Shimfi'da
*Sadaukawa ga iyayena guda hudu*
*Alhaji Muhd Tukur*
*Haj Fatima ladi Ali*
*Alhaji Dahiru Ali*
*Haj Maryam Hamisu Kano*
*Allah ya ji'kanku da Rahma ya baku aljannar firdausi*.*Fatan alheri ga Mijina*
*(M.I. Nashe)*.*Jinjina ga shugaban kungiyar Lafazi writers*
*Sadik Abubakar*
*Na gode da kokarinka akan rubutuna*.*Assalamu alaikum sister's! Barkanmu da sake ha'duwa a cikin sabon littafina.*
*Hakika na yabawa kaunar da kuka nuna mini akan littafin *Halin Yau*. *Ba abin da zance muku sai dai fatan Ubangiji ya saka muku da mafificin alheri*.
*Ina fatan zaku bibiyi wannan labarin sannu a hankali dan jin da wanne sa'kon ya zo.*
*Ina addu'ar Allah ya bani ikon rubuta dai dai, ya hana ni rubuta barna*.*BISMILLA HIR RAHMANIR RAHIM*
*Shimfi'da*
*Farko*
Harabar falo ya biyo ni yana fa'din "zo ki ji Halah! Saurare ni mana, sai yaushe za ki yarda da ni? Ai na dauka mun wuce wannan tashin hankalin? na riga na fahimta, na kuma gane bankaura nake yi, ke 'din ce farincikina, ke ce duniyata!"
Ya tsahirta da nufin ko zan tanka masa, amma sai na tsuke bakina tamkar gini yake ba yi wa magana.
Ya nisa tare da fesar da iska sannan ya ci gaba da cewa, "Ki kalli irin yadda Allah Ya juya al'amarinsa mana komai ya kubuce mini, da kaina na dinga 'karyata kalamaina. Bai kamata ki ci gaba da nuna 'bacin rai ba, tunda Ubangijinki ya yi kishinki, kar fa ki bari ni ma Ya yi kishina, tunda ba a miki sassauci wurin yi mini 'kwangen biyayya ba."
Na yi 'kasa da kaina ina jin hawayen takaici na neman kwace mini.
Ba komai ke sani jin takaici ba, sai irin yadda ba ni da yar'uwa shakikiya mace. Wacce duk runtsi ba za ta 'ki yi mini adalci ba, wacce na rik'e tamkar cikinmu guda ta nuna mini wata kusar ta fi wata, ta hanyar fifita farincikin 'dan uwanta a kan nawa, duk kuwa da tana sane da irin zaman da na yi da shi, asalima ita ce kan gaba wurin fa'din ha'kurina ya yi yawa, son da nake yi masa ya wuce hankali, ita ba za ta dauki wulakanci namiji irin yadda nake dauka ba.Amma da ya fasa kwalbar ha'kurina! Sai t ta shure dukkan ba'kin cikin da na hadiya a hannunsa, ta bari idonta ya rufe, ta 'ki yi mini kara, duk da ta san ita ce 'yar uwa mafi kusanci a gare ni.
Ya sake nanu'kata, yana cewa, "Ni na san ke mai yawan yi mini afuwa ce, wannan taurin zuciyar ba taki ba ce, ba kuma ta dace da ke ba. Kin yi hakuri da ni, na zalunce ki, na shayar da ke gubar ba'kin ciki, na azabtar da ke, na wulakanta ki. Amma don Allah ki ba ni damar da zan gyara na yarda na yi laifi, ina kuma son na gyara, amma kin rufe mini 'kofofofin afuwa.
Hawayen idona ya 'balle mini, cikin rishin kuka na ce, "Sau nawa kana yin irin wannan tuban na muzuru? sau nawa ake danne ni saboda kai?
Shin laifi ne don na zo a jinsin mata masu 'kiba, na kuma zama uwar 'ya'ya mata?"
Kuka ya 'kwace mini kwarai da gaske.Cikin rarrashi tamkar ba ta'kadiri irin Gudale ba, Ya ce, "Kowa ya shaida wannan nadamar tawa har zuciyata ce, sannan ai yanzu bisa sharadin da aka gindaya mini za mu zauna, ni na sani sakayya ce Ubangiji ya yi a tsakaninmu, aka juyar da al'amarinmu ta yadda ban yi zato ba, ina sake rokon ki kar ki bari rashin kirkina, yasa ki yi watsi da kyawawan dabi'unki na ha'kuri da sassauci, Ubangiji da kansa ya ce, "Fa sabir sabaran Jamila." Wato ku yi hakuri, hakuri mai kyau. Ya sake cewa, "A yi wa masu hakuri bushara."
Na zuba masa ido tar ina mamakin ashe ya san hakuri dabi'a ce mai kyau? A duk tsayin zamana da shi, kullum na bashi ha'kuri yana ba ni amsa da cewa bai san shi ba, domin shi ba zai yi wani ha'kuri ya cutu ba, ba kuma zai sassauta ba, sai ya yi mini hukuncin da ya yi nufin yi koda kuwa ban yi komai ba. Sai don kawai ya jefa ni cikin 'kunci da bacin rai.
Amma yanzu saboda rashin ta ido ya karkace baki yana fa'din falalar ha'kuri, domin shi yake so a yi wa uzurin ha'kurin.
Na hasaso irin tsananin da nake fuskanta ta bangaren mahaifiyarsa, take na fashe da kuka mai sauti domin na sani ba abin da zan yi wa Umma ta yi mini adalci. Kishin da take yi da mahaifiyata ne ta tattare ta dawo da shi kaina.