chapter 1

6 1 0
                                    

KE CE SANADIN*
        [|Rayuwa ta|]

     Mallakar matar dan aljannah ce 🖌️

MIKIYA WRITER'S ASSO.......📚

Na sadaukar da littafin nan ga baki dayan sa gare mr imran[ dear]

Bismillahir rahamanir rahim

SHAFI NA ƊAYA

gari ne ya ɗau duhu sosai hadari ne ya hadu sosai, gari na ruwa kowa na sauri sauri sutafi gida, amma narasa yazan yi da rayuwa ta daga wannan sai wannan' rashin iyaye baiba, inda da iyaye na taya zan zauna har yanzu a waje nasan na koma gida batare da nakai ma 'innar abu ƙudi ba nasan hanani kwana zatai gida gashi yau ba mazan.ma a gari, rashin ta kamai mai abinda zanba na kama hanyar gida,, ina isa gida nai sallama duk zaune suke a tsa kar gida amma ba wanda  ya amsa sallama ta" innar abu ce tace ke har kin dawo"?

A firgice na kalle ta, nace nadawo..
   Miƙo min kuɗin gasu "abu nan ko wacce cikin su ta dubu biyar, naki nake jira na haɗa guɗa"!

Nace "innar abu, wallahi yau ba mutane da yawa kinga Ni ban saba ba"...

            Ashar ta dan nomin tare da miƙewa tace ashe kam yau, zaki ci uban ki mai kashin tsiya.

Nidai a rayuwata na tsani naji an ai bata min iyaye, turo baki tai tace to kiyi hakuri..

       Tasowa "innar abu tai ta zo gabana cimin ƙwala tai tare da cemin ban ƙudi?
   Cire mata hannun nai ariga ta nace, "innar abu kinsan Allah bansamo ba..... sallama akai wai Sarah tazo inji Alhaji Nura"!

Murmushi "innar abu tai tace, ki maza kitafi ki samo mana wani abun ko yau baki da abinci".

Kallan ta ne kamar bazan fita, sai dai kuma na fita dan tana iya hanani kwanan gidan' ina fita murmushi Alhaji nura yayi tare da faɗin my baby kin fito?

  Murguɗa masa baki nai nace "wai malam Lafiya dai tara ko bashi"? Nace bani yi dai amma kana cemin akan me a Wane dalili?

"Innar abu ce ta leƙo tace "Sarah rashin kunya kike masa"?
    Alhaji nura yace ƙyale ta "inna kinsan yarinyar akwai yarinya atare da Ita"..
   
    Kallan sa nai tare da masa harara, innar abu dai komawa gida tai' yace min mu shiga mota na baki tsara bar ki ko.
   
   
    "Malam idan zaka Ban mi ƙomin na tafi gida dare nayi"..... murmushi yamin yace haba yarinya Ni zaki ma wayau ne? Kinsan dai halin "innar abu dai in baki so natafi.
   
    Tunawa nai da maganar ta nai shahada na shiga, badan raina ya soba' shafani yake amma ji nake kamar wuta yake samun a jiki na, ba yadda na'iya haka na hakura kusan minti 30 yana abu daya dubu goma ce yaban tare da kaza sai ruwan roba guda biyu lemu ma roba uku ansa nai ko godiya na fita daga motar' gida nafada tare da sallama "abu ce ke kwara amai abun gwanin tausai, sannu na mata tare da miƙa ma, innar abu baƙar ledar ƙudina kuma boye wanai a cikin zani kallo na tai tace ina kuɗin su ke"?

Haba "innar abu Ni bai bai da ƙudi ba, ga abun da yabani nan fa"!
      Da kike baza ki fita ba, da kinma arziki ƙulli ko, nidai ina jinta ɗakina nashige ƙudin danake tarawa nafiddo Allah ya taimaka ma "innar abu bata san da suba, irgawa nai naga dubu hamsin ne so nake su kai min ɗari nagudu natafi garin su mama na nemi dangin ta, ƙwalla ce ta zubo min sharewa bai tare da tsine ma innar abu tana san sani wata hanya ta daban....... kwanciya nai kan yar katifa ta ina tunanin Rayuwa!

*Tuna baya*

Malam Musa haiffan garin minna ne a wata anguwa da ake kira bagari, inda yake zaune da matar sa Maryam "Maryam macece mai hakuri ga ladabi ga mijinta bata san abun da zai bata masa rai, shekarar su 7 basu samu haihuwa ba inda yan uwan malam Musa ke tsangwamarta, wulakancin yau da ban na jibi daban haka ake rayuwa da ɗadi ba daɗi,, yayar sa ce tace sai ya kara Aure da ƙyar ya amince gani suke Maryam ta mallake masu ɗan'uwa ansha biki sai yada ta haibaci da suke an auro mai haihuwa ba irinta ba juya, ita dai bai wuce tai murmushi kawai ta ƙyale su"...

Innar abu tana da Wata tara ta sumbulo yar ta macce zainab [abu] tana da shekara biyu takara haihuwar nasiba, tunda ga nan haihuwa ta tsaya Mata.

Maryam wata rana ta tashi da zazzabin mai zapi, gashi ranar girkinta ne bata samu tayi ba"innar abu tace dan taga bata da yara ne dole ta ki daura girki, yinwa ta kashe mata yara kenan"!
        Ɗan Allah kiyi hakuri bani da lafiya ne...

