Chapter 6

4 0 0
                                    

*AMEERA & ADAM*
            *6*

         By S-REZA✍️

          

                 *PAGE 6️⃣*
....Da sauri Adam ya riƙe Amera da ke ƙoƙarin yin kisa. "Lafiya kike kuwa Ameera? Baki da hankali ne idan kika kashe musu yarinya fa, daga kawo yarinya har zaki naimi hallaka ta. Adam ya faɗa ya na ɗago Haura dake durƙushe ta na kuka. Ita kuwa Ameera dama kaɗan ta ke jira, kafin Adam ya ƙara sa har ta yi tsalle ta shiga tsakaninsu da Haura. Cike da gadara da nuna isa ta ce "Honey wallahi wannan yarinyar bazata zauna a cikin gidannan ba domin ban yarda da ita ba. Cike da mamaki ya ce "Me ya faru? Ameera ta fara magana cikin ɗacin rai da takaici ta na jin yau sai ta nakasa wannan yarinyar. "Daga cewa ta dafa min indomin ɗazu wallahi ko minti uku ba'ayi ba wai har ta dafa, sannan yanzu na ce ta karanta min littafin da na siya ɗazu wai daga bata waya sai rubutun ya koma wani yare da ban? Ameera ta ƙara sa maganar da wata iriyar murya. Cike da tsoro Adam ya ce "Ina indomin da littafin? Sai a lokacin suka kalli gurin da kwanon abincin ya ke, amma wayan babu abincin a cikin kwanan. Cike da sabon tashin hankali Amera ta kalli Haura ta kalli kwanan abinci ganin da gaske babu komai a ciki, ita dai tasan cokali uku tayi kawai a abincin. "Ina abincin ya ke? Ameera ta tambayi Haura cike da dakiwa alamun babu wasa. Cikin muryar kuka Haura ta ce "Ba ke ce kika cin ye ba ɗazu. Take Ameera ta lailayo wani ƙatoton zagi ta makawa Haura haɗi da faɗin "Ubanki ne ya ce miki nine na cinye? Ina ce yanzu kenan na fara cin abincin kika mayar min da littafin wani abu da ban, shine yanzu zakice ni ce na cinye.

"Kunga yanzu dai duk ku dagata" Adam ya faɗa bayan ya gama jin duk abinda kowa ya ce. Sosai ya ke ta nazarin yarinyar ganin tana yin komai a nutse ne yasa bai ta da hankalinsa ba. "Yanzu ina wayar da rubutun ya koma wani iri ɗin? Da sauri Ameera ta miƙa masa wayar ta na faɗin "Wallahi ko rubutun aljannu ma iyaka kenan. Adam na ƙarɓa ya ce "To ai ga shi rubutun Hausa ne ba na wani abun ba. Ya faɗa yana miƙa mata wayar. Cike da tsoro ta ƙarɓa tana kallon komai na Hausa a cikin littafin. Adam ya ce "Duk kinzo kin tashi hankalin mutane bayan a she kece ma baki duba ba da kyau ba, ni wallahi na rasa gane miki Honey kullum sai sauyawa kike yi kamar wata wa hainiya, please dan Allah ki bari ku zauna lafiya da wannan rayinyar bata da wata matsala.

Adam na gama faɗa ya kama hannun Haura ya tafi da ita ɗakinta ya na faɗa mata cewar sai ta yi haƙuri da Ameera wannan cikin ne duk ya mai data haka, da zarar ta sauƙa in sha Allah komai zai dawo daidai. Ita dai Haura sai sun kuyar da kai take yi ta na sauraron sa har suka iso ciki ɗakin nata. Kallonta ya yi da kyau daga ƙasa har sama yana tuno ganin da yayi mata tsirara. "Gobe idan Allah ya kaimu za'a sayo miki kayan sawa kin ji? Ba tare da tayi magana ba ta ɗaga masa kai. Juyawa ya yi ya bar ɗakin ya nufi gurin Ameera.

Tun daga nesa ya hango ta ta na zazzagawa a cikin palon ta je nan ta dawo nan , kallo ɗaya ya mata ya nufi ɗakinsa bai ko bi ta kantaba. Ya na shiga ya shiga cire kayan jikinsa ya na cigaba da tunanin lamarin Ameera da Haura. Sai kuma ya ɗan saki murmushi yana jin anya kuwa Ameera bata fara ganin biyu-biyu ba kuwa. Ya na cikin wankan yaji an banko ƙofar da ƙarfi kamar za'a ɓalla ta. Tsaye yayi yana kallon ta itama ta na kallonsa cikin ido, tsabar masifa da ke cikinta har wani jaa fuskarta ta yi, shi kansa Adam sai da ya tsorata da ganin fuskar tata. Cikin tsawa da ɗaga murya Ameera ta ce "A ina ka samo wannan yarinyar!? Adam ya haɗiye wani yawu haɗe da ruwa a lokaci ɗaya sai ji kake maƙot. Tsabar rike cewa ma ya kasa cewa komai jin yayi shiru ne yasa ta sake daka masa wata tsawar kamar wata uwar sa. "Na ce a ina ka samo wannan tsinaninyar yarinyar da har ina magana zaka riƙe hannunta ku tafi ka barni a tsaye? Ta ƙara sa tana nuna masa wuƙar da ta ɓoye a bayanta tun ɗazu. Adam ya ce.

"Am am kinga honey dan Allah a jiye wuƙar muyi magana please... Kafin ya ƙara sa ta kai masa yanka yayi saurin sun kuyawa yana zaro ido ganin fa da gaske ta ke yi. "Honey please tsaya kiji wallahi ba abun da kike tunani ba"...Nan ma bai ƙara sa ba ta ƙara kai masa wani yankan ta na kuka. Ganin haka yasa Adam saurin riƙe hannunta mai wuƙar yana jawo ta jikin sa. Ita kuwa Ameera ganin haka yasa ta fara ƙoƙarin ƙwacewa tana so taga ta luma masa yasan da gaske take. Da ƙarfi Adam yake so ya ƙwace wuƙar amma saboda ba riƙon wasa tai masa ba yasa ya kasa ƙwacewa kuma idan ya dage wani zaiji ciwo a cikin su, hakan yasa ya jawo ta jikin ƙofar ya buɗe yayi waje a guje, itama tabi bayan sa cikin gudu.

AMEERA ADAM Where stories live. Discover now