1

40 7 9
                                    

*KUKAN KURCIYA...!*
'''Gajeran Labari.'''

*©️Halima.hz*
*Halimahz@Arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

*(1)*
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".

Kalmar da na ambata kenan ina me saurin dafe bango saboda hajijiyar da ke neman ɗibana ta watsar a ƙasa.

A lokaci ɗaya jina da ganina suka ɗauke na tsawon daƙiƙu, na ƙara rumtse idanuwana da tartsatsin wuta ke ambaliya a cikin su.

Ƙafafuna suka min nauyi na kasa ko da motsa su balle na iya ɗaga su na nemi madafar tsayuwa, zuciyata ta matse, ƙirjina ya shiga bugawa tamkar ana buga mandiri, wucewar daƙiƙu biyar ina dafe da bango kafin na samu na dawo hayyacina, zuciyana da bakina ba su fasa maimaita kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ba.

"Nura!". na kira sunan da wani irin amon sauti da ban san ina da shi ba. kuma tunda na ambaci sunan nasa sai na ƙara ƙafewa tamkar gunkin da aka sassaƙa, yawun bakina ya bushe.

A wannan lokacin da nake manne da bangon ƙofar gidan mu, a jikin rila, iska ce me sanyi take kaɗawa ta ko'ina, duk mutanen da suke wucewa jikinsu lulluɓe yake da rigunan sanyi su na ƙanƙame jikinsu saboda mashahurin sanyin da ake zubawa a garin, irin sanyin nan da haƙora ke caccakewa da juna, amma ni a lokacin wani uban gumi ne ke keto min na kata'i, wanda lokaci ɗaya ya jiƙa min jiki naji tamkar an watsa min ruwan zafi.

Idanuwana da basa gani sosai a cikin gangamin hazon da ake yi, na kanne su ina bin bayansa da kallo, ina kallon yanda yake takawa yana tafiya yana barin kusa da ni, cikin kaina ina ƙirga kowanne taku na tafiyarsa, yayinda zuciyata ke matsewa tana ƙara cunkushewa da sautin takun tafiyar tasa.

Sai da ya isa bakin motarsa ya buɗe zai shiga, sannan na samu wani ɗan guntun kuzari a tare da ni, na sulale gwiwoyina suka zube a ƙasa, ƙarar sautin bugun simintin yay duka har cikin dodon kunnena.

"Nura! ka dakata Nura don Allah".

Bakina ya motsa da ƙyar wajen faɗin hakan, kuma furucin ya fito tattare da matsanancin sabon kukan da ya kufce min.

Na dinƙa bin Nura da kallo ta cikin ruwan hawayen da ya taru a idona, kallonsa na ke amma wani sabon mutum na daban nake gani a tare da shi, domin asalin Nura da na sani ba zai taɓa iya ruguza zuciyar mace ba, macen ma wacca ta aminta da shi, ta shaƙu da shi, tayi dukkan amanna da shi akan cewar shi ɗin nata ne, kuma ita ɗin tasa ce, macen da suka shafe shekaru biyar su na tsafatatacciyar soyayya, wannan macen da a kullum yake furta cewa ke ce uwar ƴaƴana, ke ce mafarkina, macen da bai da wani buri da ya wuce yaga ya mallaketa, amma a yau ita yake kallo yake furta mata cewa babu ni babu ke, *ME YA ZAMA SILA WANDA BAN SA NI BA?.*

"kiyi haƙuri Mujahida...".

Furucin nasa ya yanke dukkan tunanina, ya kuma nemi yay raga-raga da zuciyata, nayi saurin ɗaga hannu na dakatar da shi daga maganar da yake yi.

"Saura fa kwana ɗaya, Nura saura kwana ɗaya kacal fa, Nura me nayi maka a rayuwar nan?, wanne kuskure na aikata maka da ban cancanci ka yafe min ba?, Nura ka rasa lokacin da zaka ce ka fasa aure na sai a saura kwana ɗaya auren mu?, na shiga uku na lalace, me mutane za su ɗauke ni? wanne kalar tunani za su yi akan hakan? Nura me zan ce wa iyayena?".

Na faɗa ina dukan kaina a jikin garu, sai na tsinci maganar Nura na cewa da ni,"A yanda kika mayar da kanki a haka za su kalli maganar lalacewar auren ki, banda niyyar tozarta ki a rayuwa, ada ina sonki sai dai yanzu kin fita a raina, domin ba zan iya zaɓawa ƴaƴana uwa irinki ba, haka nima ban cancanci auren mace irinki ba, ki koma cikin gida, ki zauna ki natsu kiyi nazari, anan zaki fahimci dalilin da yasa na fasa auren ki, na barki lafiya".

KUKAN KURCIYA...(WA GARI YA WA YA?)Where stories live. Discover now