Can maki dai, aniyar ki ta biki munafika bakin ciki sai dai ya kashe ki wallahi.

   haka "malam musa  ya dawo ya tarda ba'ai abinci ba, sai fada taka zata kashe mata yara ne dan taga ita juya ce dakin nata ya shiga tare da kiran sunan ta ganin ta yai kwance cikin amai ko hannu bata iya dagawa, da sauri ya isa gare ta dagata yayi yace maryam lafiy"?

malam wallahi zazzabine ke damuna, ga amai dan allah kayi hakuri bani da karfin da zan daura mana abinci.......haba "maryam ana takai wake ta kaya, mai kike so kici?

murmushi nai nace" ni ba'abinda nake bukata illah dan wake"!

bari nazo, fitowa yai gun "innar abu [ rabi] yace Maryam fa bata da lafiya ki mana dan wake mana"..

Kallan uku saura kwata namasa, nace Malam idan ta asirce ka ni nafi karfin asirin ta wallahi' saboda taga bata da yara a cikin gidan dole zata make hannu ta ce maka bata Lafiya mana.

     Kallon ta na tsayayi nace; ke dakata "rabi miye abin gorin haihuwa ne Allah ne fa ke badawa kada ki manta da haka"!

A haka rayuwa tai ta tafiya daɗi ba daɗi, har cikin Maryam ya shiga watan haihuwa' wata rana malam ya fita naƙuda ta tashi tanemi taimakon innar abu tai mursisi tun da tashigo taga naƙudar nake ta ƙyaleni, yana dawowa malam yayi sallama kukan jariri ya masa mara ba da zuwa, da gudu ya shigo ya taimaka min ya yanke cibi' gyara gun Dana ɓata mukai atare ɗaura ya nayo zuwa nai na kwanta ina hutawa sannan malam ya dinga kiran yan uwa yana faɗa masu an haihu ranar suna yarinya taci sunan Sarah, alhamdulilahi muna samun kulawa ta kowane ɓangare!

Innar abu ce taje gun boka, boka isbili so nake ka mallaka mun "malam a hannu na sai yadda bai dashi"....

Kinzo wajan amma kisani aljani jibilli, sai ya ku sance ki, to ai ba komi indai bukata ta zata biya!

Hahahaha hahahaha hahahaha yake tayi tashi  muje na miƙa ki gun sa, tashi nai dan jina nake kamar ina aljannah { kai karya ne innar abu daina haɗa kanki da aljannah ato} bayan minti 30; muka fito wani farin magani ya ban dazan shafe jikina duka da shi, da wanda zan zuba masa a abunci' haka nafito ina murna ta aikata hakan ba dadewa "maryam tarasu lokacin sarah na da shekara 5 a duniya, tayi shekara daya da rasuwa malam musa yarasu wannan shine takaitaccen tarihi na"....

   back to story

tunda natashi naji kaina na ciwo, aikin da nasaba nayi duk nagama ruwan koko na daura nafita chamist dan siyan magani, shagon nura extra nasiya na ishiri ina zuwa ruwan koko ya tafasa damawa nai na zuba shi a botikin da ake zubawa' komawa nai daki na dauko kofina na dibi nawa kokon nasha na sha magani na, komawa nai na kwanta barci ne ya kwashe ni aman abu ne ya tashe daga barci na fitowa nai nace "anty abu, kije asibiti mana"!

Ke dakata Ni tsaran wasanki ce da zaki tsomomin baki, kamar an datsama kare ciyawa..

Ɗan Allah kiyi hakuri, ina sha Allah bazan sake ba.

Kima yi banza gara, innar abu ce ta fito tace ke" Sarah wanki ne na hada kizo kimin"!

To bari naje islamiyya idan na dawo sai nayi.....

Kallan uku saura kwata ta watsamin, saboda kin rainani ko niba uwarki bace to bari kiji wallahi ba inda zaki sai kinmin wankin nan!

  Cire hijabi na nai' Kayan na kwaso na cigaba da yi tun 8:am bangama sai bayan la'asar anyi abinci an hanani, ƙudina na dauka natafi yar yara naci masa na koshi wata bishiya nasamu na kwanta gun iska mai daɗi tana ratsani tunanin gudawa ne ya zomin araina sai dai idan nagudu ina zani? Nakasa ba kaina amsa haka na dau kusan awa ina hutawa gida nashi ga sallama nai ba wanda ya ansamun inda sabo na saba da irin haka "innar abu bata nan sai nasiba tace,, Sarah inna tace in kin dawo ki daura towo"...

To "nasiba tabaki ƙudin cefane ne"?
     Ehh duk nasiyo kafin ta tafi.

*Inna*

Zaune take ɗakin kwarton ta tace haba, ishulle taya kullum Ni zan rinƙa zarya a gunka!
    Kallon ta ishulle yayi kamar bazai ce komi ba ya ce in fa baki so sai a hakura da hutawar.
   
   
    Fari tai da ido ta matsa jikinsa, tana shafa kanshi Kamar wani jariri tace ishulle ban san kullum ina fita kada a cemin karu.....bata idasa ba yasa hannu ya rufe mata baƙi suka faɗa masha'ar su........

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 23, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

labari ne wanda ya kunshi abubuwa dayawa nishadi bandariya fadakarwaWhere stories live. Discover now