Page 1

90 2 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
   *AKWAI DALILI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

       Na
*Jiddah S Mapi*

*Chapter 1*

              ~Hadari ne ya haɗu sosai, sararin samaniya ya koma baki ƙirin, tsawa haɗe da walƙiya akeyi a lokaci ɗaya, iska me karfi yana kaɗawa kamar zai kada bishiyoyi, mutane sun samu waje sun raɓe domin ba karamin tsawa akeyi ba, ruwa ne ya fara saukowa kamar da bakin kwarya, gari yayi shiru sai sautin saukan ruwan sama akeji, titi babu kowo, wata yarinya na hango daga can nesa tana tafiya ruwan yana dukanta, duk tsawan da akeyi bata tsorata ta samu waje ta ɓuya ba, taja saman hijabinta ta rufe fuskanta baka iya ganin fuskarta daga inda kake, a hankali take tafiya kamar batajin ana ruwan, hannunta rike da katon leda wanda take karewa tana ɓoyewa cikin hijabinta, mutane sai kallonta suke suna mamaki, wani mota bakin mota me ɗauke da bakin glass yazo da mugun gudu, ko kaɗan bataji karan motan ba har yazo dab da ita, me motan cikin hasala yaji kamar ya bigeta, tun daga nesa yake danna mata hon bataji, tafiya ma take kamar itace ta shimfiɗa kwaltan, sharan kwana yayi ya biyo ta gabanta da mugun speed yazo kamar zai ɗauke ta, da sauri ta wurgar da ledan hannunta, a firgice ta tsaya ta ɗaura hannayenta a kunnenta tana runtse ido da karfi, tsayawa yayi yana kallonta har yanzu hijabinta ya rufe mata fuska, zuwa yanzu ruwa ya fara ɗaukewa sai yayyafi ake kaɗan kaɗan, ganin ya tsaya bai bigeta ba ta fara buɗe ido a hankali, sauke glass na motan yayi yana kallonta from head to toe, kanta a kasa tana kallon ledan daya faɗi a cikin ruwa ya lalace ya koma kalan taɓo, kayan dake ciki fari ne sal, gashi sun zubo sun koma baki, idanu ta waro kana ganinta zakasan a tsorace take, yana daga zaune a motan yace "ke mahaukaciyar inace? ko makauniya ce ke? bakya gani ne? yanzu dana bigeki zakice an miki rashin adalci"
a hankali ta ɗago kanta jin abinda yake gaya mata, hannu tasa ta ɗaga hijabin nata wanda ya rufe mata fuska, madalla da wanda ya halicci wannan kyakkyawar halittan, kyakkyawa ce ajin karshe, farace tass har ta fara komawa yellow, ɗan karamin baki take dashi da manyan idanu, karan hancinta kamar an zana, idanunta su ake cewa sexy eye's domin har wani oily oily sukeyi, gashi idanunta zara-zara kamar wacce tasa na kanti, ido kawai ta zuba mishi tana kallonshi, tsaki yaja "kina ganin idan na kalleki kyaunki zaisa na fasa fadan abinda nayi niya?"
shima ba karamin kyakkyawa bane domin da kaɗan ma zata fishi fari "kinci sa'a da saina bigeki wallahi"
bakinta ne yake motsi a hankali saide har yanzu batayi magana ba, kallon kayan ta kumayi sannan ta kalleshi, wasu zafafan hawaye tasa hannu ta share, a hankali ta durkusa kasa ta maida kayan cikin ledan, ko kallonshi bata kara yiba ta kama hanyan tafiya, zuciyarta kamar ansa wuta haka takeji, tasan abinda zai faru idan taje gida, tsaki yaja ganin ta raina mishi hankali, motan ya kunna kana yazo ta gefenta saida zai wuce ya watsa mata ruwan dake gefen kwalta,  daga kanta har zuwa rafin kafarta saida ya jiƙe da ruwan, jikinta ya fara ɓari tasa hannu ta share ruwan daya ɓata mata fuska, ta madubi yake kallonta har ya bar wajen, haushin da yaji shine rashin tanka mishi da tayi, kenan ma ba zata bada hakuri ba? hakan ne yasa ya kara watsa mata ruwan caɓi kuma har yanzu batayi magana ba.
tana tafiya tana kuka har ta shiga wani unguwa marar kyau, gashi dai kana gani kasan unguwan na talakawa ne sosai, kofan wani gida ta tsaya tana share hawaye, saida ta saita kanta kafin tayi sallama tana ɗan lekawa, babu wanda ya amsa kuma suna cikin gida, shiga tayi ta tsaya a gefe tayi shiru ta rasa ta inda zata fara, matar dake zaune akan tabarma ta zabga mata harara tace "to ina kayan? kin wani tsaya akan mutane"
jikinta na rawa ta mika mata, ganin ledan a jiƙe tace "lalle yau zakici ubanki meya jikamin ledan kaya?"
shiru tayi tana rau-rau da idanu "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" ta faɗa tana tafa hannaye, cikin masifa tace "aina kika samin kayan har ya jiƙe haka?"
