https://whatsapp.com/channel/0029Vaa1qXnKLaHrP5FjGV39*💔-ƘAWA ZUCI-💔*
*©Salma Ahmad Isah*
THRILLER
*KAUYEN KINKIN, YANKIN KABILAR HADZABE, KUSA DA TAFKIN EYASI, AREWACIN TANZANIYA, AFRIKA.*
"Ya ku jaruman wannan ƙabila ta HADZA! Ku sani cewa wannan daji da za ku shiga farauta cikinsa daji ne da ya gagari iyaye da kakaninku! Domin akwai muggan namin daji masu cutarwa da dama a ciki, idan har ku ka yi nasarar farauto dabbar da sarki ya umarceku, rayuwarku za ta sauya, sauyi irin na har abada, idan har kuma mutum ya yi saken bari mutuwa ta riske shi a can!..."
Cikin dandazon jama'ar ƙauyen, ɗaya daga cikin amintattun sarkin ƙauyen KINKIN yake shelar da babbar murya, yayin da gaba ɗaya jama'ar ƙauyen da ba su fi a ƙirga ba suka taru a fadar sarki, kusan duk shiga iri ɗaya ce a jikinsu, domin kowa ka kalla a cikinsu fatar jikinsa ta rine da jan taɓon da suka saba shafawa a jikkunansu da kuma gashin kansu. Hakan yasa hatta da tufafin da suke sakawa wanda UNICEF da sauran ƙungiyoyin tallafi ke raba musu sun dauɗaɗe a cikin jan taɓon.
Kuma duk da zamani ya sa sun sauya tufafin da suka saba sakawa tun a zamaninsu na baya bai sa sun daina amfani da sauran kayansu na al'ada ba, domin al'adu su ne jigon kafuwar ƙauyen na Kinkin.
Tun da ta fello da gudu daga saman tsaunin da ta hau ba ta dakata ba sai da ta fara dosowa fadar sarki, kuma tun daga nesa take jiyowa shelar da ake kan farautar da za a tura samarin garin. Tun kafin ta ƙarasa ta hango Nikamba cikin samarin da aka zaɓa, hakan yasa ta ƙara gudun da take.
Lokacin da ta ƙaraso har sarki ya bawa matasan damar tafiya, shewa da iface-ifacen jama'ar ƙauyen ta karu, domin a bisa al'ada wannan ihun nasu alama ce ta nuna murna ko kuka ƙwararawa matasan gwiwa. Tana isa wurin ta nufi Nikamba dake kan gaba, ta riƙo hannunsa ta juyo da shi, hawaye ko tuni suka ɓallo mata.
“Nikamba akwa oonta?” (Nikamba ina za ka je?)
Ta tambaye shi cikin harshen Hadzane.
Nikamba ya yi murmushi yana kallonta, a lokaci guda kuma yana mamakin yanda akai ta san cewa har da shi za a tafi farautar, duk da ya yi ƙoƙarin ɓoye mata hakan, domin ya san ba za ta so tafiyarsa ba.
"Ti sho kaka Akira!" (Farauta zan je Akira!)"
Ya bata amsa a taƙaice, Akira ta girgiza kanta tana ƙara riƙe hannunsa, hawayen dake zubo mata suka ƙara gudun da suke.
"Zalikma Nikamba! Bania shir'ala" (Ban yarda ba Nikamba! Ba zan barka ka tafi ba).
"Akira! Ninahitaji kiwenda!" (Akira! Dole na tafi)
Ya yi maganar yana cire hannunta a kan nasa da ta riƙe, kuka ta saki mai sauti tana zubewa a ƙasa, lokacin da ya juya mata baya ya bi sauran abokan tafiyarsa da suka fara yin nisa, duk da shi ma ransa bai so ya tafi ya bar ƙanwar tasa ba. Sai dai abij da alƙalamin ƙaddara ya zana ya fi ƙarfin ruwan hawaye ya wanke shi.
_____________________
*Dutse, Jigawa state, Nigeria.*
"Wai Mama har yanzu Saama bai dawo ba?"
Adali da shigowarsa gidan ke nan ya tambayi Mama da ya iske zaune a tsakar gida tana wa Ruwaida firfita, wadda ta yi bacci tun wajejan ƙarfe takwas. Mama ta ɗaga kai ta kalle shi tana amsawa da.
"Bai dawo ba Adali, ni kaina rashin dawowar tasa da wuri ta so ta dameni, amma da yake yau yace wai suna da wasa, shi yasa ma ban damu sosai ba, wata ƙila ya tafi kallon wasan ne!"
Adali dake tsaye ya girgiza kansa.
"A'a, tun ƙarfe goma aka gama wasan, sai dai in akwai inda ya tsaya..."
YOU ARE READING
KAWA ZUCI
RomanceRayuwa na da wahala a kauyen da al'adi ta fi muhimmanci sama da rayuwar mutanen cikin kauyen. Ko da ace kana da masu sanka a kauyen rayuwa za ta maka wahala ballantana ita da ta taso kowa na mata fatan mutuwa! Mutuwa? To me yasa? Me yasa suke fata m...