2

38 7 1
                                    

*RAGAMAR DAMISA*
       '''FreeBook.'''

*©️Halimahz*

*SADAUKARWA GA:-*
Muhammad Kareem(MK)

_for your business advert DM 08145146915._

*(2)*

ƙarar azabar da Goje ya saki ta haɗe da damƙar wuƙar hannuna a lokaci ɗaya, ganin yacca wuƙar ta huda gefen ƙirjinsa jini ya fara malala yasa nayi mugun gigita na sakar masa wuƙar na faɗi gefe guda tsabar ruɗewa.
tsananin tashin hankalin da na shiga na farat ɗaya yasa na kasa ko da haɗiye yawun da ya taru a bakina, ban yi wani ƙwaƙwƙwaran motsi ba naga yaran Goje sun arce daga wurin, ananne fa hankalina ya ƙara kaiwa ƙoluluwar tashi ganin an tafi an barni da gawa da kuma guntun ran da yake a hannun Allah.

"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". na furta ina me rufe bakina, yayinda ƙwaƙwalwata ta tafi tunanin mafita, tabbas idan naci gaba da zama anan ƴan sanda suka zo ni za'a kama da laifin kisan Ƙaura, ga kuma Goje da babu tabbacin zai rayu, kenan zai zama hukuncin kisa biyu ya hau kaina?, ga cikin gida in an tashi bincike cike yake da hodar iblis.

wannan tunanin yasa na fashe da matsanancin kuka me ban tausayi, a hankali nake ambaton sunan ubangiji tare da neman taimakonsa akan ya fidda ni daga wannan tsaka mai wuyar, da ma ance duk wanda bai ji bari ba yaji hoho.
idan na kalli inda gawar Ƙaura dake a yashe sai in koma in kalli inda Rashid yake shima a sheme baya ko motsi, wanda nasan idan shima bai mutu ba to yana dab da mutuwa, cikin ƙanƙanen lokaci sai na fara neman zaucewa.

layin tsit kamar yanda ya saba kasantuwar dama gidana ne kaɗai ginannne sauran duk kangwaye ne, sakamakon tsit na layin sai yasa gunjin kukan da nake yi ya sami fita sosai, kamar daga sama naji muryar Rashid na kiran sunana a hankali, ya ambata cikin tsananin azabar da ke cinsa.

"Asma!, Asma!".

kai na ɗago a hankali kuma na sauke idona akansa ina kallonsa ta cikin ruwan hawayen da ya taru a idona.

"Asma!, zo nan, taho wajena kar wani abu ya same ki, kina ina ne bana gani da kyau, bani hannunki nan kinji".

ban ko iya motsi ba balle magana, hawaye ne kawai ke sunturi akan kumatuna, sai juyi da nake yi da kaina, na kuma toshe bakina na hana sautin kuka fita saboda bana so ya jiyo ni, ni ba tausayinsa nake yi ba, ko kaɗan bai bani tausayi ba, domin kuwa tsab ma zan iya ƙara daɓa masa wuƙar na ƙara shi, to sai dai tsoron alƙalin da zan tsaya a gabansa  nake.

"Awarwasa kar ku bari wani abu ya taɓa ta kaji ko, bani hannunta nan don Allah".

maganar yake yi cikin ƙarfin hali da dauriyarsa, kuma babu wani mai imani da zai ji sautin muryarsa bai yi ƙwalla ba.
gwiwoyina na shiga ja har na isa inda yake, na miƙa tafin hannuna na saka a cikin nasa da ya buɗe min, sai naji ya damƙe yana sauke wani gwauron numfashi na azaba.

"kuka kike yi?".
nace,"kayi haƙuri don Allah".

"bana son kukan ki, idan kin san hawaye na zuba yi ƙoƙarin tsayar da su idan ba haka ba bazan taɓa yafewa kaina ba, bana gani da kyau balle in hana su da kaina, amma ki taimaka min".

jijjiga kaina nayi cikin sauri kamar yana ganina, da ɗayan hannuna nayi ƙoƙarin goge hawayen sai dai sam ya gagara tsayawa. hannu na kai zan cire wuƙar da ke soke a gefen ƙirjinsa karaf naji ya damƙe hannuna yana juya min kai a hankali.

"bana so shatin yatsun hannunki su fito a shaida".

yana faɗar hakan ya fizge wuƙar daga ƙirjinsa, duk jarumta da taurin zuciya irin nasa sai da ya ƙwala wata gigitacciyar ƙara a sa'ilin da ya cire wuƙar, amma saboda dauriya irin tasa shi ɗaya haka ya buɗe idanunsa tarr ya zube su akaina yana min irin wannan kallon da ya saba, kallon so da ƙauna da tausayawa gami da jin ƙai, ƙwayar idonsa sun kaɗa sunyi jawur har da taruwar jini a cikin su, ga naman ciki kamar ya bullutso yana neman fitowa, ni kuwa ganin uban jinin da ke bin ƙasa shi ya tsorata ni yasa idanuwana kullewa.

RAGAMAR DAMISAWhere stories live. Discover now