GIDAN MIJINA

87 3 0
                                    


*_______________________________________*

🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨

Short story

Story & written by

MAMAN AFRAH

     Page
32--33

  Haka Aysha tayi wunin gida a ranar ranta kwata kwata babu dadi domin ganin mahaifinta cikin ciwo mahaifiyarta cikin damuwa yasa taji gaba daya duniyar bata mata dadi. Haka ta bar gidan zuciyarta cike da damuwa domin gaba d'aya ma shi ciwon Abban nata an kasa tantance wane iri ne wani k'aton k'urji ne wanda girmansa ya yi mutum ya hada hannayensa wuri d'aya ya dunk'ule tauri k'igir dashi kamar dutsi😭 haka dai Ummarta tayi ta kwantar mata da hankali kafin ta musu sallama ta kama hanyar gida. A lokacin karfe shida ma tayi, sai bayan ta hau dan sahu ta tuna cewar lokacin dawowar Kb gida ma ya wuce. Tana sauka ta baiwa dan sahun kudinsa, karamar kofar get din ta tura ta shiga ta maida ta rufe mai gadi dake zaune kan bencinshi yana jin redio ya gaisheta ta amsa masa sama sama dan gaba daya jinta take kamar ba a duniyar mutane take ba, damuwar dake ranta ta hanata ta ji dadi a zuciyarta koda k'ankani ne. Har ga Allah tana son Abbanta tana kuma tausayin Ummarta gashi basu da wani d'a me debe musu kewa tunda ita kadai suka mallaka sai kawu Habibu dake zuwa lokaci zuwa lokaci domin taimaka Ummarta wajen jinyar Abban nata kamar yadda Ummar ta sanar da ita yau,  a cewar Umma anki sanar  da itane saboda kar ta shiga damuwa saboda abinda take dauke dashi tabbas! kwa Umma tayi gaskiya domin gashi yanzu tunda ta yi arba da halin da Abbanta ke ciki bata samu sukuni ba ko miskala zarratin. Tana tafiya tana zancen zuci bata anakara ba sai ganinta tayi har tazo sashinta, bude kofarta ta yi ta shiga ta je ta ajiye jakarta da mayafinta,  ta fito domin zuwa sashen mijinta dan ta ga motarsa alamar yana nan kenan tunda tasan matsawar ya dawo to fita kwa ta zama dole, amma kuma tunawa da tayi jiya ma ba Inda ya je wannan yasa ta fara tunanin ya fara gyara halayensa. Sai dai kuma in ko Aliyu ne ya zo suka fita tare a motarsa. Tura kofar tayi ta shiga amma kuma bata ga Kb a ko ina ba hatta bayin ta duba baya ciki, hakan yasa  ta fara tunanin ta tambayi me gadi ko ya fitane bayan ya dawo? To amma kuma me yasa be kulle part din nashi ba? Tunda ya san yanzu ba su kadai bane a gidan akwai Ummulkhairi. Fitowa tayi da niyyar zuwa tambayar me gadi, shaida mata yayi Alhajin yana ciki bai fita ba,garden ta nufa wai ko can ya je yake hutawa, tun daga nesa ta hango inda kujerun suke amma babu kowa a kansu. Cikin lambun tabi ta dan zagaya amma babu shi babu alamarsa,abun ne ya daure mata kai haka ta kamo hanya ta dawo har zata shiga daki sai wata zuciyar tace ta tambayi Ummulkhairi  dan jim tayi tunda tasan ba wani shiri suke ba amma a haka ta doshi dakin Ummulkhairin tana fargabar kar ta mata rashin arziki. Tana zuwa kofar dakin ta fara jiyo tashin sautin dariya data kasa banbance mamallakan muryan, kwankwasa kofar tayi amma ba, a mata magana ba kuma tasan an ji, sake nocking din tayi a karo na biyu, jin ba, a mata magana ba yasa ta tora kofar, abinda idanunta suka gani👀 shi ya sanya ta razana Ummulkhairi ce da Kb zaune akan kujera daya kanta akan kafadarsa suna kallo a waya yayin da wayar take a hannun Kb suna ta dariya abinsu hankalinsu kwance, kamar ma basu san da shigowar Aysha dakin ba. Wani kululun bakin ciki da takaici ne suka taru suka mamayewa Aysha ranta take ta ji wani kishi ya hayayyako mata hawaye ne suke neman zubo mata amma kuma basu samu dama ba domin kwa tayi namijin kokari wajen ganin ta danne su, bude baki tayi da niyyar yin magana amma kuma maganar da Kb yayi ita ta hanata furta tata maganar.

"Dalla malama ya zaki fadowa mutane daki ba sallama? ko irin tarbiyar gidanku kenan? " ya fada yana wani hade rai tare da zaro mata idanu.

"A, a toh kai ma dai ka fada Ya Kb, tunda idonka ya nuna maka yanzu"Ummulkhairi tace tana dariyar shekiyanci.

"Yanzu dan na shigo dakin nan kake kiran babu tarbiya a gdn mu?  Kafin in shigo sau nawa na kwankwasa kuka kyaleni?bayan na shigo na ganku manne da juna bayan ku ba ma, aurata bane ba kuma muharraman juna bane, kai koda ku muharraman juna bai kamata kuyi irin zaman da kuka yi ba yanzu amm.......

GIDAN MIJINAWhere stories live. Discover now