*UMMIN ABBATEE*😘
🌸 *17~18* 🌸
*UMMI NAH*🌸🙎🌸
Mama sannu da aiki kawo natayaki yanka albasa......no ummi tana da yaji karkiyi hawaye ummi tace kullum cikin hawaye mamie na take ay gara nima inyi inaga ita ma albasa ce kesata kuka dan kona tambaye ta sai yace bakomai......murmushi nusaiba tayi tace wai shekaranki nawa ummi?ummi tace cewa akeyi how old are u?sai nace I am 12years old........ohh ummi kina nufin kin kai 12years?eh nakai kawai dan banda kibane sannan mutane nace we wai ni nacika wauta halin yan fari ta kyalkyale da dariya Anwar yashigo mtsw duk kin dame mutane da hayani ke bakya gajiyane idan akayi miki tambaya daya sai kin bada amsoshi biyar ni matsamin dan Allah zan dauki ruwa a fridge......mtsw ummi tayi tsaki tace mama shi da wa yake? dan naga nidai bana wasa da maza daukan ruwan shi yayi tare da cewa mama baa gama lunch bane?tace sowie Anwar yanxu zaa fara fito da dashi just give me 10mns yace ok mama......yana fita ummi ta tabe baki tace mama wannan yacika raina ni nusaiba tace kece ummi ay karama kidena yima babba rashin kunya KO bakiji dadi ba kin samu yayan har guda biyu ba?ummi tace aa ni bana son wani yaya ay mamie na ma batada yaya.............
🌸🌸🌸
Alhamdulillah mun dawo lafia dan haka yanxu zanje naga matata da iyaye na......iro ne ke wannan maganan alokacin da ya dauko katon akwatin shi yafito palourn ya samu hajiya hafsat mike wa tsaye tayi tace toh Ibrahim ba komai Allah ya tsare min kai amma dan Allah karka dade,kallon ta yayi tare da saurin kauda kai yace shekara nawa bananan shine yanxu zakice karna dade toh gaskia kawai sai kin ganni tace ahh kaman ta cewa garin ba bako na bane sai naje nagani me take yi maka dayasa ka ki dawowa...........hanyar fita yabi yace natafi tace muje na rakaka driver nanan yana jiran ka awaje. ......................Gaban sa bai tashi faduwa ba sai da suka shiga cikin kauyen haka kawai yaji hankalin sa duk ya tashi sun kai bakin kofar gidan inda yanuna ma driver ya yayi parking yafito tare da bude boot ya dauki akwatin sa ya shiga cikin gidan......shuru yaji gidan ba wani hayaniya kaman da sannan kofar dakin salma awangame bayan da take kulle wa ba ga tsakar gidan kaca kaca.........
Sallama yashiga yi shuru ba a amsaba sai daya kara kwalla sallama sannan aka amsa da cewa wanene anan yace iro ne inna kina ta inane?fitowa tayi da azama ta ware ido dan jin abun da taji ko da gaskene idan ba kizo yake mata ba?tace iro da gaske kaine?lafia iro saceka akayine?jamaaa saude kuna ina kuxo ga iro yadawo......shidai iro binta kawai yakeyi da kallo gaban sa nata dukan bakwai bakwai.........yace inna ina salma me kikeyi adakin ta?tace kaji tsiyan taka bakako tambaya jamaan gidaba sai matar ka kake tambaya saude tazo aguje inna wakika ce?tace zoki gani da idanunki daga ido tayi tace inna wane bature kika samu haka?tace aike idan bazaki gane shiba sai ki kira dan uwanshi ayshi bai isa yamanta jinin saba,haba inna yi hakuri kaman na san fuskan wallahi toh iro ne dauko tabarma kishinfida wajen yafi iska .....saude tace iro????kaina haka kazama uwa bature ?lallai ashe kai dadinka kaje kana taji kabar matar ka da yarka acikin wahala........matata da yata? inna ta saka mata tsawa tare da zagin ta idan kika bazaki dauko tabarma ba sai ki fada min yar uban mai surutun tsiya.............
. bayan anshinfida tabarma ne suka zauna yace inna ina wuni tace kai ko iro ina nashiga?nan ya dukar dakai hawaye suka fara masa zuwa ya kwashe duk abunda ya faru yafada ma su sai salati suke tayi. ....inna har da kwalla.......yace inna ina salma ina malam nakuma ji saude na maganan ya dagaske nabar salma da cikina?tabbas kabarta da cikin ka dan kuwa yar nan ba inda tabarka akama da hasken fata halinka ne kawai batayi ba dan akwai baki da tsiwa........murmushi da kuka yafara yi yace inna suna ina ?ko sun fitane?tace sun bar gidan ne tunda malam ya rasu tace bazata iya zaman wahala ba ta sa yarta agaba suka tafi, saude tace wallahi inna adaiyi ahankali antsufa ana fadan karya salma batace haka ba iro itace ta kori salma da yarka balkisu ana ce mata ummi. ..........wat yafada malam ya rasu? kuma jika kori matata da yarinyata?ALLAH sarki malam nasan nayi maka laifi Allah yasa ka yafemin amma ina baki kyauta min ba yanxu ashe bakya sona?kai iro kana da hankali kuwa inhaifeka kace bana sonka ?eh bakya sona da bazaki min haka ba yanxu ta ina kikeso nafara neman su cikin duniyan nan bansan ma ina suka dosa ba. ..........ya mike yafita gidan hajara yaje yayi sallama mijinta ne yafito bayan sun gaisa anyi yaushe gamo...............sai mijin hajara yake cewa Kaikuwa ina kaje ne? kabar iyalinka cikin wahala gaskia bakayi musu adalci ba gashi daga baya akace innah ta koresu munyi munyi su zauna tare damu salma tayi haka dai hajara tace motan Abuja suka shiga...........dukar dakai kawai iro yayi baice komai ba yace ina zuwa kadan jirani anan.........komawa cikin gidan yayi ya ja akwatinsa batare da yace ma inna tak ba datake ta faman kiran sunan shi tana tambaya ko lafia ina zakaje......saka kayan yayi a mota ya bude akwatin yaciro wasu tsara ya rufe koma wa yayi kusa da mijin hajara yace ga wanann kaba hajara wannan kuma yara sannan dan Allah inaso kashiga ciki ka kira min ita inaso natambaya ko ina salma tace mata zataje sannan wane gida ne?yace toh fa wllhi tatafi gidan kitso amma salma tace mata gidan kakar mamarta zataje wai iro ya mika masa hannu sukayi sallama yakoma mota yace ma driver mu tafi. ................
🌸🌸🌸
Haka suma su papa kiri kiri gasu sun dawo amma da basuda address din gidan salma sannan kuma basu san wa zasu tambaya ba tinda dama mamar tace ta samu kuma Allah yayi mata rasuwa.........Haka suka zauna wata daya kenan da dawowan su hankali atashe batare da sun sami address din ba .....kawai sai dabara ta fadowa mumy tace tunda sunsan garin suje inyaso sai su tambaya gidan da sunan malam dauda..........Haka kuwa akayi suka shirya washe gari suka kama hanya,basu wani sha wahala ba wurin samun gidn saboda malam sanannan mutumin kirki ne agarin. ..........
amma abunda suka tarar ba karamin tayar musu da hankali yayi ba dukan su...............🌸🌸🌸
Yau ne su adil zasu koma makaranta adil yashigo palourn ya same ummi zaune tayi shuru yace an mata yau meya faru naganki shuru ne?fada min waye ya tabaki ko anwar ne?murguda masa baki tayi tare sa matsawa tace bakomai yace bakomai shine zaki zauna shuru haka tace in fada maka ne?yace eh mana aydama so nake ki fadamin,tace toh promise me idan nafada maka zakayimin yace y not just tell me kinga mun kusa wuce wa,tace toh ba mamie bace taki Sakani a secondry ba ta tura fuskan ta atsakan kanin karar ta tana sheshekan kuka dagoda ganta yayi tayi saurin buge hannunsa ta ce karka kara tabani ina wasa da mazane aka fada maka?tace toh sorry yanxu dama akan school ne kawia kike
kuka?ta ce eh zaka sakani ?yace kar ki damu insha Allah zaki fara bari naje nayi ma mama maganata ce yauwa yaya dan baki nagode ya juyo ya bazaki dena kirana dan bakiba wallahi zan fasa tace wayyyo yaya wallahi nadena yi hakuri............🌸🌸🌸
Toh fa ummi anfara zuwa school da taimakon nusaiba wanda kafim tayi sai da ta shawarce mijinta wanda yakusa dawowa nan da next month dama mutum ne mai tausayi dan ta nuna masa kaman cewa salma yar uwar tace.............anyi saa kuwa anyima ummi interview nida tafi jss 3 saboda tana da hazaka gashi salma ta kokarta sosai wurin koya mata English dan idan suna tare su kadai bata ceka yi mata hausa ba...........saboda akwai lokacin da take yi mata tiranci ko acikin mutane ne sai inna ta dinga cewa zagin ta sukeyi.........shiyasa ta dena yi mata sai idan suna su kadai kawai
Sati na biyu kenan na ummi a school duk da idan tayi wani abun bata iya ba anayi mata dariya saboda komai tana kokarin taga ta iya har yan class din suna ganin fa kaman tacika kaudi. ..........yau ummi tashigo class taga wata ta dayan a wurin da tasaba zama batace mata komai ba sai taga wani kujera daban ta wuce ta zauna can bayan teacher ya shigo yafara karatu sai ga wani yaro yashigo kai tsaye wurin da ummi ke zaune ya wuce ya zauna,ummi na ganin haka ta fito da biro ta dora sai ga yaron yamike da sauri yana wash wash wash menene kaman allura tace ba allura bane biro ne........amamkince now ya juyo yana kallon ta ta kara daure fuska teacher yazo kusa dasu yace me yasa zaki saka masa biro wurin da zai zauna?ummi tace nifa bana wasa da maza meyasa zaizo ya zauna kusa dani ay ni ba namiji bace. ..........dariya malamin ya kwashe dashi yace toh waye yace miki nan school dole sai mace da mace zasu zauna?ummi tace nidai ba ruwana mamie tace bakyau wasa da maza yan clas sai dariya akeyi mata teachern yace kowa yayi shuru ke bilkis khaleel waye yace miki dan kun zauna tare sai dole kunyi wasa?ay karatu kikaga anayi ba wasa bako ?m teacher wallahi baxan zauna dashi ba salon tamin ciki tafara kuka ta mike kafafun ta asaman kujeran makami yace kai Adam je kasamu wani sit din ka rufamin asiri da bilkis bazan iya da itaba.........
Haka rayuwan ta dinga tafiya kwanakin na tafiya a yau ne mijin nusaiba zai dawo daga kasar india...........
By rukky😘 *luv u all*