33

178 3 2
                                    

💔RAYUWAR MAKARANTA💔



*From the writer of  RUWAN DARE,RAYUWATACE,TAWA KADDARARCE HAKA,GABA DA GABANTA AND DIJEN KAUYE*🥰

*_follow me on watt pad @ prettysalma17_*





*_171-175_*💔




"Hakane love Amma wannan yazama dole nafadamaki domin kuwa kullum idan zantuna abinda na aikata inaji inama nice wadda Allah ya dauki rayuwarta,wallahi billahi baby bansan hakan zaisa mi'at tayi rashin lafiya ba har yakaiga ajalinta,tabbas nabiyewa son xuciyata amma ina fatan Allah yayafemun"

Cikin mamaki mufeeda take kallon merry tace"wat do you mean,kina nu fin kinsan ta yadda akayi mi'at ta mutu ne or wat?"

"No love,Amma nice naje wurin malami yamun aiki nasa aka dasamaki tsanar mi'at cikin ranki,shiyasa bakya ganin kowace mace saini kiyafemun love nayi dana sanin aikata hakan danayi"

Tashi mufeeda tayi kamar an tsunkuleta saiga hawaye sharrr a idanunta,itama merry tashi tayi tazo kusa da mufeeda da niyar kamata mufeeda tayi saurin kauce jikinta cikin kuka ta duke kasa tana cewa"why?why me?miyasa kikayi haka,how i wish nice ki kayima asirin da mi'at zata tsaneni bawai nice natsanetaba,how can i imagine cewa wai nice natsani mi'at harta komaga Allah banason ganinta,kaicona,banga amfanin rayuwa dakeba maryam,bantaba dana sanin tarayyata da ke ba sai yau,wallahi billahi da zan iya maido da hannun agogo baya tabbas yau da sai na maido dashi na goge duk wata rayuwar danayi dake abaya,bantaba dana sanin saninki arayuwanaba sai yau,i regret knowing you,zuwanki arayuwata ba alkairi bane baby alkairi acikinsa,kin kauce hanya kinbi boka don cimma burinki,duk irin zunubin da muke aikatawa bai ishekiba  saida kika hada Allah da wani,bakin cikina daya da bansan awane hali mi'at ta koma ma mahallicintaba,shin ta roki yafiyar ubangiji ko aa(dama haka rayuwa take,zamu dade muna aikata ba dede ba sai muce ai zamu tuba nan gaba,nan gaba yayshe,?itafa mutuwa bata sallama ahto"
Saurin mikewa tayi tajawo wayarta don taga kamar lokacin da ta kunnata sakon ummie yashigo,duba wayar tashigayi hannunta na kyarma,message din da mi'at ta turamatane tagani,haka ta bude tafara karantawa kamar haka.
*_Assalamu alaikum,momy hakika nasan ko baki duba message dinaba alokacin da na turamakishi to ina fatan bayan babu raina zaki duba,nasan cewa kina mai cike dajin haushina wanda ni bansan minayimakiba,harga Allah nanunamaki kauna fisabilillahi babu shamaki atsakaninmu,nasoki fiye da yadda nake son kaina,kuma da sonki acikin zuciyata da gangar jikina zan koma ma mahaliccina,momy akwai wani sirrin da nakeson fadamaki saide bansan tawane fuska zaki kalli wannan sakon nawaba amma ina fatan lokacin da sakona zai riskeki bana raye don bansan da wane ido zan kallekiba,farko inaso kiyi hakuri ki gafarceni akan laifin da bansan nayimakiba,hakika bazan iya jure ta rayyarkuba dakeda wacce nafi kauna  ba,am sorry am sorry dear,Ina sonki ina kaunarki amma duk da sob da nakemaki hakan bai kawar da zuciyataba izuwa ga wadda take muradi kuma nake fatan kasancewa tare da itaba,tabbas nasan zuciyata batayimun adalciba amma babu yadda na iya domin dazan iya hakura da tuni tun farkon ganinta na hakura da ita saide kasss nakasa,inajinta acikin raina da dukkanin ilahirin jikina,ina kishinta,ina kishin naga ta rabeki,kema kuma ina kishin naga kin rabeta amma hakan baya nufin wai bana kaunarki kuma nasan ban isa narabakuba sabida tare naganku,dan girman ubangiji momy ki mikamun wannan sakon zuciyar tawa zuwaga wadda nafi kauna aduk duniya watau MARYAM ABDULLAHI kice nayafemata dukkanin abinda tayimun duniya da lahira kuma kema kiyafemun nayafemaki duk da babu abinda kikamun tsakanina dake sai alkairi,sakona nakarshe inason kurike junanku da amana kiso anty meryy fiye da yadda kike sona idan har kikamun haka tabbas zanji dadi koda ace bana raye kiyimun wannan alfarmar,bissalam daga mai kaunarki akoda yaushe mai son ganin farin cikinki mi'atullahi_*😭

Wata irin kuka mufeeda tasaka batasan sadda takama merry tana girgizawaba"whyyyyyyyyy,maryam whyyyyyyyyy,mi mi'at tayimaki har haka maryam nayi dana sani ya Allah kayafemun kayafema mi'at don isar annabi muhammadu SAW"kuka takeyi tana mikama merry wayarta wai takaranta abinda ke ciki,hannu merry tasaka takarbi wayar tafara karantawa,itama kuka naga tabarke dashi cikin ban tausayi tace"kaicona kaicona tabbas mi'at bandace dakeba mufeeda itace wadda ta dace dake tunda har zan iya saka hannu wurin ganin kin rabu da farin cikinki ya Allah badon ni ba Allah kayafemun kayafema wannan baiwa taka"tarungume mufeeda suna kukan tare,saida sukayi mai isar su babu mai rarrashin kowa sana sukayi shiru.

