☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆
𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲
𝗣𝗮𝗴𝗲 2️⃣
Ta aje plate din hannunta da sauri ta zari tissue ta goge bakinta.
“Amma na tafi kar na yi latti”
Amma dake kokarin jefa tawul a ruwa ta ce
“Kya ji da shi, kullum ke ce uwar yan latti sai an jiraki, ga kokari ga buga latti”
Hurriya ta dauki jakarta ta makaranta da sauri ta goya tare da daukar lunch box dinta ta fice daga falon da gudu, kamar zata fadi haka ta isa bangaren Appanta sai haki take kamar wadda aka yi yakin duniya tare da ita. Hannu ta mika jikin window falon kamar yadda sauran yan mata sa'aninta da wandanda suka girmeta suke mika na su hannu suna karbar karamin hollandia da chocolate da yake raba musu, tana son karba yan'uwanta na tureta tana yin baya har sai da suka gama karba sannan ta samu karba daga gurin mahaifinta, kyautar wani abun ci da ko abun sha a kowace safiyar week days wani abu ne da ya sabawa yaransa da shi tun suna kanana.
“Na gode Appana”
Ta fada tana murmushi jindadi, shi ma murmushin yayi yana kallon kyakkyawar yarsa, mai yawan yi masa godiya da nuna masa jindadinta a duk lokacin da yayi musu kyauta komai kankantar kyautar domin haka mahaifiyarta Amma ta koyar da ita, kusan ita ce karama a cikin yayansa mata a cikin maza kuma kanenta Hamad ne karami ƴaƴansa na jini amman ya fi sauran yayansa godiya da yabawa idan yayi musu abu.
“Allah ya miki albarka Hurriya, ga ladabi ga basira”
Ta yi yar siririyar dariya mai sauti.
“Appa haka Uncle dinmu yake cewa, har da cewa yayi wai akwai wata gasar da zan sake shiga”
“Da kyau ni ma ya fada min haka, kuma yace wannan gasar ma mai tsoka ce, suna kyautata zaton idan kika yi ta daya za su dauki nauyin karatunki domin haka suke yi ma duk wadda yayi na daya, ni kuma na kara musu da cewa ko da ba su fitar da ke ba, zarar kin kallama makarantar da kike yanzu zan fitar da ke waje ki yi karatu mai kyau, duk kuwa da bana sha'awar fitar da ƴaƴa mata waje yin karatu amman ke zan fara akanki”
Ba shiri Hurriya ta bude baki tana mamakin jin furucin mahaifinta.
“Appa da gaske?”
“Da girmana zan yi karya?”
Ta saki chocolate din da hollandia ta rufe baki tana zaro ido kamar zai fado. Sai kuma ta daka tsalle ta dire.
“Appa i love you i can't wait”
“Ki dage da karatu Allah ya taimaka ina alfahari da ke, Allah ya miki albarka”
Ya fada yana murmushi yana nuna mata alamar lokaci a hannunsa da babu agogo, sai ta duka ta dauki abun da ta zubar ta.
“Ameen ina sonka Appana, na tafi sai na dawo”
“Allah ya kiyaye,”
Ta amsa da Ameen already ta sauka entrance din tana hadawa da gudu domin yan'uwanta sun kusa isa gurin bus din dake kaisu makaranta ta maido su. Tana daf da isa ta ji an fisge chocolate din dake hannunta kamin ta juyo aka fisge madarar hollandia din dake dayan hannunta. Suna hada ido ta bata fuska ta buga kafa kasa, shi kuma ya saka dariya yana kokarin bude ledar chocolate din.
“Yaya Yassar dan Allah ka ba ni”
“Wallahi ba zan baki ba”
Ya fada kai tsaye yana mata dariyar keta, juyawa ta yi cikin yanayin damuwa ta koma bangaren Appanta wannan karon bata tsaya gurin windows din ba ta murda kofar falonsa ta shiga, sanin talkamin makaranta ne daure a kafarta sai ta fadi kasa tana rarrafe dan kar ta taka masa carpet.
YOU ARE READING
H U R I Y Y A
FanfictionWata rayuwa ce zan taɓa ta Hausawa, wani ɓangare na ƙabulan da yara suke fuskanta a gidan iyayensu, tun farko tashi har girma, wani abu ne da nake ta hangowa kuma na daɗe da ƙishin son rubutawa. ••• ••• H U R I Y Y A -Labari ne mai ban tausayi da...