Labari 2

1 0 0
                                    

3️⃣

Ammi wai gidan mu babu lfy wai mama ta rasu suna asibiti , tana magana hawaye na zubowa daga fararen idanun ta. " Subhanallah wace maman ta rasu haka, kinga tashi muje asibitin, ammi ta fada tana mike wa tsaye. Driver ammi ta kira tace ya shirya mota zasu je asibiti. Da kyar sadi ke tafiya tana faman tunanin wace maman ce ta rasu. Suna shiga asibitin taji gaban ta ya mugun faduwa hakan yasa ta dan runtse idanun ta tanajin wani kuka nazo mata wanda bata san dalili ba.

Ammi ce ta jawo ta Ahankali har suka isa gurin da 'yan gidan nasu suke. Ahankali idanun sadi suka kai kan mama hajar ganin kamannin ta sun chanza gashi kowa yayi shuru kukan ma yaki zuwa ma kowa saboda abun was unexpected. Da gudu hauwa ta rungume sadi ta fashe da wani irin kuka mai tsanani tace, " aunty sadi wai shikenan mun rasa mamaaa!, ta kara she maganar tana fashewa da wani irin kuka.

Ganin mama hajar a wurin ne ya bama sadi tabbabcin cewa mahaifiyar tace ta rasu.

——————
Bayan 'yan watanni da rasuwar mahaifiyar su, mahaifin su ya kamu da rashin lafiya wanda dalilin hawajinin shine daya tashi lokacin da hafsa ta rasu, sanadiyar haka ya rage fita yana aikin gonar da yake.

Ganin hakan yasa bello ya dage sosi yana neman kudi domin ya ciyar da mahaifiyar shi da kannen shi duka sannan ya taimaki mahaifin shi dan ya samu sawkin ciwon kafar dake damun shi.

BACK TO STORY

Suna shiga asibitin aisha ta tsaya ganin da gaske wai ta fiya zasuyi su duba wannan 'yar iskar yarinyar.

"Wai aisha me haka, sadi ta fada rai a bace ganin abubuwan da aisha keyi sun fara yawa, " gaskiya aunty sadi ji nake kamar na koma gida Wallahi, saboda kince nazo kawai nazo idan ba haka ba, ba wanda ya isa yace nazo, ta karashe maganar tana turo dan karamin bakin ta.

"Wallahi aisha za gayama abba. Ai kafin kace me aisha tayi gaba dan bala'in tsoron abba takeji.

Mutane biyu kawai suka gani a dakin, hakan yasa sadi ta tambaya ina mara lafiyar.

"Allah sarki dazun nan aka sallame su, wata mata ta fada tana hada kayan ta suka rage, "to dan Allah inane gidan su, sadi ta fada damuwa shimfide a fuskar ta.

Ganin haka yasa matar tace gidan da dan nisa amma idan zaku iya zuwa yanzu se muje tare na kai ku gidan, Murmushi sadi tayi mata tace "Toh".

Duk wannan abun da akeyi aisha na nan bayan sadi tana wani kumbure kumbure, ita adole baza ta ba. Wani irin kallo sadi tayi mata tace " abba zan gayawa wallahi", jin ta kara ambatar abba yasa jiki na rawa harda kama wa wajen hada kayan da zasu dawka.

Fitowa suka yi daga asibitin su uku, suna biye da matar da zata raka su gidan su badiyya.

Wurin wata mota mai shegen kyaw suka nufa, ga wani hadadden gay fari dashi yana sanye da jeans blue da farar
t-shirt, ya saka facing cap baka ya jingida da motar yana pressing phone dinshi. Shiga motar matar
tayi, tace su shiga su zawna. Daga idanun ta da zatayi taga Abdul, ashe shine wanda ke tsaye wurin motar.

Murmushi ya sakar mata yana mai kara yaba kyawun ta, se kace Barbie doll.

Ita kuma ko kallon inda yake batayi ba tun kallon farko da tayi mishi ta dawke kai ta shige bayan motar, tare da kanwar ta.

Haka suka bar asibitin, a hanya se satar kallon ta ya keyi ta mirror. Babban abunda yake burge shi a gurin ta shine lips din ta, gasu pink yarrr, gasu so tiny da su. Shi burin sa be wuce yayi kissing din su ba, saboda duk cikin 'yan matan shi babu mai irin lips dinta.

Haka ya cigaba da driving yana tunanin ta inda ze bullo mata, saboda yaga tana da wuyar sha'ani. Baze same ta cikin sawki ba, amma ko menene se ya samu abunda yake so.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 06 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NA CIKA ALKAWARIWhere stories live. Discover now