*MATAR UBA*
*Na*
_Muneera_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
_TRUE LIFE STORY_
*DUKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI ME KOWA ME KOMAI DA YA KARA BANI DAMAR KAWO MUKU SABON LITTAFINA ME SUNA A SAMA DAFATAN ZAKU BANI HADIN KAI MASOYA NAGODE*
*DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMAR DUK WANDA YAGA NAYI BA DAI DAI BA KAR YAJI KOMAI YA MIN GYRA ZAN KARBA KO DAGA WURIN WAYE NAGODE*
*NIDIN BA MA'ABOCIYAR YIN TYPING ME YAWA BACE DAN ALLAH KAR AMIN KORAFIN TYPING KU BINI A HANKALI HAR NA AJIYE AL_QALAMINA NAGODE*
*BAN YARDA WANI KO WATA SU CANZA MIN LITTAFI TA KOWACE SIGA BATARE DA IZINA NA BA*
*HAKIKA WANAN LABARIN YA FARU A GASKE KOME KUKA GANI CIKIN YA FARU SEDAI DAN ABINDA ZAN KARA AKAI*
*Sadaukarwa ga duk Wanda ya rasa mahaifiya*
Page 1
"Innallilahi waina illahi rajiun mamana abbba ka Kara gudun motar Dan Allah Dan wallah kamar numfashin mamana ya tsaya" budurwar da bazata Gaza Shekarau asirin da daya ce take wanan furucin
"Haba mana Amira Dan Allah kiyi shiru kibar abba yayi tuki a nutse in shaa Allah mama ba mutuwa zatayi ba" wata a gefe Wanda yake nuni da ita din Yayar Amira ce ta fad'a tana maida kwalar da ta zubo daga cikin idonta.
Amira kuwa tsurawa mahaifiyar Tata ido tayi tana Jin wani nauyi a kirjin ta tana Kuma tuno irin maganganun da sukayi da maman nata jiya da dadare se hankalin ya Kara tashi.
Ji tayi mahaifiyar Tata ta ambaci la'illah ha'illah lah sanan ta Kara damke hanun ta tare da Jan wani numfashi se Kuma ta saki hanun ta, Amira Kara tallafo mahaifiyar Tata tayi Dai Dai nan Kuma suka tsaya a gate din asibitinLikitan ne ya fito ya Kale su "Ina mahaifin ku yake" doctor fada mana menene in ka ganmu ai ka ganshi, Jan numfashi yayi Yana kallon su musamman Amira sbd ba yanzu ya sansu ba ya sansu tuntuni Kuma yasan irin shakuwar da take tsakanin wanan ahali tataro duka kwarin gwawar sa yayi ya kali khadija wace itama tayi tsiro Dan gwara ita sau Akan Amira tafi Amira dauriya sosai yace "khadija Allah da ya fimu son mama ya karbi abarsa" bangaje shi khadija tayi ta fada Dakin da maman nasu take Kwance ta ganta idon ta Yana kallon sama kuka sosai ya Kuma kwace Mata a ranta take Jin wani irin zafi me rad'ad'i dama akwai ranar da za'a wayi Gare ace mama ta rasu Innallilahi wa'ina illahi rajiun, Khadija ce ta shigo 'Dakin tana kallon gadon da mahaifiyar tasu take kallon fuskar ta Khadija tayi se taga kamar likitan nan karya yake musu sbd babu abinda ya canza a fuskar mahaifiyar tasu se taga ma kamar murmushi takeyi, karasawa tayi bakin gadon tayi addua sanan ta rufe idon maman nasu kallon Amira tayi wace ta kasa motsi Kuma ta kasa yarda da abunda kunenta yaji Kuma idon ta ya gani gani take kamar mafarki take ba gaskiya bane.
Jan hanunta Khadija tayi suka fito daga Dakin a bakin kofar suka tarar da mahaifin nasu Yana kallon su, rungume shi sukayi tare da had'a baki wurin sanar Dashi cewa mahaifiyar tasu Allah ya Mata cikawa shi kuwa idris Ji yayi kamar an soka masa wani Abu kirji matar sa abun sonsa matar rufin asirin sa Aliya ce ta rasu matar da suka doshi Shekara Talatin tare baiwar Allah Aliya se yaji wani irin hawaye Yana zubo masa shi a rayuwar sa be taba hasaso cewa Aliya zata mutu tabarshi yafi Bawa kansa mutuwa Akan Aliya gani yake kullum shi ze tafi ya bar Aliya bawai ita ba ashe itace zata fara tafiya ta barshi a wanan duniya me cike da abubuwa iri iri beda buri a rayuwar sa na yayi kudi yaga ya farantawa Aliya se gashi lokacin da Allah ya fara azurtashi Allah ya dauke Aliya subhanallilahi ya fadi a zuciyar sa Yana me sakin yaran nasa guda biyu wato Khadija da Amira Wanda hawaye ya kasa barin fuskar su (Wanda a nasu tunanin kukan rashin mahaifiya ne amma wanan kukan kansu sukewa kuka sune abun kuka yanzu ba ita ba da Allah yasa tayi kyakyawan karshe).
