejin takaicin fada Auren Asma har cikin zuciyar ta ,tasan Asma yarinya ce me hankali bazata taba kuskuren mishi abunda zesa ya fasa auren ta ba ko ita da ta ksance mahaifiya agare ta bata taba mata miss behaving ba bare saurayi ,
A haka Su Fahad suka shigo suka same ta ,hankalin su ba karamin tashi yay ba "Mamy what's wrong "? Fahad ya tambaya yanajin bbu dadi aranshi.
"Mamy dan allah ki mana bayani ,ya zaayi ki zauna kina kuka hakan nan ,idan dan rashin ganin Asma ne gamu nan ai zamu tsaya kai da fata wurin nemo ta kinsan baza mu bari Acutar mana da ita ba "
Share hawaye Mamy tayi cike da takaici da bakin ciki tace "Ahmad ya fasa auren Asma ...."
Da sauri suka juya su dukan su atare jin karar faduwar mutum a kasa.
YOU ARE READING
ASMA'UL HUSNAH!
Mystery / ThrillerA lokacin da duniya ta mata zafi, rayuwa ta mata kunci ta rasa wanda ze lallashe ta ,A sanan ya bayyana mata duka wani sirri dake zuciyar shi ,amman banyanar hakan be sa taji wani sanyi ko dadi cikin zuciyar ta ba ,Saboda Ahmad ya mata tabon da ya r...