baya baya ta fara tana ɗaga mata hannu tareda girgiza kai, cikin masifa ta ɗau takalminta tayo kanta, haɗa hannu take tana mata alaman tayi hakuri, hawaye yana sauka daga idonta, da karfi ta fara dukanta da takalmin, kuka ta fara tana kwace kanta, saida ta mata lilis kafin ta kyaleta, rakuɓewa tayi a lungun kofa tana kallon hannunta wanda yaji ciwo "shegiya marar hankali dan tsaban bakin ciki shine zaki ɓatawa yarana kayan da zasu sa? dan kina bakin ciki ke baki dashi, to ahir ɗinki mara kunya, kuma ki gama kukan kije kitchen ki girka musu ruwan wanka da abincin dare"
a hankali ta gyaɗa kai ta mike zata shiga ɗaki domin canja kaya, sanyi takeji sosai "ke karki sake ki canja kaya a haka zakiyi girkin saide sanyi ya kasheki"
juyowa tayi ta shiga kitchen ɗin tana rawan ɗari, haɗa bakin ice tayi yanata hayaki domin ya jiƙe, da kyar ta samu wutan ya kama, ruwan zafi ta girka musu, tana wajen har yayi zafi, juyewa tayi ta kuma girka wani ruwan, saida ta gama dana wankansu kafin ta girka abincin dare, da kyar ta gama har zazzaɓi ya kamata, tana juyewa a flask ta lallaɓa zata shiga ɗaki, ji tayi an janyota haya, ido ta waro baki a buɗe alaman taji tsoro sosai, tana ganin wacce ta janyota, ta kwace jikinta zata shige ɗaki, hijabinta ta murɗa ta baya tace "har zaki lalatamin kaya? wallahi ya sai kin wanke"
a hankali ta kwace hijabin ta juyo ta fita, kayan ta ɗiba ta wanke kafin ta shiga ciki, kayan jikinta ta cire kana tasa wani riga da skirt na atamfa wanda ya koɗe daga green ya koma fari kat, kayan data cire ta fitar waje ta shanya, katifan dake ɗakin tazo ta faɗa akai, wani hijabinta dake gefe ta rufa jikinta dashi, rawan ɗari take sosai bakinta yana rawa, gashin kanta wanda ya jiƙe sosai taji yana jika mata katifan, a hankali ta mike ta cire hulan dake kanta, tulin gashin ta warware, har yana taɓo mazaunanta, gashi baƙi kirin yana sheƙi, bazasu tayi sosai ta yadda zasu bushe da wuri, jingina tayi da jikin bangon ɗakin tana jira gashi ya bushe ta kwanta, buɗe kofan ɗakin akayi tana ganinshi jikinta ya fara rawa, ido ya zuba mata yana lashe baki, a mugun tsorace ta janyo hijabin ta kuma rufe jikinta sosai, shigowa ya fara da sauri ta fara ja da baya, saida ta mannu da bango kafin ta fara zazzare ido tana haɗa hannu alaman yayi hakuri, zama yayi a gefenta yace "ke dalla nutsu ina yayanki me zanyi miki? so nake kiji tsorona a duk inda kika ganni kin gane?"
gyaɗa kai tayi, yace "tashi ki bani shayi sannan wawiyar tayi bacci"
a hankali ta mike tana kakkare jikinta domin tsoronshi take sosai, shayi ta haɗa mishi kana ta kawo gabanshi ta aje, fita take da niyan yi yace "ke!!!" a firgice ta juyo tana kallonshi da idanu a waje, tsaki yaja "ke wace irin matsoraciya ce? ko mai saiki firgita?"
shiru tayi saida ya gama ta juya ta fita, a kofa ta zauna duk sanyin da ake tana kare jikinta da tafin hannunta, sai lumshe ido take dan bacci, karamin bakinta yanata rawa tsabar sanyi, a haka har bacci ya fara ɗaukanta, koda yazo fita yace "ke tashi ki shiga marar wayo kawai"
tashi tayi ta shiga ɗakin, kwanciya tayi akan katifan ta fara baccin wuya, sai bayan isha ta farka daga baccin tana hamma, murza ido tayi tana kallon wani agogon dake maƙale a jikin bangon ɗakin, tashi tayi da sauri ta fita, alwala taje ta fara wanda ba wani yinshi take akan tsari ba, da sauri ta wanke hannu ta wanke fuska sannan ta wanke kafa ba tareda tayi shafan kai ba, shiga ɗaki tayi ta ɗau ɗan kwali ta shimfiɗa, tada salla tayi da sauri da sauri takeyi har ta gama, sallama tayi ba tareda tayi addu'a ba ta mike ta fara sallan isha, shima idarwa tayi kafin ta tashi ta fita zuwa waje, babban kwano ta ɗauko cike da madaran shanu, akan wuta ta girka rabi sannan ta aje rabi a gefe, hayaki sai damun idonta yake, gaba ɗaya fuskanta yayi jajur, saida ya tafasa kafin ta juye ta ɗauko wani nonon me ɗan tsami ta zuba akai, rufewa tayi ta koma ɗaki, a bakin katifan ta zauna tayi tagumi, a zuciyarta take magana ita kaɗai "haka rayuwata zata kare cikin azaba da wahala? kullum cikin tsoro da firgici babu nutsuwa babu kwanciyan hankali?"
hannu tasa ta share zafafan hawayen da suka zubo mata "kodai na gudu nabar gidan ne?"
a hankali ta kuma girgiza kai alaman ba zata gudu ba zata juri duk wani abinda zasuyi mata, da wannan kukan da tunanin bacci ya kuma ɗaukanta domin ta gaji sosai yau.

AKWAI DALILI!!!Where stories live. Discover now