Karasawa yayi ya kali Aliya da take Shimfide Akan gadon Wanda se yaga kamar bacci take kamar in ya kirata zata amsa tunda mahaifiyar sa ta rasu ba'a Kara masa mutuwa irin wanan ba Aliya masoyiyar sa ta asali wace ta so shi tun beda komai yau gashi Allah ya dauke ta Innallilahi wa'ina illahi rajiun kawai yake maimaitawa a kasan ransa ya kasa motsi kwata kwata.
Mijin Khadija ne ya shigo asibitin Shima hankalin sa a tashe ya hango Khadija rungume da Amira suna ta kuka kamar ransu ze fita karasawa yayi ya Kale su se Kuma ya Kara maida dubansa ga Khadija kafin yace "Khadija jikin maman ne" girigirza masa kai tayi tare da sakin wani kukan tana fadin "Abban Nasirin Allah yayiwa mama rasuwa" se Kuma ta Kara fashewa da kuka kafin ta Kara so inda yake ta rungume shi, Innallilahi wa'ina illahi rajiun ya maimaita kafin ya dube ta yace "toh yanzu Ina abba yake" magriba ta gabato se muyi sauri mugama da asibitin kafin a Kira sallah kasa cewa komai Khadija tayi saboda bakin ta baze Iya furta komai ba.
Mijin Khadija shi ya kamala komai na cike ciken asibiti sanan akasaka gawar Aliya a ambulance din asibiti sanan shidai mijin Khadija shi yaja motar Abba Bayan yasa Khadija, Amira da abba a motar suka nufi gida
Tun daga bakin layin da suka shigo sukaga kowa yayi cirko cirko domin Kan su bar asibitin Seda mijin Khadija ya Kira kanen Aliya ya sanar dasu rasuwa kafin su baro asibiti suma Yan uwan nata duk sun taho gidan suna karasa shigowa layin makota Kowa da hawaye a fuskar shi suna kallo maaikatan asibiti suka fito da gawar Aliya kowa ya Kara fashewa da kuka da gaske kenan Aliya ta rasu kowa yake fada a ransa saboda Aliya mutum ce mutuniyar kirki ce tafi Shekara 20 tare dasu Amma babu Wanda ta taba samun matsala dashi tsakanin ta da kowa Sam barka ne batada matsala Mata ce me matukar hakuri da kau da kai Aliya ce kawai a unguwar nan za'a kama danta a daka Amma bazakaga ta leko ba bale Kuma Har tayi magana Kuma duka layin babu Wanda zece be mori Aliya ba
Haka suka kwana a gidan cike da y'an uwa saboda ba'a samu an kaita ba a lokacin sbd dare yayi sedai an saka jana'iza karfe Tara na safe
Da safe haka aka shirya Aliya za'a kaita gidan ta na gaskiya (Allah ya jikan mu in mun mutu subhanallilahi 🥹) Khadija, Amira, habiba, Ahmad, Khalifa, da yar karamar su mufida haka suka tsuguna Kan gawar mahaifiyar tasu suna kuka suna masu roka Mata rahama a gurin Allah kafin kanenta su shigo a fita da ita Khadija tayi sauri zata bisu aka rike ta, tana fadin mamana karku tafi da ita Innallilahi waina illahi rajiun, itama Amira haka ta dinga kuka Ana ririke ta haka aka fita da ita makota nata fadar kyawawan halayen sekaji wanan yace haka ta min kaza maman Khadija baiwar Allah sekaji wancen Nima haka ta min kaza Allah ya jikan ki maman Khadija (shiyasa ake so ko yaushe mutum ya aikata aikin alkhairi sbd mutuwa se kaji mutum Yana ai ni Bana tsoron abunda mutane zasuce aikana sun Dade basu ce toh Wlhy kuji tsoron Allah sbd in mutum ya mutu halin sa na ainahi mutane suke fada Koda kuwa mumunan Hali yake zasu fada mala'iku Kuma su dauka suyi sama dashi Allah yasa mudace)
Fatiman ku ce👌🏽