*ƘARFE A WUTA*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
P8
Ta saka hannu, ta kare kanta, tana jiran su hauta da cizo.
Wani irin fito ya yi wa karnukan, suka juya suka koma da gudu in da yake.
Matashin nan ne na ɗazu, da ta biyawa bashi, ya kalleta ya ce "Kin san meyasa na taimake ki?"
Bai jira amsar da za ta bashi ba ya ce "Ba na tunanin Aminu yana da wata ƴar uwa mace, dan haka ƙarya ki ke yi, akwai wata manufa a ranki da yasa ki ke nemansa. Sannan ya taɓa yi mini alfarma a lokacin da ya samu damar da zai kashe ni, kuma kin kyautata mini, alhalin baki sanni ba.
Ɗan daba ba mahaukaci bane ba, shaye-shaye ne yake ruɗa mana tunani.
Wannan shi ne kaɗan daga abun da ka iya samunki, idan ki ka cigaba da neman sa, ko bibiyarsa, wannan dabar babu abun da suke buri da fata, sama da su riga ƴan sanda kama aminu, mace ce ke ki kiyaye kanki, tashi maza ki tafi gasu can tahowa, idan suka cimmiki babu lallai na iya hana su illata ki"Da ƙyar ta tashi, ta yi gaba da sauri, tana cigaba da haki, adaidaita sahu ta hau, ta yi masa kwatancen in da zai kai ta.
Kasancewar mai rabon shan duka, baya jin bari, suna tafe tana sauke numfashi, tana tunanin son sanin su kuma waɗan nan me yayi musu suke son su riga ƴan sanda kama shi, suna ƴan uwansa ƴan daba.
"Ko wani ya kashe musu?" Ta tambayi kanta.
"Yayi kisan kai, kuma a sake shi?
Aikuwa sai na ga ƙwal uwar daka" ta furta a hankali.Ta so ta gaya wa Nasir, abun da ya faru yau, amma ta san tsaf zai ce zai zaneta, saboda kasadar da ta yi, dan haka ta bar wa ranta cewa sai ta samu wata gagarumar nasara, sannan za ta sanar da shi.
Ko sumayya ma ba ta gaya wa ba, tayi shiru da bakinta, sai dai faɗuwar da tayi, duk ta goge gwiwa.
Haka kurum tausayi, da tunanin makomar rayuwar matasan da ta gani, a harkar daba da shaye-shayen nan, ya dami zuciyarta ta rasa abun da yake yi mata daɗi, tana matuƙar son sanin me suke ji a cikin kayan shaye-shaye? Tabbas da ita wata ce, sai ta taimakawa rayuwar su, ko a mutum goma, idan biyu suka shiryu ai an rage.
Kamar wadda ta sha kayan maye, haka yau tayi bacci da wuri, gudun da tayi jikinta duk ciwo yake yi mata, ga numfashi sai wahala yake ba ta.
A wani ɗaki ta ganta, mai duhu sai haske kaɗan a ciki, ga karnuka duk a cikin ɗakin, sai haushi suke yi mata, an ɗaure su da sarƙa.
Ihu take yi tana neman agaji, amma babu wanda ya san tana yi.Can sai ga wani mutum ya shigo, dogo sosai, mai cikar halitta, ba ta ganin fuskarsa saboda duhu, ya shigo ɗakin bai ce mata uffan ba, ya danƙo hannunta ya biyo tsakanin karnukan ya fito da ita daga ɗakin, ya ciro wuƙa zai caka mata a ciki.
Wani uban ihu ta saki, tana kiran sunan Allah, da na Abba da Nasir.
Tana buɗe ido, ta ga Abba a kanta, da Nasir, da su walida har da Anty da baba magajiya, ana ta tofa mata addu'a.
Kallonsu take yi ɗaya bayan ɗaya, ta ce "Abba ya na ganku a nan? Meyafaru?"
Nasir ya ce "Sannu"
Abba ya ce "Arfa ba kya addu'a ko?"
Ta girgiza kai ta ce "Ina yi Abba"
"A'a ba kya yi, da kina addu'a babu yadda za ayi, ki kwanta kina yi mana ihu da safiyar nan, shiyasa nake hanaki wannan shegen fentin da bulbula turare a jikinki, dole sheɗanu su yi ayari, su yi ta binki"
YOU ARE READING
*ƘARFE A WUTA*
Acción*A lokacin da doka, ke ƙoƙarin yaƙi da ta'addanci, ko ta halin ƙaƙa, an samu naƙasu a sanadiyyar bara gurbi, da masu yi wa dokar bi ta da ƙulli. Nasara na daf da samuwa, soyayya ta yi kutse, wurin gwamutsa ƙaddarori biyu wuri guda. Ga soyayya da ta'...