Labari

6 0 0
                                    

2️⃣

Tana shiga dakin asiya ta dawki jakar ta da mayafin ta ta bar gidan da gudu domin ta san ba za ayi mai kyaw ba idan asiya ta biyo ta. A bakin karshen layin ta tarar da adede ta se makarantar school of nursing inda ta ke rokon Allah yasa ta samu admission. Gaban ta se faman faduwa yakeyi amma ta dawre taje wurin da aka manna list din mutanen da suka samu admission. Cikin faduwar gaba ta rinka bin sunayen da ke manne cikin rashin sa'a da duba kaf amma ba sunan ta. A hakan ta koma gida cikin zuciyar ta babu dadi.

Tana shiga gida ta wuce dakin abban su, a kwance ta ganshi yana kirga kudin da ke gaban shi, abba ina uni dazu nazo da safe dan na gaya maka zanje nayiwa hajiya bilkisu kitso kuma naje da duba list din admission dinda aka fitar. Toh maddallah sadiyya da fatan an samu nasara, cikin sadda kai kasa ta gaya mai bata samu ba shima bai ji dadi ba amma se yayi Murmushi yace, haba sadiyya na sanki da tawakkali dan haka kiyi hakuri kila shine yafi zama miki alkairi, toh abba nagode.

Bayan ta fito daga dakin abban nasu ta wuce dakin mama hajar ta gaishe ta sannan ta gaya mata bata samu admission ba itama mama hajar bata ji dadi ba se kawai ta bita da addu'a.

Dakin su ta wuce tayi wanka ta sawya tufafi sanna ta dora girki. Bayan ta kammala ne ta zuba wa kowa nashi sannan ta nufi dakin abban su ta kai mishi. Daki ta shiga ta dawko wayar ta ta kira ammi tace ta bawa asiya hakuri dan Allah Wallahi bada gangan tayi hakan ba. Haba sadi menene na bata hakuri ai har an siya mata wata dan kuka ta rinka yi muna seda aka siya mata amma Karki damu kinsan mutuniyar ki bata da rikon mutum a ranta especially ke dan haka don't worry kinji, toh ammi ki de kara bata hakuri gobe zan shigo da safe insha Allah. Se da suka taba fira sannan tayi mata sallama ta kashe wayar taje waje dan ta zuba musu abinci ita da kanwar ta, Tana cikin zubawa taji sallamar ta. Sanye take cikin uniform din islamiya, farar mace alkebbar mata AISHA sede a furta tabara kalla dan akwai kyaw ga fari iya fari ga kyan fuska tana da manyan idanu se dogon hanci da karamin baki gata nan dai kamar baby doll ❤️. Da ita da sadi banga wanda yafi wani kyaw ba dan kamar su daya harta da yanayin jikin su daya.

Se faman huci take fuskar ta tayi jawur gashi taji ciwo a goshin ta har zubar da jini yakeyi. Subhanallah aisha meya sameki, hankalin yayar tata duk ya tashi da sawri ta je inda take a tsaye ta jata zuwa daki tare ta cire mata hijabi. Ina jinki me ya faru, gaskiya sister ki daina sakewa su zainab fuska ashe su munafukai ne, zagin ki fa naji sunayi wai ashe ke 'yar iska ce saboda malam Nasir yace yana sonki wai dama ashe ke budurwar shi ce su basu sani ba da naga abun nasu yayi yawa shine na dawke zainab da mari ita kuma badiyya da dawko bulalar malam daya bari a aji ta buga mun ita a fuska ai kuwa na hasala na dawko dutse na buga mata a kai se ga jini tarrrr ya zubo mata a fuska ke yanzu haka tana asibiti dan har suma tayi.

Innalillahi wainna ilaihi rajiun, aisha me kika aikata haka suma fa kikace tayi kuma tana asibiti, eh mana sister ba ita taja ma kanta ba, to yanzu de ki tashi kiyi wanka se nasaka miki spirit sannan muci abinci. Tana fadin haka Aisha ta tashi tayi wanka sannan sadi ta saka mata spirit din. Bayan sun gama cin abinci sadi ta kwashe kwanukan sannan ta je ta dawko hijab dinta ta mikowa aisha nata.

Sister ina kuma zamuje?

Hospital zamuje!

Gun wa zamuje ko asiya ce ba lafiya.

Aa gun badiyya de zamuje tunda ke kika fasa mata kai!

Haba sister gaskiya ni babu inda zanje ina nan kuma kema ba inda zaki kizo mu kwanta dare yayi.

To uwata sannu, se naga wanda ze hana ki zuwa kin san duk na fadawa abba se ya dake ki koh dan haka gwara ki tashi muje, aisha najin an ambaci abba tamike ta sawri ta saka hijab suka wuce. Aisha kam akwai bala'i amma idan aka ambaci abba yanzun nan duk wani iya shegen da takeyi ze tsaya cak.

NA CIKA ALKAWARIWhere stories live. Discover now