1

550 9 1
                                    

💔 *RAYUWAR MAKARANTA* 💔




*From the writer of  RUWAN DARE,RAYUWATACE,TAWA KADDARARCE HAKA,GABA DA GABANTA AND DIJEN KAUYE*🥰

*_follow me on watt pad @ prettysalma17_*




*1_5*💔




Ranar monday tushen aiki,ko bature yana tsoron ranar,a ranar ne kuma MI'AT  tasauka a cikin GG,suna shigowa tadinga bin makaranta da kallo gabanta nata faduwa har suka isa office din principal a India Akagama Mata komi akabata house(yellow) house kenan,nan yayanta yamata sallama yaciro kudi 1k yabata.
"To mi'at gaki a boarding skul,inafata zaki maida hankali akan abinda yakawoki,ki maida hankali kan karatu kada kibiyema kawayen banza,babu ruwanki da rashinji kinjidai irin fadan da ammie tamaki,kinsan cewa badason ran ammie kikazo boarding ba amma babu yadda ta iya don taga kinaso shiyasa tahakura tabarki kizo dan haka kibata mamaki kiyi karatu sosai kinji ko" yajuya zai shiga mota yatafi mi'at tayi saurin riko hannunsa cikin marerecewa kamar zatayi kuka idanuwanta sunfara cika da kwalla tace"yanxu yaya tafiya zakayi kabarni"

"Ehmana,bake Kikace kina so ba,keda gida yanxu kuma sai anyi hutu,idankuma kinfasa to mutafi tare"

Mi'at najin yace idan tafasa tayi saurin sakin hannunsa ,nan suka karayin sallama yatafi.

Hanyar class tanufa,wata yarinya tagani tatanbayeta"ke dan Allah inane SS 1A"

Wadda tatanbayadinne tanunamata sana tatafin

Shiga tayi cikin class din lokacin malam yana ciki,wani seat tagani a row na biyu layi na ukku mutum dayace akai nan tashiga ta zauna,tamaida hankalinta kan abinda malamin yake koyawa.

1:30pm dai dai timekeeper tabuga alamun antashi area class,kowa tana fitowa cikin natsuwa suna nufar hostel,itama mi'at koda tafito inda aka ajiyemata kaya nan tanufa tajawo trolly nata da wani big bag tanufi hanyar da taga saura nabi.
Koda tashiga hostel taga wata senior,ranta bai bata komiba tatsaya kusa da senior din takalleta ido cikin ido tace"ke dan Allah inane yellow house"

Ai wanan senior din da mi'at takira da ke tasaki wata uwar ashar datasa mi'at tarazana"kutumar babban bura'ubannan kayyasa,ke dan uwarki ni kikecema keee,aiko yau zan koyamaki tarbiya dan maicin uwarki ragameni tsawonki"
Duk da mi'at taji tsoro amma tadake tabata amsa da cewa.

"Yi hakuri dan Allah ni bakuwace yau nazo shiyasa bansan yanda abun naku yake ba"

"Aiko yau zansanar dake yadda abun namu yake,yau zakitabbatar da kinshigo GG,yau duk wani iskancin dake cikin kanki saina gogemaki harda dan ubanki nace kirageman tsawonki,ina tsaye kina tsaye matsiyaciya"

Turo baki mi'at tayi kawai taja trollyn ta da nufin tayi gaba aiko taji saukar marin dayasata sakin karar da batasan tayiba,cikin firgita tasaki kayan hannunta tace"minayimaki kika mareni,wayyo ammiena zata kasheni,Allah Ya isana wallahi"

Aiko ji kake tass saukar bugu tako'ina,harda samun wani icce taci gaba da dukanta......haba marry miye haka,tundazu ina kallonku naga duk abinda yafaru,tafadamaki yau tazo batasan kan rayuwarba saikimata uzuri ai"

"Dalla malama sakeni,banason iskanci,bakiga irin rashin kunyar datakeminba,narantse da Allah yau mai rabani da yarinyarnan said Allah,saici durin uwarta harda na ubantama"tafisge bulalar daniyar kara safkema mi'at ita amma Fiddy tayi saurin janye mi'at taboyeya bayanta,ita kanta mi'at din kankame fiddy tayi domin taji azaba iya azaba,nanfa fada yakaure tsakanin marry da fiddy,marry tayi rantsuwa sai tasake dukan mi'at itakuma fiddy tace muddin tasake dukan mi'at saita ramamata tunda bataga abinda tayimataba,fada sosai dan har suna neman dambacewa mate suka shiga tsakani,nan aka dinga basu hakuri.

"Narantse Da Allah feddy kifita sabgata,ke kanki sainaci uwarki azauna lafiya babu abinda zaki iyamin nafadamaki,dama taraki nakeyi"

"Babu a binda zaki iyamun ke kanki kinsani,nafi karfinki bama keba wadda takawoki duniyarma nafi karfita bare ke kucaka kazama wofi"

Dakyar akaja feddy zuwa cikin daki tareda mi'at.
After fadan yalafa,feddy tadubi mi'at daketa rusa uban kuka idanunta sunyi jajur har fuskarta tafara kunbura tace"kidena kukan hakanan kinji,kiyi shiru muje nakaimaki ruwa kiyi wanka kici abinci,kibarni da ita nice dede yinta,idan takamarta mugunta zangwadamata iyakarta wallahi"dakyar dai feddy tallashi Mi'at tayi shiru.
Bayan tadena kukan feddy tadubeta tace.
"Wane house aka kaki?"

Mikamata takarda mi'at tayi nan feddy takarba takaranta.
"Yellow house aka kaiki kenan"

Gyada kai mi'at tayi alamar eh.

"To sai kuma gashi marry ce House captain din dakin,amma kada kidamu kiyi zamanki nan,nasan muddin kikaje dakinta wallahi kinzama jaka duka har wanda baayi saitamakishi,idan kuma kinason can din to muje nakaiki"
"Aah bazanjeba zan zauna anan"

Tashi Senior feddy tayi taje takira wasu yara yan ss1 su sumayya da lubabatu tace ga yar kwana sun samu sukaimata kayanta,nan suka kwashi kayan suka kai kwanan sana ita da kanta feddy takai mi'at har Corner sana takoma side nata.
Itade mi'at tayi tagumi tana tunanin yadda daga zuwanta anfaracin ubanta hardama uwarta,ammie ta tuna nan wasu sabbin kwalla suka biyo kuncinta,tanaji inama batace tanason boarding ba,for the first time tayi regretting zuwa makarantar kwana,kallonta sumayya tayi cikin tausayi tace.
"Sis kidena kuka indai makarantace zaki saba wallahi,muma zuwanmu  na farko haka mukadinga kuka kullum sai munyi kuka amma yanxu munsaba saidema mubama wasu dariya,kima godema Allah badaga jss kikafaraba,mukam tundaga jss mukafara,munci uwarmu harda ubanmu,amma yanxun kinganmmunan bamu yarda adakemu sai dai idan an rutsa da mu wallahi,dan haka kima daina wahalar da idanunki kisaki jikinki tunda har aka kawoki coner dinnan zaki waye wallahi,luba fadamata yadda akecema gang dinmu"
Kallo luba tabi mi'at dashi tace"yo Allah natuba sumayya ai tunda har muka hakura kowama ya hakura wallahi acikin skul dinann,kemufa tsabar tsaurin idonmu sunan gang dinmu 7star,mu bakwaine a gang dinmu amma munfitar da daya saboda rainin wayon da tayimana,ammafa ina fata kinada dauriya don wallahi 7star muna amsar gashi duk randa aka jiyo kanmu,saidefa muma muna fanshewa ahto"

Itakam dai mi'at tanatajinsu amma hankalinta duk yakoma kan ammie dinta,tanaji inama tayi tsuntsuwa kawai taganta a gida gaban ammie nata.
Har 4 yayi mi'at nanan zaune batada niyar tashi tacire uniform nata har saida sumayya tadawo daukar container taganta tananan yadda suka barta,tsayawa tayi sololo tana kallonta."ke wai bazaki tashi kicire uniform nakiba kisaka check's ba sai anzo kora ko"

"Kora Kuma,atafi ina"

"Evening prep mana,ina kika saka check's din"

Nunamata trolly tayi,nan sumayya tazage tafiddomata check's nata sabbi yellow,cike da mamaki sumayya tace"yo yanaga yellow,yellow house aka kaiki kenan"

"Eh,Amma Senior feddy tace anan zan zauna wai"

"To indai hakane saide nabaki red ki saka,idan ba hakaba ana ganinki zaace kitafi dakinki"

"Ehto kibani naki mana nasaka idan kinada extra"

Tashi sumayya tayi ta bude akwati tafiddomata doguwar riga ta check red nan tacire uniform tasaka sana suka fita tare,mono suka wuce don suyi alwala suwuce masallaci.

Suna zuwa mono suka tarar da layi kowacce nason tayi alwala,nanfa sumayya tabama mi'at ajiyar white hijab nata.
"Rikemin hijab dina kigani nakutsa nasamomana ruwan alwala idan ba kutsawa nayiba wallahi saide mutafi batareda munyi alwalaba"
Amsar hijab din mi'at tayi tatsaya kallon ikon Allah.

Ihu sumayya tasaka tana fadin ga uncle mubarak nan yataho,kan kaceme kowa yadirare yabar mono harda yan ss3 din,cikin minti daya mono yazama kwalam babu kowa.

RAYUWAR MAKARANTAWhere stories live. Discover now