"Kiyi hakuri,kiyi hakuri daughter bandace nacigaba da kasancewa acikin rayuwarkiba,tabbas kinyi gaskiya ni annobace tunda har zan iya ruguza rayuwarki ashe duk wanan abu da mi'at takeyi donni takeyins,na dauki tsanar duniya na dauramata,Allah sarki mufeedata kiyi hakuri bansan da wane baki zanbaki hakuriba amma namaki alkawari zanfita daga cikin rayuwarki don bana fatan wani abu yasake faruwa dake ta silata kinjiko"ta mike tana sharar hawaye ta dauki kayanta zata fita,saurin tsaida ita mufeeda tayi idanunta na fitar da hawaye tace"bazan iya barinkiba kodan cikar burin mi'at zanci gaba da zama dake ,kuma nayi alkawari zancigaba da kulawa dake kamar yadda mi'at ta bukata zancikamata wannan burin,duk abinda mi'at takeso nima ina sonsa koda kuwa babu ruwantane zancigaba da son abinda takeso saide bazanci gaba da rayuwar kaskanci damukeyiba dole musake rayuwa kodan mi'at tasamu rahamar ubangiji mommy mucanza kinji"

"Inshaallahu baby daga rana irinta yau bazan sake aikata lesbian ba nayi alkawari kuma ina fatan Allah yayafemana yakarbi tubanmu,sana inayima mi'at fatan samun rahamar ubangiji,zamu cigaba da yimata addu'a daganan har ranar da zamu koma ga mahallincinmu"
"Insha'Allahu daga yau zamu fara sabuwar rayuwa saide son danakemaki bazai canzaba dayardar Allah"

Sosai sukabama junansu baki har meery tayi sallana tatafi tabar mufeeda da jimami sosai aranta.


Bayan sati biyu da rasuwar mi'at kuma yayi dede da komawa makaranta,haka mufeeda tayi parking domin komawa skul shima saida zee tazo tatayata sana ta iya hada kayan nata don ita cewama tayi bazata komaba don zatana ganin kamar mi'at bata mutuba.

*******************
Alhamdulillah Masha'Allahu shekara kwana gashi su mufeeda yau sunyi candy inda suka zana jarabawarsu ta karshe kowace na sallama zasu wuce banda mufeeda da taketa kuka tanajin kamar yaune mi'at ta rasu,tanajin mutuwar tata tadawomata sabuwa,bama kamar da 7stars sukazo sunayimata bankwana suma sunata kuka luba ta rungume mufeeda tanata kuka tanacewa"Allah sarki da yanxu mi'at nanan itama tana kukan rabuwa dake"hakan bakaramin tadamata hankali yakarayiba dakyar akasamu aka shigar da ita cikin motar uncle nura dayake shi zai maidasu ita d zee.

Wata daya ciff da yin candyn su aka sakamata rana itada uncle nura,baki daya mufeeda ta canza tazama so silent,dama batada hayaniya amma sai rashin hayaniyar takaru sakamakon babban rashi da tayi,kullum zakaganta da wayarta ahannu tana kallon kyakkyawan hoton mi'at da tasaka a screen wallpaper  dinta wataranama har kuka takeyi idan tana kallon hoto,baki daya rayuwarta ta canza takoma abar tausayi kamar ba mufeeda tar gayun da kuka saniba,haka lokacin bikinta yaxo merry da zee sune kan gaba aka gudanar da hidimar biki duk da bawani event akayiba aka kai amarya dakinta sai muyi fatan Allahu yabasu zaman lafiya amin.




*_ALHAMDULILLAH MASHAALLAHU,DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN SAMMAI DA KASSAI DA YABANI DAMAR KAMMALA WANNAN LITTAFI NAWA,ALLAHU YASA MUDACE MUFI KARFIN ZUCIYOYINMU YARABAMU DA AIKIN DANA SANI AMIN,GODIYA MARAR ADADI GAREKU MUTANAN WATTAPAD HAKIKA NAGA KARA NAGA KAUNA SOSAI WALLAHI JIKI DUK MADARA INA GODIYAFA SOSAI ANA MUGUN TARE_*💔

Du hast das Ende der veröffentlichten Teile erreicht.

⏰ Letzte Aktualisierung: Jul 07, 2023 ⏰

Füge diese Geschichte zu deiner Bibliothek hinzu, um über neue Kapitel informiert zu werden!

RAYUWAR MAKARANTAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt