PART(1)

3.4K 138 4
                                    

🎻💕 EMRAAN ZAYD 💕🎻 page 1⃣
© Jeeddah ja'o🏵
www.jeeddahjao.WordPress.com

🖊 This is a story of love, ignorance, tears , and lots more!! ......
'''when you find love, hold on to it! Celebrate its feelings and feel what love can do!!!'''

chapter one
THE ZAYD FAMILY'S DIARY

Fuska a d'aure ya shigo gidan yana faman sassauta necktie nashi, sam bai kalli inda suke ba ya haura upstairs cikin sauri......
Affan da ke zaune kan couch ya rik'e remote ya bishi da kallo har kamar wuyanshi zai karye saida yaga har ya haura sama sannan ya dawo da duban sa zuwa sauran da ke cikin falon...

HANAN: siririya ce ba sosai ba Fara ,sarkin zolaya ce sosai sannan akwai damuwa da damuwar wani ga son gulma. she's only fifteen years and also a bookworm.

Aysha: k'atuwa ce sosai tana da k'iba gashi ba'a magana ,bata da aiki se ci , kullum hannun ta da abun tabawa ga son kuka da wuri Shekarun ta goma sha d'aya ne.

Tasleem: Shariya, masifa , karkarin ta murmushi ne ,kullum tana tare da wayar ta always online, WhatsApp,twitter, Facebook etc ga uban son gayu always with friends partying in or out bata damu da harkokin cikin gida ba .she's seventeen years.

AFFAN: d'an Gaye ga iya fafa y'an Mata , duk wani house jest ba'a barinshi a baya , saidai babu wanda yake ji dashi irin yayan sa Emraan gashi da tsokana da kuma son wasa kyakkyawa ne sosai gashi d'an fari and also 18 yrs yana kan tashen shi.

'''Duk wad'annan halayen nasu bai hanasu had'a wasu halayen ba! Suna matuk'ar k'aunar junan su, abu ya samu d'aya kamar ya same su ne kuma basu da raini kansu a had'e yake sannan ga ilimi addini ga kuma boko'''
Back to story

Yana shiga d'aki ko rufe k'ofar bai yi ba ya zube a k'asa duk da cewar gado ne makeken gaske cikin d'akin, yanayin idanuwan sa sun sauya fiye da na da,wani irin ciwon kai ke damun shi a take yaji gaba d'aya duniyar tai masa zafi. Ya dad'e a haka kafin ya samu bacci yay gaba da shi.
Sai lokacin Affan ya durk'usa daidai k'afar sa yana zare masa takalman sa da socks, condition da yaga Emraan ya shigo cikin sa yasa ya kasa tashin sa gudun kar baccin yak'i daukansa bayan ya koma gadon , A hankali Hanan ta zare suit nashi gami da rataye wa a hanger sannan suka dawo kusa dashi suka zauna gami da saka shi a gaba kamar zasu cinye shi kuwa tuni ya harba wata duniyar don baccin nashi yay nisa sosai.......

Cikin nutsuwa take sauk'owa daga d'ayan wing d'in stairs sai baza idanuwa take a falon bata ga kowa ba, batare da ta yi k'asa a gwiwa ba ta fita zuwa harabar gidan inda taci Karo da motar Emraan ko rufe ta ba'a yi ba , kai ta girgiza tana motse k'aramin bakinta ta shiga motar tayi Mata key sannan taje tai parking da kanta , daga Chan ta hangi musa mai bayin flowers tace " Mal musa yaran nan suna garden ne?" Cikin girmamawa ya amsa da " A'a yau basu ma zo ta nan ba " murmushi tayi ta koma ciki direct hanyar side na su Emraan da Affan ta nufa nan ta iske su a d'akin shi sun wani sa shi a gaba kamar matacce.

" Ah ah! Me kuma kuke yi hakan?mesa yake kwance haka shame shame wani abu ya same shi ne? " Affan ya mak'e kafad'a yace " Muma munga ya shigo a fusace shine muka biyo mu tambaye shi already se yayi bacci ,da alama ciwon kai kawai ke damun shi Mom don naga idanuwan shi sun sauya ,ni fa ban tab'a ganin shi a wannan yanayin ba Mom"
Kai Hajiya Ameenah ta jinjina tace "Am sure stress ne ,he'll be alright ku kuma ai se ku bashi waje ko? " Aysha dake faman taunar chocolate tace " Mommy kuma mu barshi shi kad'ai ? Idan ya tashi he'll feel lonely " Wani kallo Mommy ta watsa Mata gami da wafce chocolate d'in " ke wai yaushe zakiyi hankali ? Mutum kullum se uban ci, ke ko kunyar jikin nan naki bakya yi ?" Zumbura baki Aysha tayi tace " Am sorry Mommy barin sake sha ba ,but pls ki bani wannan it wll be mah last piece "
Tsaki Mommy tayi ta mik'a Mata don tasan ko bata bayar ba ita tana da source na samo su da yawa ,amma kuma jikin Aysha really irritates her. Ta juya ta fice su kuwa sukayi zaman su suka ci gaba da jiran farkawar yayan su.............

Dedicated to FEEDOH Y'AR FICIKA 💃🏻
Jeeddah ja'o🏵

EMRAAN ZAYDWhere stories live. Discover now