Free page (Chapter 10)

81 4 0
                                    

@fatymasardauna

*PART OF OUR DESTINY*

*(Daga yanzu zaku iya samun wannan book din a Arewabooks, musamman masu neman daga farko, yana nan akan arewabooks, and kar ku manta idan kunje kuyi following dina @fatymasardauna.)*

*Free page*
*Chapter 10*

Kallon hoton tabkeken hoton take yi batare da ta iya tantance ko wanene ajiki ba, saboda idanunta dake gane mata abubuwa dishi dishi.

"Zo muje kici abinci ko."
Amma dake rik'e da hannunta ta fad'a, tana me ci gaba da janta suka nufi dining table kaitsaye.
Akan d'aya daga cikin kujerun dining table din Aamman ta zaunar da ita.
Singapore noodles, da kuma Nutella milkshake ta had'a mata, tare da turo mata plate din gabanta.
Abincin ta k'urawa ido na d'an wani lokaci kafun ahankali ta janye kanta gefe, tare dayin alaman cewa bazata ci ba.
Kai Aamma dake kallonta ta girgiza tare da dubanta cikin tausasa murya tace.
"Haba Yacine kici ko kad'anne koda ba yawa kinji."
Kai ta girgiza alaman a'a, saboda bata jin zata iya cin komai.
Ganin haka yasa Aamma fara rarrashinta, daidai lokacin Aammabuwa ta k'araso, wanda fito war ta daga bedroom dinta kenan jaye da k'afafunta wanda suka kumbura sun tun, da gani kasan ciwo sukeyi mata.

"Sannu da fitowa, har k'afafun naki sun d'an sake kenan."

Aamma ta fad'a cikin kulawa, kasancewar d'azun ta lek'a side din Ammabuwan ta samu tana kwance k'afafunta sun kumbura har ta kasa tashi.

"Yo ko kafafuna basuyi sauki ba ai dolena ne na fito neman abunda zanci, domin bazan fasa fad'a ba, wallahi da raina bazan zauna ku kasheni da abinci marassa dad'i ba, na lura dudduniya babu wacce kuka tsana sama dani, saboda haka karyawa nazo yi, wancan abincin da kika kai min ni bazan ci shi ba ehe."
Cewar Ammabuwan adaidai lokacin da take hawowa kan d'an dakalin dinning table din, wanda isowar nata ne yasa idanunta sauk'a k'ir akan Yacine.

"Wannan kuma fa?"

Ta fad'a alokacin da take jan d'aya daga cikin kujerun dinning din ta zauna.

"Itace marar lafiyar da Emraan ya kawo."
Amma ta bata amsa atak'aice.

K'uri tayiwa yarinyar lokaci d'aya kuma ta k'ank'ance idanunta dake cikin medicated glass din dake k'arawa idanun nata k'arfin gani.

"Ikon Allah abu kamar Albino (zabiyya) wannan mutum ce ko aljana? karfa agarin jaye jayensa yaje ya kwaso mana aljana, abu sai kace d'an itaciyar nan cost (tsada), anya ma wannan marar lafiyar gaskiya ce kuwa, dan banga alamar rashin lafiyar atattare da ita ba."
Tayi maganar abayyane tane me lek'a kowacce gab'a dake jikin Yacine din, harda k'afafunta wai ko da zata ga k'ofato.

Amma kam idanu ta lumshe cike da takaicin maganan Ammabuwan, saboda tasan halin ta sarai, ita d'in irin mutanen nanne da duk abunda yazo bakinsu fad'i suke ba ruwansu, wannan yasa atausashe tace.
"Aljana kuma Ammabuwa, ai koma dai aljana ce ke ai kinfi k'arfinta, nan nake ji ko yaushe kina cewa babu wani aljani ko maye da ya isa shan ruwan jikin ki, and ma kince wai k'arya ne babu maita, ku Berber baku yarda dashi ba."

"K'warai kuwa mu bamu yarda da wannan abun ba, duk canfe canfe ne na Nigerians, balle ma wane mutum, kurwata kur, ni nan anbuga dani anbarni, dama ku nake jiyewa danni dai kam babu wani aljani ko aljanan da nake tsoro."

Ta k'are maganar tana me sake kafe Yacine din da idanunta dake cikin glass.
Saidai abunda bata sani ba, ita Yacine kamma duk way'annan sambatun da Ammabuwan keyi sam basa shiga kunnuwanta, atak'aice ma ji takeyi duniyar na juya mata, daga cikin zuciyarta take jin kamar ta ruga da gudu, saboda wani irin bugawa had'i da mummunar tsinkewar gaban dake neman gusar mata da nutsuwarta.

Amma kuwa jin abunda Ammabuwan tace ne yasa ta yin murmushi, batare kuma da tace komai ba, ta soma k'wala k'iran
"Jilde."
Jilde itace housemate din gidan, dake kula da wanke wanke, had'i da shara da kuma mopping.

PART OF OUR DESTINY Where stories live. Discover now