part 1

9 1 0
                                    

Bismillahi-rrahmani Rahim.
D

ukkan godia ta tabbata ga Allah SWA ma mallaki komai da kowa wanda ya halicci dukan abunda kea cikin sammai da kassai.
Ina rokon Allah dayabani ikon rubuta wannnan labari lapia sannnan yabani ikon karesa lapia.
Dukkan abunda zan rubuta aciki na kuskere Allah ya yafemim sannnan dukan abunda zan rubuta aciki na lada nida na rubuta daku da kuka karanta Allah yahadamu acikin ladaah.

*Naudhiii *
by Meerah(HijabieQueen)
Started on 27-12-2022
P

age 1

misalin karfe 10da dare Cen jikin wata yar bukka na hango wata yarinya wanda bazata wuce shekara 8-9 rakube take cikin bukkan se rawan sanyi takeyi da alama sanyi takeji sakamakon wethern sanyi muke ciki.Bakinta se karkarwa takeyi da alama magana takeyi hade da rawar sanyi yayinda idonunta kea fitar da hawaye da alama a jigace take.koda na leka dayar bukkar yaraneh wanda suma shekarunsu baze wuce 11-12ba da alama yan biyu neh kwance suke hankalinsu akwance se sharar baccin su suke abunsu babu abunda kea damunsu.koda na leka dayar bukkar ma wata mata nagani ta dan manyanta da wani dan tsoho wanda baxe wuce 45yrs ba yanayi mata mata.yanzu dan Allah ma'u bazakiji tausayin yarinyar nanba kodan marainiyace kibar ta awaje ita kadai da wannnan uban sanyi eyee ma'u wani mugun kallo ta aikowa malam jauro wanda yasashi hadiye sauran magan ganunsa ya juya ya kwanta batare da yakara cewa komaiba.koda na sake lekawa dayar bukkan wani saurayi matashi nagani wance shima yana sharar baccinsa,wannnan kenan.

Wani iskaneh yafara kadawa me sanyin gaske wanda yasani fitowa cikin sauri domin tausayin yarinyar daya kamani asannu naga iskan nayi wurin yarinyar yana curewa cikin alamun kaman xe koma wata halitta.wani dan tsoho neh naga ya bayyanah  fari sol 🙄 dashi gashinsa har gadon bayansa yayinda kashinma yakasance fari kayan sa ma farare wani kamshin turare naji wanda yasani lumshe ido nasake bude wa wuri yasamu daga gefen yarinyar ya zauna yayinda ya tallafo kan yarinyar ya kwantar bisa cin yarsa ya daga hannu sega bargoya bayyana yq rufe mata cikin ta sannnan yakara mika hannu kawai se dan gar washi a kwasko ya bayyana seya tura mata ta kasan bargon.se tafara sauke ajikin zuciya da alama she's feeling comfortable yanzun.murmushi naga yana saki yayin yake shafa dogon gashinta,cen Kuma yadena wannnan murmushin yayin da ya hade ransa yakuma daga hannu samaa se kawai naga dukkan bukkokin cikin dan gidan samansu ya kwaye yayin da wani uban iskaa kea busawa ciki.koda na leka naga yan matan nan se rawar sanyi sukeyi da alama sanyi sukeji sabanin daxu,koda na sake lekawa dayar ma haka naga dan saurayin nan yana rawar sanyi,haka zalika dayanma sede wannnan matar da aka kira da ma'u ita kadai kea rawar sanyi yayinda malam jauro kea bacci hankali kwance.wannnan kenan.

Koda yasake fita wurin yarinyar tana nan yanda nabarta wance kan cinyar wannan tsoho yayin da shi kuma hannunsa ruke ta casbaha yanada lazimii.ido nasake budewa nakare masa kallo yanada tsawo matsaici yayin da fuskarsa kea dauke da dogon hanci da madedecin labba fatarsa tafara tattarewa sakamakon tsofa gashinsa har gadon bayansa sede yaki dagowa naga kalar idonunsa ina nan tsaye ina jiram ya dawo domin kawo muku rahotu amman yaki daga kansa  se ma alamu dayamin da da hannu akan nabar wajen😂😂sum sum na tattara yar birona da jakana nakama gabana.

NaudhunWhere stories live. Discover now