page 46~50

1.4K 94 0
                                    

JARABAWA TACE


yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                     (NWA)


THIS PAGE IS FOR YOU DEEJERH
Banda bakin da zan maki godia irin kaunar da kike nunaman saidai ince Allah yasaka maki da alkairi yabiya maki buk'atunki na Alkairi....thankyou so much priya❤






                 4⃣6⃣➖5⃣0⃣

     Kyarma hannuna yakamayi bansan sanda na fara kwalla ba, da sauri na nufi d'akin su Yaya ina shiga banyi sallama ba na afka ciki saboda yanda na rud'e. Gaba d'aya suka mik'e ita da Uncle suna tambayana lafiya, kasa magana nayi sai kuka da nake faman yi, tsawa Yaya ta dakaman wanda yasa na fashe da kuka, d'aure fuska Uncle yayi yace "akanmi zaki mata wannan tsawar? Baki binta a hankali" hannuna yakamo ya zauna dani kallo na yayi yace "Lady mike faruwa?"
     Mik'a mashi wayan nayi, yana amsa yakai dubanshi kan screen d'in zumbur ya mik'e shima yana salati, matsowa Yaya tayi kusa dashi tace "wai miye?" Wayan yabata tana karba tace "what?" Saleem nake gani da wata, girgiza kai Uncle yayi yace "tabbas shine."
      "Dama ya gaya maki zaiyi aure ne? Ko kuma kun samu matsala ne?" Cewar Uncle. Girgiza kai nayi na share hawaye nace "ko d'aya babu wanda nasani yanzu nagano dalilinshi na canja man kwana biyu ashe aure zaiyi, miyasa yaman haka miyasa zaizo rayuwata ya wargazaman farin cikina mina mashi haka? Uncle Yaya miyasa tun farko baku ce karna saurari Saleem ba? Miyasa" sai kuma na fashe da sabon kuka, kuka Yaya takeyi ta jawoni ta rungume shi kanshi Uncle saida ya share kwalla...
      Yaya tace "kiyi hak'uri Lady JARABAWAR KICE haka bazaki iya kauce mata ba, muma bamusan zai maki haka ba inda munsani da bazamu bari ba..

     Wayana tayi ringing dubawa Uncle yayi da yake tana hannunshi Prince Charming yagani, mik'oman yayi yace "Lady ki d'auki wayan kiji mizai ce maki" amsawa nayi na d'aga dan bazan iyayin musu dashi ba ina d'agawa yace "Lady ina gaban gidanku" kashe wayan nayi na juyo na kalli Uncle da kanshi yake k'asa "nace Uncle wai yana gaban gidanmu."
       D'agowa Uncle yayi yace "kira Deeyerh ta shigo dashi falon bak'i", Kiran Deeyerh nayi a waya nace ta shigo da Saleem falo..
      Kallo na Uncle yayi ya sakamar man murmushi yace "Lady kije kiji dami yazo" da sauri na kalleshi d'agaman kai yayi, kallon Yaya nayi murmushin k'arfin hali tayi tace "kije My baby kinji" tashi nayi na nufa d'akin bak'i...

      Tafiya nake jiki ba kwari  falon bak'i na tardashi yana ganina ya taso da sauri yanaman dariya, ganin  hawaye a ido na ya tsaya cak, kallo na yayi yace "My Lady miyafaru? Mi aka maki? Waya tab'aman ke?" Binshi nayi da kallon tsana nace "kai kake da amsoshin tambayarka" zaro ido yayi yace "ni kuma?"
      Wayana na mik'a mashi nace "minene wannan?" Ido ya zaro kallo na yayi yace "Please Lady kar abun nan da kika gani ya d'aga maki hankali Allah zan maki bayan.....bai ida ba na daka mashi tsawa...

      Nace "bayanin mi zakaman? Mizaka gayaman, a yanzu baka da abinda zakagayaman kariga da ka cuceni ka yaudareni dama ka shigo rayuwata ne dan ka wargazaman farin ciki? Tabbas kayi nasara ka wargazaman farin ciki saboda sai da ka koyaman sanka kana zaka gudu kabarni ka cuceni kaci amanata amma kasani Allah ba Azzalumin kowa baneba, yanda ka cuceni kaima sai anmaka."
        Ki saurareni mana kiji mizan gaya maki wlhi iyayena ne suka had'ani da ita ba santa nake ba kinsan ke nakeso, kuma na gayama Iyayena da na aure ta idan kin gama karatu zan aure ki saboda kece muradina...
        Harara na watsa mashi waye zaka aura? Badai ni Nafeesar ba, shiyasa dama kwanaki kadaina kirana?  Kafita harkata ka shareni Saleem kasani a yanzu na tsaneka na tsani ganinka, cuta dai ce ka riga da ka cuceni amma kasani kana da k'anne kuma zaka haifa, yanda ka shigo rayuwata ka tarwatsa ta haka kaima in shaa Allah za'a tarwatsa taka rayuwan, ina kaiwa nan na juya na fita da gudu ina kuka

      Duk abin nan da mukayi akan idon su Uncle, ina fita d'akin suka shiga bansan mi sukace mashi ba. D'akina suka shigo da sallama kwance nake ina kuka, na kasa amsa sallamarsu...

©FEEDOH DEEDOH

JARABAWA TACE Where stories live. Discover now