1&2.
*Free page.**Tushe*
Asalin kakanmu Alhaji Zubairu Lawal Moriki, 'dan asalin 'kauyen Moriki ta cikin 'karamar hukumar Zurmin
jahar Zamfara ne. Bahaushe ne, kuma Bafulatani, domin mahaifiyarsa Bafulatanar daji ce, kyakkawan dattijo fari tas. Ya taso cikin tsari da 'ka'idar tarbiyar Bahaushen Arewa mai tsananin ri'ko da dokokin shari'ar Islama.
Fataucin dabbobi ne ya kawo shi garin Kano har ta zame masa tamkar gida. Domin kuwa sannu a hankali ya kwaso iyalinsa suka dawo kano gaba'daya. 'Ya'ya biyar mai dakinsa Maimuna (Adda) ta haifa masa, duk da sun binne wasu da dama a dalilin tana wabi.
Hajiya Hafsatu ita ce babba (Yaya ta 'Kwalli) ba ta ta'ba haihuwa ba, sai dai kuma yan'uwan nata ba su ta'ba bari ta ga gurbin rashin haihuwa ba. Sai dai kawai motsawar da zuciya za ta yi idan sha'awar ganin jininka ta motsa. amma ba don kukan wani abu ba, domin 'ya'ya biyu 'yan uwanta suka bata ta goya, ta kuma aurar. Dukkan abin da ya shafi yaran kuwa yana hannunta. Ramla da Ashir. Mace mai zafi idan aka tabo ta, mai son dinke barakar zumunci, duk inda ta ga zumunci zai samu tawaya yanzunan za ta yi dukkan mai yiwuwa ta 'dinke shi.Sai Alhaji Abubakar Moriki (Abba) shi ne na biyu, dattijon arziki mai tsananin ri'ko da ka'idojin shari'a, masoyin zumunci da kyautata shi. Dukkan karatunsa ya yi ne a bangaren addini, a 'kasar Sudan ya yi digirinsa na farko a fannin sanin ilimin Hadisai. (Hadith Science) Daga nan ya wucewa 'kasar Masar ya sake zurfafa iliminsa a kan sanin a fannin Shari'a da rabon gado. Dukkan karatun tallafi ne na gwamnatin tarayyar Najeriya.
Daga nan kuma sai ya fa'da harkar kasuwaancin safarar zobo da 'karo a tsakanin 'kasashen Africa. Sosai ya samu daukaka a harkar, ba 'karamin nasibi yake samu ba, domin idan ana lissafa attajirai, babu shakka za a saka Alhaji Abubakar Moriki.
Matarsa 'daya Hajiya Saude (Umma). 'Yar asalin garin Yola ta jahar Adamawa ce.
Kyakkawar mace fara 'kal mai cikakken diri, mai yalwataccen gashi, sai dai gajeriya ce.
Mace ce mai izza da jin 'kai, ta tsani wani ya rabe su, kasancewar mijinta shi ne garkuwa a danginsa.'Ya'ya shida Ubangiji ya azurta su, biyar 'din farko dukkansu mata ne kyawawan gaske domin dukkansu ita suka biyo, suka sami tsayin mahaifinsu duk da mijin nata ba baya ba ne wurin kyakkawar sifa, sai dai ko kusa ba a hada kyaun mace da namiji, sannan farinta da dogon gashinta baki sidik sun shahara, sai ta zamo tamkar Balarabiya. Haka 'ya'yanta suke farare dogaye, masu gashi, duk irin yadda Ubangiji Ya azurta ta da samun wa'dannan kyawawan yaran kuma masu lafiya, ita ba ta gode ba, domin ba abin da take so irin ta haifi namiji. Hafsat ce babba, wacce ya yi wa yayarsu magajiya, sai Maimuna (Ummu) mai sunan kakarmu, sai Juwairiya, Ramla, Sakina, sai autanta da ya ci sunan sahabin Ma'aiki Abubakar ake ce masa Sadik kasancewar sunan Abbban ke nan, ita kuma ta ce Gudale.
Sai Hajiya Binta Moriki (Maman Kebbi) da take aure a Kebbi tana da 'ya'ya uku Shafa'atu, Adnan da Ashir.
Sai Alhaji Ssni Moriki (Baban Gusau) da ya kasance dan kasauwa mai sayar da suturu, a cikin babbar kasuwar Gusau, a can kuma yake zaune da iyalinsa. Mutum mai tsauri da fe'de gaskiya, komai 'dacinta, marar daukar wargi. Matarsa 'daya da yara biyar, Fatima, Abubakar, Maimunatu (Ummj), Abbas, da Farisa. Abbas kuma yana tare da mu, tun daga karatun sakandire da ya yi a Science Dawakin Kudu da su Ya Sadik shike nan ya zama dan Kano, duk sa'anni ne da su Ya Al'amin, Kuma duk Gudale ne 'karaminsu.
Mahaifina Alh Ibrahim Moriki (Baban Yara) shi ne autansu, kusan Alhaji Abubakar shi ya yi masa komai tunda ga kan hidimar makaranta, har ya zuwa aure. Ma'aikaci ne a hukumar ilimin bai 'Daya. Mahaifiyata Safiyya (Mama) 'yar Kano ce, ta fito daga unguwar Magashi, cikin babbar zuri'a, ina nufin masu haula da yawa ba wai ku'di ba. Matsakaicin kyau ne da ita, sannan tana da dan jiki, da manyan idanuwa dara-dara, sannan wankan tarwada ce, yayin da Baba ya kasance fari tas! Lokacin da aka auro Mamanmu, Umma tana goyon Ramla ne, sosai suke zaman lafiya, domin Mama tana gama gyara bangarenta, matu'kar mijinta ya fita to kuwa za ta rufe ta tafi wurin Umma saboda a gidansu na gado suke zaune wanda Abba ya fadada shi, ya zamanantar da shi, a cikin unguwar Hausawa 'Yan-Babura.