[01/11 8:14 am] Rukayya Yelwa: *UMMIN ABBATEE*😘
🌸 *27~28*🌸
*UMMI NAH*🌸🙎🌸
🌸🌸🌸
Tagumi salma tayi hawaye na zuba a idanun ta iro kawai take tunawa saboda arayuwar ta bata taba zaton cewa zata iya auren wani da namiji ba bayan iro,gaskia Maman anwar bazan miki butulci ba kinga nidai bason mijin nake yiba toh mai zaisa dan son zuciya na kuntata miki waye keson kishiya aa nidai inaso zumuncin mu ya dore wallahi banda wani dangi ahalin yanxu bayan ke kinga kuwa idan na auri mijinki ko kulani bazaki dinga yiba kuma dawane ido zan kalli su hajiyan ki ay mutane bazasu gane ba cewa zaayi naci amanan ki..........dariya nusaiba tayi wanda sai da salma ta juyo tana kallon ta amamakince,nusaiba Tace kin ga ba ruwan hajiya ta mace ce mai fahimta saboda dayardar tane ma nazo nasame ki da wannan maganan ajiyan zuciya salma tayi tare da mikewa ta ce gaskia ni bazan iyaba itama nusaiba tamike tace to tsaya kiji wallahi rashin yardar kine ma zaijawo mana matsala dake saboda haka kawai bazaki kashemin miji akan sonki ba shawara ta rage naki kuma ina bukatar amsan ki zuwa gobe idan kinga zaki iyamin halacci bantaba rokon ki wani Abu ba kiyimin wannan idan kuma bazaki yiba toh shikenan. .....fuuuu tamike ta fita daga cikin dakin ummi da ta dauko ruwan tana tsaye bakin kofa sai murna takeyi tafada cikin dakin ta riko hannun salma da ta Lula cikin tunani tace mamie nah aure zakiyi?dan Allah kiyarda kisamo min baba ni ma kinga idan ana p.t.a sai babana yadinga zuwa salma tace kai ummi wai meyasa ke bakya girma ne?ni sakeni pls go and pray zuhr eh mamie zanyi amma promise me zakiyi if not nima ba ruwana dake tunda bakyaso nasamu baba..........
Tirkashi salma tace oh ni ummu salma ina cikin tsaka mai wuya nayi ma nusaiba adalci kuwa idan na aure mata miji daga taimako zan jawo mata matsala toh kuma idan ban aure shiba haka zanzauna?aybansan wazan aura ba dan bakowa ne namiji bane zai iya auren ka har ya kire maka yarka ba tunda gashi itama ummi din itama tana son shi ay shikenan
🌸🌸🌸
Tunda amince war salma baa tsaya bata lokaci ba akace sati mai zuwa kawai sai adaura,
amma me sai da nusaiba ta shiga dakin fa ta rufe tana ta kuka ita kadai ba ta bari kowa yagane koda zata fito sai dai ta ta dariya kamar bata da damuwa.....
Duk shirin auren nan da akeyi salma bata taba bari sun haduba da Salman shi ma kanshi ya daina damuwa da ganinta tunda dai komai yazo karshe takusa zama tashi gaba daya.....Nusaiba ba karamin shiri take ma salma ba sai kace ba it's zaayima kishiyaba tare sukaje gidan gyaran jiki akayi harda lalle da kitso ba karamin fitowa sukayi ba inbama salma da bata saba yin kitson ba sai yafito da ita sosai nusaiba tace gaskia amaryan baban anwar am jealous irin wannan kyau haka ay sai kisa ango bama xaigane nayiba akan taki tafi tawa salma tace kinsan dai saboda ke nayi badan shiba wallahi saina kunce ay ni har abada nafison son da kuke yima juna da kulawa su dore har abada nusaiba ta dafa ta ce insha Allah salma shiyasa nanace sai ke din dan wallahi nayarda dake sosai fatana Allah yaba shi ikon yin adalci atsaka nin mu salma ya kawad dakai nusaiba tace bazakice amin ba?kawai murmushi salma tayi batare da tace komai ba.
🌸🌸🌸
Rana bata karya kam.....
dan ayaune aka daura auren salman da salma akan sadaki dubu hamsin,wanda zata tare ayau....
amma me?da dare yayi nusaiba tayi tayi da ita kam tayi ma wanka takaita dakin oga amma fir taki ta juya mata baya tayi baccin ta haka nusiaba ta koma side din salman ta sameshi azaune yana karanta news ppr ya dago idanunsa ya kalle ta tare da leka bayan ta yaga ba kowa nusaiba ta dagoshi tace baban anwar kana lekawane on zakaga amaryan ka wato yau baa maraba dani? yace kinjiki aike bakya tsufa matata yar aljannah insha Allah tayi murmushi ta kawar da maganan tare da cewa nayi nayi amaryan ka tazo taki fa yayi shuru can sai yace barta kawai ana dole ne zo muyi baccin mu kinji uwargidana ran gida kibarta tagama sai naga gudun ruwan ta ay..... ....
[01/11 9:18 am] Rukayya Yelwa: *UMMIN ABBATEE*😘🌸 *29~30*🌸
*UMMI NAH*🌸🙎🌸
Wata biyu kenan da yin auren nan amma har yanxu salma bata shiga dakin mijinta kuma ko magana bata hafasu haduwa ma bata bari suyi.........
abun tun baya damunshi har yakai nusaiba ta gane damuwan tasa saboda baya boyewa ma kullum dai ummi nazuwa tayi masa fira saboda yarinya akwai ban dariya ayanda yake cema nusaiba.....Yau ne nusaiba ta dauki qudirin tunkarar salma da maganan rashin kula mijinta...
ta same ta ta idar da sallah ta daga hannu tana addua nusaiba ta e Allah yasa ana karban sallahm nan taki salma saboda Allah da malaiku bawanda baya fushi dake ayanxu haka ta zauna abakin gadon dakin salma batayi magana ba sai we tashafa adduae ta sannan ta juyo tace Maman anwar ina wuni ya aiki ya gajiya ?eh dole kice min ya gajiya kinbar ni da angonki nikadai inata fama toh tsaya kiji bama sai naja maganan da nisa ba wallahi yau idan dare yayi bakije dakin mijinki ba ko toh wallahi sai nace yazo nan dakin try me and see tamike ta fita can sai gata ta kara dawowa fa ajiye mata wani hadadden leda sai walkiya takeyi ta ce ga wannan karfe takwas bayan ishai ki tabbata kin shirya saboda nice yar rakiyar siyan baki salma ta ce Maman anwar anya zan iya kuwa?gaskia bazan iyaba nusaiba tace oho dai sai naxo........*8:14*
alokacin salma na zaune tagama cin dinner ita da ummi saboda tare suke cin abinci nusaiba tayi sallama tashigo dakin turus tayi ganin salma zauna bata shiryaba daure fuska nusiaba tayi tace meke nan hakan?salma daba tasan da tsayuwan taba ta dago kai tayi shuru nusaiba ta duba saman gado wurin da ta ajiye kayan har yanxu suna ajiye wuce wa tayi ta dauka tadawo ta rike hannun salma tace taso ummi ke kuma ki kwashe kayan kine ki kwanta kinsan gobe zaki fara zuwa ss1 ko?ummi tace eh wallahi mama yanxu zan kwanta sai da safe yauwa yar albarka Allah yatashe mu lafia kiyi bacci ki karki tsaya jiran mamien ki zata tsaya yin wani dan aikine
direct dakin nusaiba suka wuce ta ce shiga kiyi wanka salma tace wanka kuma nusaiba tace eh salma tace ay nayi wanka dazun nan eh shiga dai kisake yi wannan na daban ne nasa miku turaruka acikin ruwan yi sauri
jiki ba kuzari salma tashiga tayi wankan, tafito daure da towel sai a lokacin nusaiba taga kyan salma dakyau wanda dole kowane da namiji yagani ya yaba gatanan sai kace wadda bata tabayin aure ba ga jikin sai sheki yakeyi, tace zauna to kishafa mai da taimakon nusaiba ta shirya salma tsaf tace oya kalli mudubi kiga yanda kika fito juyawa salma tayi ganin kanta ahaka ba karamin tayar mata da hankali tayi ba kawai sai ta fashe da kuka nusaiba ta rukota suka zauna tace haba salma sai kace wata sabon shiga meye na kukan toh?kinga karkije kinama mijina kuka kitayar masa da hankali saboda banhada kowa da mijina ba dan bana son tashin hankalinsa sai ki kiyaye muje na rakaki.........sun kwankwasa dakin suka shiga har suka kai kusa dashi baima san sun shigo ba ya nacan yana tunani ganin haka yasa nusiaba ta radama salma a kunne dan Allah jeki ki tsugunna kusa dashi ki dafa shi zakiga yanda zaiyi wallahi wannan tunanin nakine yakeyi salma........
haka kawai salma taji bazata iya mata musu ba jiki ba kwari ta karasa ta tsugunna tare da dora hannunta asaman kafarsa hannun nata har makarkata yakeyi,Jin antaba shi yasa ya dawo daga tunanin da yakeyi tare da dora idonuwansa akan salma ba shiri ya gyara zaman sa ya fara murmushi nusiaba ta karaso tace dama nafada kece matsalan gashi har mijina yafara murmushi yanxu dai soka bani kudin siyan baki sai nabar maka matar ka idan kuma haka bani ba ba inda xani yace nawa kikeso matata ?tace 200k only yace angama jeki ki dauka ko nawama kike so tace ahhh toh nagode sosai
nusaiba takoma daki amma tunani bai bari tayi bacci ba tana fa juye juye yau nice mijina zai kwana da wata amatsayin matar sa kawai sai ta fashe da kuka ganin dai har karfe daya Jamaa bacci sai kawai ga mike tare da dauro alwala ta tafara nafila tana rokon Allah ka sassauta mini kishi kasa nayi kishi irin na addinin musulunci. ........ta mike ta ninke sallayan ta bude kofar ta tafita dakin salma taje wurin ummi tare da kwanta wa a gefen ummi ta rungumo ta sai asannan ta samu baccin ya dauke ta..........BY RUKKY 😘 *luv u all*