💕 *ƳAR TSUNTUWA* 💕

✨ *GORGEOUR WRITER'S FORUM* ✨

      ✨ *G.W.F* ✨

[GORGEOUS WRITTER'S FORUM WE ARE THE BEST AMONG THE REST]

*Story & writing*
           By
_ZAHRA ALI ABDULLAHI_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

PAGE-- 1

Zaune take karkashin bishiyar mangoro tayi tagumi hannu bibiyu da gani ba sai an tambaya ba kasan tana cikin damuwa,ba komai kedamun taba I'lla yanda akoda yaushe abokiyar zamanta ke aibata mata 'ƴa gakuma shegen masifa na dare daban na rana daban ta dauki tsawun minti goma awajen zaune kafun ta sauƙe hannunta daga tagumin sannan ta sauke numfashi ta tashi ta nufi madafi dan daura tsanwan rana.

Da shigan takuwa ko wutan bata samu daman hurawa ba sai gata nan kaman anjehota saboda masifanta muke kiranta nida ƙawayena da suna Gwamma aiko tana zuwa bakin madafan ta hau tsirfa masifa cewa take"yanzu habiba tsanwan ranan shine har yanzu baki ɗauraba,sai yau she zaki daura nide nagamu da gamona tun yanzu habiba horon yunwa zaki fara yimana da ƴaƴana a gidan nan.

Riƙe take da ƙugu tayi tsaye saboda masifa har kumfa bakinta yace itade Inna dayake ba mai hayaniya bace ba tace"yi hakuri Yaya dama Ma'arufa nake jira tazo ta ɗebo mun ruwan da zanyi amfani dashi dan ba ruwa a gidan kaɗan dayage dashi Lantana tayi wanki Ma'arufan ta kusa dawowa inaga ko tashine basuyi da wuri ba a makarantar ba haryanzu bata dawo ba shisa,sake baki Gwamma tayi tana kallon Inna ta hau tafa hannu tana cewa"yau naga bala'i Habiba wato ruwan ma da Lantana tayi amfani dashi sai kinyi magana ita ƴar tsuntuwar taki...takai ga karasa abunda tayi niya ba ta shigo gida "da sallama abakina da gudu tazo ta rungumi Inna da take zaunea madafa tace "nayi kewarki Inna ta,

A zabure Gwaggo tayi baya yanda kasan taga wani kashi inda sabo ta saba dariya Inna tana shafa mata kanta tace "nima haka nayi kewarki Auta kinga yi maza kiɗebo mana ruwa yanzu na daura mana tsanwa yau mun makara"tam Inna ta tafaɗa tana miƙewa dauke da botiki yitayi tamkar bataga Gwaggo datake tsaye ba,a fusace ta matsa tana cewa"ke shegiyar ɗiyar tsuntuwa baki da hankali ko?tace Gwaggo minayi kuma?"ohh bama kisan abunda kikayi ba saura kaɗan kitureni kika shige"laa banfa ganki bane Gwaggo"kinyima uwarki tasake cewa nace kiwa uwarki yanzu kan harda hannu take nunan alaman dakuwa.

Shegiya ɗiyar karuwa nan take naji kaina yafara juyawa in akwai abunda natsana baifi zagin da  Gwaggo tama Inna ta ba ga cin mutunci da takewa mata ko wasa Inna bata taɓa nunawa ko a fuska wani lokacin harda Baba take haɗawa idan ta tashi inde yana gidan nan idona ya canza launi daga fari zuwa jaa nace"a'a Gwaggo zagin ki yatsaya iyani amma banda Inna ta karki kuma ce mata karuwa.

Saukan marin da naji shiya dakatar dani bakowa bane ya mareni illa kuwa Inna ta"ranta a bace tace"bana hanaki maidawa nasama dake magana ba"kiyi hakuri  Inna maza ɗauki botikin kije  kiɗebo ruwa,ai tako Gwaggo cewa take ayya Habiba wannan katuwar shegiya ɗiyar dakuka ɗauko ke da Malam bama kuga komai ba wallahi ai irin mugun abunda kike koyama ne yafito fili da kin barta tayi ...

*ALLAH YASA MUDACE*

labarine mai taɓa zuciya hade da barkonciWhere stories live. Discover now