*KUKAN KURCIYA...!*
'''Gajeran Labari.'''*©️Halimahz*
*Halimahz@Arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya**(2)*
"Ya Subhanallah!".
Alhaji Musa da Baba Sabitu suka taso da sauri suka yo kan Mujahida da ta sume a wajen.Iya ta fita daga parlon cikin tashin hankali taje ta ɗebo ruwa ta kawo, Baban Mujahida dai na zaune kawai ko motsawa daga inda yake bai yi ba, idonsa ma na kallon can wani gefe na daban, shi kaɗai yasan abunda yake ji a zuciyarsa, takaicin abunda matarsa da ƴarsa suka aikata kawai yake yi, ya sn akwai ƙaddara amma a wannan fagen sai dai ya alaƙanta hakan da ganganci, domin da ace ba su kai kansu ba da babu wacca zata tsinci kanta a halin da take ciki.
Har tsawon wucewar mintuna 5 kafin nan Mujahida ta farfaɗo.
Ina buɗe ido na ƙara fashewa da sabon kuka, nayi kan Ummanta wacca ta riƙe kanta da hannaye duka biyu, banda hawaye masu zafin gaske babu abinda ke suntiri a saman kumatun ta, zuciyarta danƙare da baƙin ciki, ƙunci, danasani tare da nadamar abunda take aikatawa a ɓoye, abunda ta ɓoyewa jininta banda mahallacinta da ke kallon duk wani motsinta.Na damƙi kafaɗunta ina yi mata wata iriyar girgiza ina faɗin,"Ummana kiyi magana, idan kika yi shiru su Baba Musa za su yi miki kallon mutuniyar banza, don Allah Umma ki buɗe baki ki faɗawa Baba yayi kuskure, ba ke ce matar da yake zargi ba, hasalima ke ba ki haifi wani ɗa Auwal ba, kiyi magana Umma ko Baba zai maida igiyar aurenku, Ummana idan kika bar gidan nan ina zamu saka kanmu, ke ɗaya ce gatanmu, ba zamu taɓa samun wacca zata bamu kulawa irin wadda kike bamu ba, babu mai bamu irin tarbiyar da kika bamu Umma, don Allah Ummana ki faɗa musu ba ke ba ce".
Maganar Baba ta katse ni da abunda nake faɗa. "Ni zancen da nake son sa ni waye Auwal? A ina kika samo shi? Kuma waye ubansa?...".
Bai ƙarasa zancensa ba Ummana tayi saurin tarar numfashinsa,"Haba Habibu karka yi min mummunan zato mana, lalacewar tawa bata kai nan ba, bata kai naci amanar aurena ba, ka dai fi kowa sanin cewa a budurwa ka aure ni".
Sai tayi shiru tana saka gefen ɗankali ta goge hawayen fuskarta, sai dai tana gogewa wasu na zubowa.
Sai kawai na kifa goshina a saman cinyarta, tausayinta da tausayin kaina suka kama ni, duk a girgiza nake, nema nake na ɗimauce, na san wace mahaifiyata, macece ta ƙwarai mace ta gari, su kuwa waɗancan matan da ke rubutun batsa sun fi kama da karuwai, to taya za ai ace wai Ummana ke rubuta irin wancan rubutun da yay sanadin lalacewar tarbiyata.
Cikin dasashshiyar murya na ke faɗin,"Me yasa Ummana?".
"Ba komai yaja min faɗawa wannan musibar ta harkar rubuce-rubucen bariki ba illa don neman ɗaukaka da kuma neman kuɗi, da mutuwar zuciya. sai dai ga shi kashh na aikata abunda har mutuwa ba zan daina zubar da hawaye ba, babu a idon wanda Ummu Auwal ke da mutunci, zaton kowa ni karuwa ce ko yar lesbian duk saboda irin iskancin da nake rubutawa, ba kowa na illata ba sai kaina, sau tari maza karuwai na kiran wayata su na nemana da yin lalata, haka ma yan maɗigo wanda in ace ban ɓarar da mutumcina ba da babu wani kwarton namiji da zai kira ni ina matsayin matar aure da sunan zai yi lalata da ni, sai ga shi a bayan fage kuma ba tare da sanina ba ƴata na aikata maɗigo, ƙalu innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".
Sai kawai tayi shiru ta kasa ƙarasa maganar, kuka sosai take yi, parlon yay tsit hatta ni kaina na daina yin kukan saboda ciwon da zuciyata ke yi min, ba komai nake hangowa ba sai lokacin da na fara karatun littafin batsa, ina tunawa tun ina ɗauke kai ina kawar da ido har na zo na kwaɗaitu da son karatun, kuma da na zo na fara sai ya zamar min tamkar yunwar ciki, idan ban karanta ba bana samun natsuwa, duk da nasan abunda nake karantawa ɗin haramun ne, ya ilahi ka yafe min ka yafewa mahaifiyata.
"Tabbas a yau nayi danasanin ƙin karɓar gaskiyar da aka jima ana faɗa mana, gaskiya da nasihar da bayin Allah salihai ke ta faɗa mana, sai dai muka toshe kunne muka zauna akan zugar ayarin ƴan abi yarima asha kiɗa, muna rubutawa mu lalata aure, mu lalata yaran wasu, namu kuma muna yi musu nasiha akan su guji aikata hakan. sai gashi reshe ya juye da mujiya, na rubuta abu da kaina wanda ko mijina ba zan so ya karanta shi ba balle kuma ƴar da na haifa, na san bamu isa mu yiwa Allah wayo ba sai dai ban taɓa tsammanin sakamakon zai zo min ta haka ba. Yanzu *WA GARI YA WA YA?*, kamila kuma salihar ƴata ta lalace ta sanadin karanta baɗalar da nake rubutawa, an fasa aurenta, ta kamu da ciwo me muni, ni kuma mijin da nake taƙama da shi ya sake ni, Hasbunallahu wani'imal wakil, ga kuma hukuncin ubangiji da yake jirana domin Allah kaɗai ya san adadin Al'ummar da suka ɓaci, Allah kaɗai yasan adadin da suka yi min Allah ya isa a akan hakan, Allah kaɗai yasan adadin tsinuwar da ke kaina, na shiga uku ni Bilki, Muhajida ki yafe min don Allah da Annabinsa, ba kiyi sa'ar uwa ba Mujahida ki yafe min".