PART (2)

1.6K 77 0
                                    

🎻💕 EMRAAN ZAYD 💕🎻 page 2⃣
© Jeeddah ja'o🏵
www.jeeddahjao.WordPress.com

   
     A kasalance ya ke bud'e ido yana cije labb'an sa , hannun sa a goshin sa yana addua sannan ya mik'e zaune yana kallon su d'aya bayan d'aya , ganin fuskar su d'auke da damuwa yasa ya Saki wani kyakkyawan murmushi wanda yaso taking breath nawa away ya dubi y'an matan yace

  " Hello princesses! Kun wuni lpya?" Sosai suna jin dad'in inkiyar da yake musu ( princesses) cikin farin ciki suka amsa a tare " Lpya lau Bro! " Aysha ta yamutsa fuska ta matso gefen sa " Me ya sameka ka shigo kamar baka da lapya kuma ka kwanta a nan?" Tana maganar tana gutsurar chocolate , murmushi ya sakar Mata gami da shafa kanta yace babu komai princess kawai stress ne bakiga na ware yanzu ba?"
   Yana rufe baki cikin sa ya soma 'kara kulululu shi kanshi saida ya rik'e cikin yace " Kai! Am starving! Excuse me barin yi wanka in shirya in na gama zamu je d'auko Dad daga airport by four " da murnar su suka fita shi ma ya yi dariya duk da dai kan nashi ciwon yake sosai rufe k'ofar sannan ya fad'a bayi don yin wanka............

     D'aure da towel ya fito daidai lokacin wayar sa tana 'kara don haka ya nufi inda wayan ke ajiye ya d'auka gami da karawa a kunne , daga d'ayan 'bangaren Affan yace " yaya ka fito muci abinci your favorite dish is served ! Sosai yaji dad'i domin babu abunda ke burge shi irin spaghetti and Chinese sauce 🍝 , wata Armani T-shirt bak'a ya saka da white combat trouser hakan ya yi suiting farin fatar shi ya feshe jikin shi da Hugo boss perfume sannan ya taje kansa yasa casual slipper nashi ya fita downstairs to dining section. Affan yace " tab! Wlhy Hanan gwara da yaya bai damu da chicks ba don da tuni ya kashe min kasuwa , ji fa yanda ya d'au wanka!" Sosai suka kwashe da dariya se lokacin Tasleem tace " Ai yaya Affan kai ma ba laifi baka ga wancan me hancin kofin ta mak'ale maka ba? Ai taga yaro d'an wanka da gayu ga kyau ga kuma nauyin pocket ne" sosai suka kwashe da dariya Affan ya had'e rai yace " Kedai Bari Tasleem wlhy kawai ina kyale ta ne saboda abokantaka dake tsakanin old man nata da Daddy ba dan haka ba se na yanka Mata tiket din rashin mutunci wlhy!!"

    Daidai lokacin Emraan na neman zama yace " Kai sarkin y'an Mata ! Kace Mom ta iso ina kuma take? " d'aga gira d'aya Affan yayi yace " Bro nasan ka da wanka idan ka fito kamar mace ka fesa wancan ka fesa wancan shiyasa na k'ira ka don kar ka b'ata mana tym ni yunwa nake ji" sosai Emraan yayi murmushi gami da murd'a kunnen Affan yace " Acici kaifa marabar ka da Aysha kawai k'iba ne da baka da shi amma ci kam inaga har ka fita wlhy" sosai su Hanan sukayi dariya ,basu dad'e ba Mommy ta sauk'o suka soma cin abinci ciki salon kwarewa da kuma hankali............

      Bayan sun kammala ne suka fita don tarbar Dad daga airport...........

Dedicated to FEEDOH Y'AR FICIKA💃🏻

    Jeeddah ja'o🏵

EMRAAN ZAYDWhere stories live. Discover now